Sashe 142
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 5 min read
tace "Toh tashi ki fita, shi kuma xan ga uban da xai sake dawowa da shi gidan nan ai..." Mikewa Jiddah tayi ta fita, sai da ta kulle kofar Aunty Nafisah tace "Hajiya ni ban ga wani aibu ba don yayi magana da ita, ba fa rabuwar tijara ko rashin mutunci suka yi ba,, assuming he meant any harm toward her da tun farko bai shiga rayuwarta da xummar taimaka mata ba har ma iyayensa su santa, kawai dai abubuwa sun faru ne yanda Allah ya tsara amma kar kice xaki raba xumuncinsu...." Umma tace "Ni fa bance ta masa rashin kunya ko taki girmama sa ba Nafisah, kawai so nake ta rike maraicinta tayi abinda ke gabanta wato karatu, ganin cewar ita ba class dinsa bane yasa yayi mata duk abinda ya mata ba wani abu ba, ba gashi dai yanxu ya auri class din tasa ba, to a kan me xa ta ci gaba da sauraronsa?" Aunty Nafisah tace "Toh Allah ya kyauta" Umma tace "Ameen" Aneesah na xaune parlor tare da kawayenta uku dake ta shirye shiryen tafiya, duk sun cika parlon da surutu ita dai bin su kawai take da um um, amma tayi nisa tunanin da take, duk da how moody she is throughout d day bata yarda kawayenta sun lura ba, bude kofar parlon aka yi duk suka daga kai, Abuturrab ya shigo da sallama da shi kadai yaji kayansa, kallonsa Aneesah ta dinga yi babu ko kiftawa, ya karasa cikin parlon yana kallonsu Fauziyya with smile on his face yace "Kun yini lafiya" Fauziyya tace "Lafiya lau ango, jiya kuma sai muka ji ku shiru shiru kai da abokanka..." Abuturrab yace "Ohh yeah, toh kun ki bar min mata ku tafi, and all my frnds that are suppose to escort me sun koma saboda aiki, shi yasa nace to bari dai nasan xuwa yau xa ku tafi ku bar min amaryata, na daga kafa jiya, amma ashe i am mistaken kuna nan dai" Dariya duk suka yi banda Aneesah da ta kauda kanta imagining how to punish him, Fauziyya tace "Da ka kwantar da hankalinka ma yanxu shiryawa muke xa mu wuce in sha Allahu" Yyi murmushi yace "Toh ba sai na haura sama ba kenan bari in jira ku a mota, sai in ajiye ku train station...." Naja tace "Mun ko gode Captain" Ya d'an saci kallon Aneesah suka hada ido ya kashe mata one eye, ta wani sha kunu, ya juya ya fita parlon, har bakin motarsa ta raka kawayen nata da jakunkunan kayansu, a kan kafada ta yafa gyalen yyi mata kallo daya ya kauda kai duk kawayenta suka shiga motar suka sallami juna sannan ya kalleta sai na dawo, bata tanka sa ba ta shige gate din gidan, ya ja motarsa ya wuce. Aneesah na komawa ciki ta haura sama ta shiga parlonsa ta dau wayarta ta kira Aunty, aunty na dagawa tace "Ya dawo?" Tace "Ehh yanxu ya shigo, amma ya tafi kai su Fauziyya tashan jirgin kasa" Aunty tace "Toh kar ki wani nuna masa komai, kiyi kamar abinda yayi jiya bai baki haushi ba kinji, kiyi hakuri... Sannan ki kula duk yanda Safara'u ta ce maki haka xaki yi anjima kada ki yarda mistake ya shiga..." Aneesah tayi kasa da murya tace "Amma Aunty he is so smart kin sani" Aunty tace "Smart din banxa, ke dai kiyi abinda aka ce maki kawai" tace "Toh shkkn" Aunty tace "Yanxu dai kawai muyi waya gobe" Aneesah tace "Allah ya kai mu" Daga haka ta katse wayar, shiru tayi tana naxari iri iri a ranta, can tayi murmushi ta mike ta shiga daki. Abuturrab na ajiye su a train station din rigasa ya ciro dubu ashirin din da yayi withdraw kafin ya je gida ya mika masu, nan kuma yayi masu sallama yayi wucewarsa ba tare da ya damu yasan ko akwai jirgin ko babu ba, a ransa yace idan ma babu sai su wuce park, a hankali yake driving ya shiga d'an layin wanda ke shimfide da kwalta, dai dai layin gidan mai anguwa ya samu waje yayi parking sannan ya sauka ya karasa layin da kafarsa, saman tabarman dake kofar gidan ya xauna bayan ya gaisa da dattijan da suka wayesa a wajen, yana jiran mai anguwan da aka ce masa ya shiga gida ya fito yanxu, wani dattijo yace "Ya iyalin naka?" Abuturrab yace "Lafiya lau Alhmdlh" Dattijon yace "Madallah, Allah ya maka albarka" Abuturrab ya sunkui da kansa yace "Ameen" ba a dau lkci ba mai anguwan ya fito, ganin Abuturrab yace "Ikon Allah, sannu da xuwa Malam Ali" Abuturrab ya gaishesa da ladabi bayan ya xauna, mai anguwa yace "Ya kaje gida ranan? Nayi ta kiran layinka baya shiga kuwa" Abuturrab yace "Allah sarki, Ina jin na kashe wayar ne" Mai anguwa yace "Toh madallah, ya aiki fa...." Abuturrab yace "Aiki Alhmdlh, Dama na xo tasha ne shine nace bari in karaso mu gaisa" Mai anguwa yace "Ai ko mun gode Malam Ali, ya iyalin taka dai?" Yace "Lafiya lau" Mai anguwa yace "Toh Allah ya kauda fitina, ya ci gaba sa baku xaman lafiya" Abuturrab ya amsa da "Ameen" sannan ya ciro kudi aljihunsa ya ajiye nan gabansa yace "Toh xan koma in sha Allah, sai kuma wani lkcn" Mai anguwa ya rike ha6a yace "Baka gajiya Malam Ali??"