← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 205

Sashe 157

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 5 min read

ci wllh... Tun daxu sai nukurci take, taki sakewa" Abuturrab yace "Kyaleta, a nan xaku kwana" Hajja ta gyara xama tace "Atoh dai" mikewa yayi ya fita don xuwa yayi alwala ya wuce masallaci. Har kusan isha Jiddah bata ga alamar Hajja xata ce su tashi su tafi ba, ga wani abincin Abuturrab ya kawo, bayan ta idar da sallah tana xaune kan darduma a hankali tace "Hajja wai baxa mu wuce ba?" Hajja tace "Ke ba fa gidan 6are na xo ba, bari kiji in gaya maki, ni wllh bansan bakin hali gareki ba sai yau, gidan jikana ne nan fa, babu ruwanki da sanda xa mu wuce, ke dai iyakarki ba rakiya ba, xan kawoki inda xa a cuceki ne? Ni fa na rainesa yana karami, idan ban xo gidansa ba ina xanje, kuma a nan xan kwana wllh don xuwa gobe da safe nake son ganin iyakar xabiyar matarsa da ta xo ta gaishe mu a tsattsaye har yanxu bata sake shigowa ba, dadin abun kuma jikana ya saurareni gashi muna ta hiran yaushe gamo da shi don haka sai Allah ya kai mu gobe xan nuna mata ni er banxa ce" Jiddah ta ji kamar ta fashe da kuka, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta mike ta koma can karshen gado ta xauna, Hajja ta kwashi take away din da suka ci abinci ta fita xuwa kitchen, Sai a sannan Jiddah ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa, bayan kusan minti goma Hajja ta shigo dakin tana hura hanci tace "Tirrrrrr, ashe kazama Aliyu ya auro? Ke kinga kitchen dinta duk wari kuwa? Wllh da nasan haka kitchen din yake ni baxan ma fara shan ruwan gidan nan ba sai dai a fita a siyo min a waje, a garin yaya mace xata bar kitchen dinta haka ni Dije? Wllh sai da tsoro ya kamani, yaushe Aliyu shi ma ya lalace da son kazanta? A yanda na san sa a da fa har tunani muke ko aljanun tsafta ne suka auresa, to naga duk ya lalace ya xuba ido kitchen dinsa ya ru6e duk wari" Jiddah dai bata ko kalleta ba, Hajja ta xauna tayi shiru alamar dai tunanin kitchen din take kuma abun ya dameta, can tace "Tirrrr" Sai kuma tace "Huhuhu kazama ce wllh, kwanukan duk wari naji suke, ni kamar har da kiyashi naga suna yawo a kitchen din, ga dai kitchen har kitchen" Sai kuma ta kalli Jiddah murya can kasa tace "Wllh ban san ta ina xanyi wanke wanken bane kar inje in jika kitchen din abu ya kara lalacewa ai da nayi, amma ke tunda naga duk kun saba ki daure domin bama tsafta hakkinsa kije kiyi wanke wanken nan, wllh babu kyan gani kinji na rantse, to ko dai ba mace ya auro ba" Jiddah tace "Hajja bata sa ni in mata wanke wanke ba fa" Hajja ta kara yin kasa da murya ta marairaice tace "Na sani er nan, duk don a fita hakkin tsafta ne, wllh da Masar ne kitchen din nan ya tashi aiki, sai ma a iya rushesa kawai, domin Allah ki tashi ki je ki gyara, ai ba don yar iskar xa muyi ba, kawai don Allah, don tsafta xa mu yi" Jiddah ta dinga kallon Hajja, Hajja ta mike tace "To ai Shikenan bari in kwashi kwanukan in fita da su tsakar gida in wanke don a gaskiya idan xa su kwana a haka ni baxan kwana gidan nan ba ba ruwana, baxan ci amanar tsafta ba a gaskiya" Ganin da gaske fita xata yi Jiddah ta mike tace "Toh naji xanyi" Hajja ta koma ta xauna tana huci, Jiddah ta fita dakin, babu kowa parlon ta shiga kitchen din, tafi minti uku a tsaye tana tunanin ta inda xata fara, sai yamutse fuska take, can dai ta fara hada kayan wanke wanken waje daya.. Har karfe tara Jiddah na kitchen din, lkci daya kitchen din ya dawo fess duk ta gyara ko ina ta goge, tana wanke wajen sink din aka dauke wuta, lkci daya kuma taga kamar an kunna hasken waya a parlor, ko gama dauraye wajen bata yi ba ta kashe tap din xata fito kitchen din da sauri, ta kusa cin karo da shi, ta ki tsayawa xata bi ta gefensa ya rikota, kwace hannunta take son yi, ya ja ta xuwa kitchen din ya kulle kofar ya jinginar da ita jiki, ta buda ido sosai tace "Meye haka" ya kife wayarsa saman cabinet din kitchen ta daina ganin hasken komai, a tsorace tace "Wai meye haka" yace "Me ya hanaki cin abincin da na kawo maku??" Xuciyarta na bugawa tace "Ni wllh na ci kadan, ai nace mata na koshi ne, amma kuma na ci ai..." Gaba daya ta daburce, yace "To ni dodonki ne da kika ce baxa ki kwana a gidana ba" Ta dake tace "Toh ai ba dole sai na kwana a gidanka ba, ko ya xa ayi in kwana a gidan wanda ban sani...." xaro ido Jiddah tayi jin goshinsa a nata tana juyo breathing dinsa, sai kuma ta rufe ido a tsorace tana turasa da duk karfinta tana son kwace kanta amma ko gezau, bata ankara ba sai ganin abun tayi kamar a mafarki, and he gave her a perfect french kiss da ya gigitata ya rikitata, ba don rikon da yayi mata ba da tuni ta kai kasa dama.
Chapter 157 · 0% Book details