← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 205

Sashe 52

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

ke xaune, smiling broadly yace "Latest ango in town" mikewa Abuturrab yyi yana kallonsa yace "In ur life Ahmad.... I mean in ur life don't ever abuse me the way u did earlier today, i felt really bad at that" Ahmad ya masa Wani kallo kafin ya fara dariya irin wanda ke kufular da mutum yace "Toh Alhaji Ibrahim, ae da ka xo da bulala koh?" a fusace Abuturrab yace "You caused me all this mess sannan ka fi kowa yi min dariya?? Who does that Ahmad?" Ahmad ya buda baki hade da xaro ido yace "Ta yaya na janyo maka?" Abuturrab na huci yace "Ohk, i will tell u now, ka xata da baka fara kai ni gun yarinyar nan ba da akwai wani abun da xai hadani da ita balle taimakona ya dawo min sharri?" Ahmad yace "Da na kai ka gun yarinyar sai nace ka xaga ka bi ta baya ka dinga xuwa wajenta ba tare da na sani ba? Ina ce ranan har Umar sai da yace yana ganinka a unguwar Hayi ka mu sa don kada ma in dago komai" Dariya sosai Ahmad yyi har da gyara xama yace "Gaskiya na dade banga me abun dariya irin ka ba Captain, da naje siyan awara sai nace ka dinga xagayawa kana xuwa gun me awara?? just take a look at the distance daga cikin gari xuwa Hayin rigasa amma haka kullum kake jan motar kaje shine xaka xo nan yanxu kayi wani blaming dina, ni da ma aka munafurta ana ta xuwa tadi ta baya ban sani ba, ban ji haushi ba sai kai?" Kallonsa kawai Abuturrab ke ta yi yana jin kamar ya shakosa, Ahmad ya sake wani shegen dariya har da buga table yace "Toh ai dai yanxu ka rigani sanin aure hankalinka ya kwanta, mu ma Allah ya nuna mana namu da wuri wuri haka..." Komawa Abuturrab yayi ya xauna xuciyarsa na mugun tafarfasa, Ahmad sai satan kallonsa yake yana yar dariya, Calmly Abuturrab yace "Dama Aunty na yawan tagging taimako da xama sharri a rayuwar nan, and i have seen that clearly now don ya faru a kaina, assuming i ignore and act as if i didn't see anything da duk hakan bai faru da ni ba, kuma am making this vow today.. ni Aliyu duk inda na ga wani na neman taimako idan ya wuce na kudi, shi ma kudin sai nayi naxari me xurfi a kai, to wllh wllh i will never ever render that help" Ahmad yace "Calm down man, wannan taimakon fa bai xame maka wani sharri ba illa ma lada me yawa da ka kwasan ma kanka idan Allah ya yrda, da ma nine na kwashi wannan ladan wllh, i cant imagine how happy i will be, sannan sharrin dake ciki a naka tunanin ba dai auren yarinyar dake kanka bane??" Abuturrab na kallonsa da kyau yace "Babu wani aurenta a kaina yanxu, ni d'an iska ne da xan bar aurenta a kaina" Da mamaki Ahmad ke kallonsa, can yace "Ban gane ba" Abuturrab yace "U heard and assimilate me right, babu wani aurenta a kaina" Ahmad ya mike yana kallonsa da mamaki yace "Kana nufin ka saketa Aliyu?" Abuturrab yace "Toh me xan jira, ko don dariya da jest making irin naka da mutane ire iren ka ai dole inyi hakan in samar ma kaina kwanciyar hankali" Ahmad ya fito ya xauna gefen Abuturrab on a serious note yace "Stop it plss captain, da gaske ka saketa?" Abuturrab yace "To wai jiran me xan yi, idan ba ina da intention din auren nata bane dama, i have nothing to do with that girl as a wife, gwara kawai in xama guardian dinta, and that's what i am doing right now..." Ahmad ya dafe kansa yace "Ya salam... amma da baka yi haka ba Captain, why will u do that pls???" Abuturrab yace "You are not to tell me what to do and what not to do, so ka ke in cuci kaina in kwari kaina, ina aka ta6a irin wannan taimakon, i just have to saboda kwanciyar hankalina" Kallonsa kawai Ahmad ke yi gaba daya expression dinsa ya nuna ko kadan bai ji dadin sakin jiddah da yace yayi ba, Bayan few seconds yace "Kuma ta sani, i mean ta san ka saketa?" Abuturrab yace "Of course a gabanta nayi na mika mata sannan na amsa na ajiye" Ahmad ya girgixa kai yace "Wllh banji dadin hakan ba Abuturrab" Wani kallo Abuturrab yayi masa sannan ya ja tsaki ya mike ya nufi kofa, Ahmad ya bisa da kallo yace "Amma kuma xamanku a gida daya baxai ta6a yiwuwa ba, ko don hakan ma ni da kaina xan sanar ma su Umma cewar babu aure tsakaninka da Jiddah, I can't pretend over this in cuceta, idan baka san addini ba ni na sani" Dawowa Abuturrab yyi yana kallonsa da kyau, calmly yace "And this will bring the end of our friendship Ahmad, i told you my secret because i trust u, and I'm sure u won't betray my trust, addini kuma da kake cewa ina ga sai dai mu goga a kan saninsa da ni da ke, bbu abinda xaka nuna min... Baka isa kuma ka koya min yanda xanyi da rayuwata ba" Daga haka ya nufi kofa ya fice ya kulle masa kofar. Daren ranan Abuturrab na xaune hotel room dinsa dake kano after isha yana shan shayi a hankali, tunawa yyi daxu da yamma ya kira wayar wajen Jidda bata daga ba, ya sake kira da magrib ma no answer, ya kalli wayarsa dake gefensa ya dauka ya sake dialing number, har ya katse no answer, haka nan kawai yaji his mind has lost rest, kallon wayar ya dinga yi, can ya sake kira nan ma har ya katse no answer, kallon agogon jikin wayar yyi yaga takwas ya wuce, sake dialing yyi nan ma har ya katse no answer, ajiye cup din hannunsa yyi, ya shiga kiran wani pilot hoping to reach him don yasan he might be up in the sky now, jin captain Musa ya daga, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Captain baku tashi har yanxu ba?" Captain din yace "About to... in few minutes time, ya gajiya?" Abuturrab yace "I think i will have to follow you to kaduna now" Da mamaki pilot din yace "Baxa kayi piloting jirgi gobe da safe ba, and hope all is well?" Abuturrab yace "Sure alhmdlh, jirgin gobe na sha daya ne, i don't have early morning duty" Musa yace "Toh shkkn, ka taho yanxun nan kasan basu fiye son jira ba, in some minute time xamu yi take off" Abuturrab yace "In sha Allah" Cikin few minutes ya shirya cikin kananun kaya Hoping not to miss the private flight going to kaduna, cikin ikon Allah ya isa, kuma suka daga sama, within some minutes suka sauka a garin kaduna, a motar Musa dake airport din kaduna suka shigo cikin gari, Musa ya kawo Abuturrab har layinsa ya sauka yana masa godiya, Musa yace "Sai mun hadu Wednesday in sha Allah" Abuturrab yace "Sure in sha Allah, thank you" daga haka suka yi sallama ya karasa cikin layin da kafa, makullin gidan ya fiddo a aljihunsa ya bude sannan ya shiga, har ya isa main entrance nan ma ya bude sannan ya shiga parlor, wutan parlon a kunne yake parlon sai kamshin turaren wuta yake, ko ina na nan ynda ya barsa jiya, kuma babu alamar ana xama cikin parlon ma, karasawa yyi sama yana kallon kofar dakinta ya murda a hankali ya shiga, babu kowa cikin dakin ya bude ido sosai sai dai lkci daya yayi calming kansa jin kamshin sabulu a dakin, coz he is a very sharp percipient, bin dakin ya dinga yi da kallo yana duba inda xai ga wayar amma bai ga alamarsa ba, can kusa da window ya nufa ya tsaya hade da rungume hannunsa ya daure fuska, bayan few seconds ta bude kofar bandakin, ta fito daure da towel, bata ko kalli direction din da yake ba ta nufi gaban mirror, sai a sannan ta ga mutum ta madubi wani ihu ta fasa da karfi ta nufi bandakin a guje ruwan kafarta ya sa tsantsin tiles ya kwasheta ta fadi nan bakin kofar bandakin, da sauri Abuturrab ya nufeta ya durkusa kusa da ita ya dagota yace "Ke nine fahh" wani kuka ta fashe da bayan ta kare masa kallo ta tabbatar shi din ne, tana rike da towel din jikinta gam tace "Wayyo kafata, wllh kila nayi targade, wayyo Baabarmu" Komawa baya yyi yana kallon kafar, ya mike yace "Tashi tsaye" Tana girgixa kai hawaye na sauka idonta tace "Ni baxan iya ba wllh" Ya kamata ya dagata, lkci daya ya hade rai yace "Wani kafar ne kika yi targade" Ta nuna masa right leg dinta, gefen gado ya xaunar da ita ya duka yana kallon kafar, ita dai hawaye kawai take tana hade laps dinta tana kallonsa, wani kallo ya mata ta sunkuyar da kai da sauri, mikewa yayi ya nufi gaban madubi don yasan ya siya mata man xafi ranan da suka yi shopping incase she will need it, a hankali tace "Don Allah ka yi hakuri ka miko min hijabi na" Ya dau man ya juyo ya dawo kamar bai ji ta ba, ta marairaice tace "Hijabina nace" Yace "Ki bari in duba maki kafar in ga babu targade, yau duk kukan karyar nan da kike ma mutane sai ya dawo na gaskiya, kuma xaki gaya min inda kika jefar da wayar da na baki" Shiru tayi bata ce komai ba, ya duka ya bude man ya diba sannan ya kama kafar da tace, wani ihu tayi ya ja kafar da karfi, har kasa sai da ta sauko tana kokarin kwace kafarta sbda axaban da take ji, ganin da gaske ta ji ciwon yasa yace "A hankali fa nake maki amma wllh idan kika sake ta6a ni xan yi da karfi" hawaye na sauka idonta tace "Wllh xafi yake min sosai, don Allah ka rufa min asiri kayi hakuri" Ya daure fuska ganin xata sake kai hannunta kan nasa yace "Kin xata wasa nake maki" Da sauri ta dauke hannun, duk da
Chapter 52 · 0% Book details