← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 205

Sashe 60

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

sama" tana lullumshe ido ta mike xaune sannan ta tashi ya haska mata hanyar stairs, ta fara tafiya sannan ya bi bayanta, tana shiga dakinta ko rufe kofar bata yi ba ta fada kan gado ta ci gaba da baccinta, yana tsaye daga bakin kofar bayan ta shiga, ya kulle kofar sannan ya wuce bangarensa. Sae kusan karfe tara da rabi Abuturrab ya sauko downstairs, kamshin girki kawai yake ji a gidan, ya tabe baki ya xauna saman kujera, sae ga ta tafito kitchen, turus tayi ganinsa, sae kuma ta juya ta koma kitchen din, shi dai idonsa na kan tv da yyi powering, can sai ga ta ta fito ta karaso cikin parlon, kallonta yyi... Her expression today isn't of someone that is sad, ta xauna kasa ta sunkuyar da kai, dimples dinta na lotsawa tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau" Ya gane da magana a bakinta ganin yanda take wasa da fingers dinta, can yace "Me xa ki ce?" Ta kallesa tace "Dama cewa xan yi in kawo maka kumallo?" Da mamaki ya dinga kallonta, can yace "Na me kenan?" Tace "Dankalin turawa na soya na soya kwai, sai na tafasa ruwan shayi" Yace "Ohk mun yi da ke xan ci ne?" Ta girgixa masa kai yace "Toh baxan ci ba, kayan abincin da kika gani a kitchen don ki girka ke kadai na siyosu na ajiye ba don ki girka ma ni da ke ba" Sunkuyar da kanta kawai tayi, bayan few seconds ta mike a hankali xata bar wajen yace "Tsaya" Tsayawa tayi amma bata yarda ta kallesa ba, yace "Dama kin iya soya Dankalin da kwai kike tsayawa da yunwa?" Bata ce masa komai ba, ya tabe baki yace "Je ki" Juyawa tayi ta koma kitchen din. Tana komawa ta fara kuka a hankali, sae da tayi me isarta sannan ta goge idonta ta fito xata wuce sama, ya bi ta da kallo yace "Kin karya?" Ta gyada masa kai xata haura sama yace "Dawo nan!" Ji tayi wani sabon hawayen na shirin xubo mata, ganin tsayawa tayi yace "Ba kya ji na ne?" Dawowa tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Wuce ki xuba abinda kika yi ki xo nan ki xauna ki ci" xata yi magana ya jefa mata wani kallo, kitchen din ta nufa trying hard kar ta fara rusa kuka, a haka ta debo abinda tayi ta dawo parlon ta xauna tana turawa da kyar yana kallonta yana kallon TV sai da ya ga ta gama sannan ya bar ta ta wuce sama, shi kuma ya fita xuwa siyo fastfood.... A ranan mutumin da Abuturrab ya sa ya nemo masa mai gadi amma mai mata ya kirasa ya sanar masa an samu, Abuturrab ya masa izinin kawosa gida amma wajajen biyar na yamma. Yana xaune parlor yana jiran Jiddah bayan azahar, he is been sitting for almost 20 mins now, daga cewa ta shirya shine har ynxu, mikewa yayi ya haura sama ya bude kofar dakin suka kusa cin karo don xata fito ne ita ma, ta koma baya da sauri, ya wani hade rai yace "Baki da hankali ne xaki shanya ni a parlor?" Ta marairaice tace "Na kasa rufe rigar ne?" Yana kallonta daga sama har kasa yace "Wani riga?" Hijab ne jikinta har kasa sai atamfa daga ciki, tace "Zip din rigar" Ya jefa mata wani kallo ya juya, bin bayansa tayi, har suka sauka parlor, ya dau makullin motarsa ya nufi kofar fita ta bi sa da sauri, yana cikin motar ta iso parking space din xata bude back seat yace "Kinsan meye ma'anar mutum ya shiga bayan mota bayan su biyu ne kawai a motar?" Tayi shiru tana kallonsa, bai kuma ce mata komai ba, ta xagayo xata shiga motar sai a sannan ya ga how obvious zip din da bata kulle ba yayi cikin hijab din, bayan ta shiga gaban motar yace "Daga hijab din nan" a hankali tace "A bude zip din yake" ya hade rai yace "Daga nace" kamar warce xata yi mugun abu ta fara daga hijab din, sai kuma ta kallesa kamar xata yi kuka, ganin yanda ya hade rai ta daga hijab din kawai, bayan ta yake kallo da bra strap dinta, ta sunkuyar da kanta, yace "Da a haka xaki bi ni don baki da hankali?" Ta girgixa masa kai, yace "Koma ki canxa kayan" Ta buda ido tana kallonsa, ganin irin kallon da yayi mata ta bude motar ta sauka, sauka yyi ya bi bayanta to check another clothe for her, sai bayan da suka shiga parlon ta kallesa tace "Xaka iya taya ni jan zip din fa, ba lalacewa yayi ba" yace "Ban yi niyya ba" bata kuma cewa komai ba ta wuce sama ya bi ta. Bude press din nata yayi yana kallon kayan ciki, abaya baki ya ciro mata da mayafinsa ya ajiye gefen gado, ta dan xaro ido tace "Wannan ai yana kama jiki" ya harareta yace "Baya yake kamawa ba jiki ba, minti uku na baki ki canxa kayan nan ki dawo kasa ki sameni" Bai jira cewarta ba ya fice daga dakin nata dake ta kamshin turarurruka, a balcony ya tsaya yana jiranta, sai gata ta fito, sosai bakin abayar ya haska farin fatarta ta dawo kamar balarabiya, flat show ne kafarta, she looks so beautiful and neat, kawai dai ta rame ne ba kadan ba, ganin ta tsaya ta wani sunkuyar da kai yace "Tsayuwar me kika min a nan?" Tafiya ta fara yi, ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, front seat ta bude ta shiga, sai da ya fara bude gate sannan ya dawo ya shiga motar suka bar gidan, ya sauka ya kulle gate din, gidansu Ahmad ya nufa don xuwa gaida Umma, ya lura kamar she is a bit angry at him, don gashi wannan satin ma bata ce masa xata xo ba, a parking space din yayi parking, Yana sauka motar Jiddah ma ta sauka tun da taga gidan da suka shigo farin cikin fuskarta ya kasa boyuwa, shi dai ko kallonta bai yi ba, kallonsa tayi a d'an tsorace bayan ta sauka tace "Don Allah xan iya xuwa in gaida maman Abdallah?" Ya fara tafiya xuwa cikin gidan yace "Ki je mana" Da sauri ta nufi dakin Maman Abdallah, sai da ta gaida mai gadin ya amsa da fara'a yana mata sannu da xuwa tace "Maman Abdallah fa?" Yace "Ki shiga tana ciki" Da sallama ta shiga dakin, Maman Abdallah na ganinta ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Idonki kenan Jiddah, kai kai kai kinga yanda kika yi kyau kuwa, sannu da xuwa amarya" Wannan kalmarta na karshe ne ya d'an sa mood din jiddah ya canxa don tasan dai ita ba amarya bace, Xaunawa tayi tana ta kirkiran murmushi tace "Abdallah na bacci" Maman Abdallah tace "Wllh kuwa, ashe ku ne kuka shigo gidan a mota, sannunku da xuwa" Jiddah na ta murmushi tace "Bari inje in gaida Umma" Maman Abdallah tace "Toh maxa ki tafi, amma fa don Allah ki leko kafin ku koma kinji?" Jiddah tace "Toh" fita tayi dakin dai dai sanda Ahmad ya shigo compound din, ya buda ido sosai ganinta, sai kuma ya hango motar Abuturrab, da ladabi ta gaishesa ya amsa da fara'a yace "Yaushe ku ka xo?" Tace "Yanxu muka shigo" yace "Maa sha Allah sannunku da xuwa" Tafiya take yana gefenta shi ma yana tafiyan, can yace "Amma baki da damuwa ko Jiddah, kar ki boye min komai ki gaya min" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyi tace "Ina son dawowa nan wajen Umma" Shiru yayi bai ce komai ba, don yasan taurin kan Abuturrab ya wuce ya amince Jiddah ta dawo nan gidan, a hankali yace "Kar ki damu Jiddah, nasan xama ke kadai ne baki so ko?" Ta gyada masa kai, yace "Kar ki damu nasan me xanyi" Da damuwa tace "Amma kar kayi masa magana ihu xai yi min" Murmushi Ahmad yyi yace "No baxan yi masa ba" Abuturrab suka gani bakin kofa tsaye alamar lkcn ya iso wajen ganin jiddah bata shigo ba, Jiddah sai da taji gabanta ya fadi ganinsa, shi kuwa sai ya hade rai, suna isa balcony din Ahmad yace "Sai ga amarya yau ta xo gidanmu, kun xo gaida Umma kenan" Abuturrab da yayi masa wani kallo underneath his breath yace "Half-wit" daga haka ya juya ya koma parlon. Rungume Umma jiddah tayi, sosai tayi farin cikin ganinta kamar yanda Umma ma taji dadin ganinta, Shi dai Abuturrab na yi yana kallon agogo don bai ma son la'asar yayi masu a gidan, Kitchen Jiddah ta tafi bisa umarnin Umma na cewa taje ta taya su Siyama da mai aiki girki, Umma na kallon Abuturrab tace "Why is she this lean? Bata da lafiya ne?" Ya sunkuyar da kansa yace "Eh tayi xaxxabi kwana biyu, amma ta samu lafiya yanxu" Ahmad dai sai wani kallo yake masa, Da damuwa Umma tace "Toh Allah ya sauwake, ita kadai din ce a gidan kenan yanxu?" Da sauri yace "Aa Umma ai nace akwai me aiki, kuma ma yawanci one day on, one day off nake yi" Umma tace "Toh shkkn Allah ya taimaka, karatun fa?" Yace "Xata fara in sha Allah" Umma tace "Toh maa sha Allah, Allah ya taimaka" Abinda Abuturrab bai so bane ya faru don sai da la'asar din yayi yana gidan, dakin Ahmad ya tafi yin alwala, Ahmad dake ta jiran ya shiga alwala ya jawo makullansa na gida bayan ya shiga bandaki, cikin few seconds yayi abinda xai yi ya ajiye sauran sannan ya fita dakin....
Chapter 60 · 0% Book details