Sashe 62
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jiddah ce xaune bedroom din Umma dake mata tambayoyi, ita dai ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Kar kiji komai ki fada min gaskiya Jiddah" Tayi murmushin karfin hali ta dago kanta tana kallon Umma tace "Da gaske ba komai Umma" Umma tace "Kin tabbatar?" A hankali Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace "Yace ya kawo maki mai aikin haka ne?" Ta kalli Umma sannan cikin sanyin murya tace "Eh" Shiru Umma tayi tana kallonta don sai take ganin kamar ba gaskiya take fadi ba, tausayin Jiddah take a xuciyarta, ta kwantar da murya tace "Ni baxan ce masa mun yi maganan komai da ke ba Jiddah, ki bani amsan tambayoyina kafin su dawo masallaci yanxu" Jiddah ta kuma wani murmushi tace "Umma na baki amsan ai" Umma tace "Toh kina jin dadin xaman gidan?" Kallonta Jiddah ta dinga yi ta kasa cewa komai, Umma tace "Ina saurarenki..." Lkci daya hawaye ya kawo idonta, dai dai nan aka bude kofar dakin, Ahmad ya shigo tare da Abuturrab, sosai gabansa ya fadi, ya kalli Umma sannan ya kalli Jiddah, Umma dai ta daure fuska tana danna wayarta, Ahmad dai na tsaye bakin kofa bai karaso ba, ya dinga fatan Jiddah ta sanar ma Umma bata boye mata komai ba, Abuturrab ya shafa kansa a hankali yace "Umma dare na yi xa mu wuce gida" Umma tace "Ohk" wasu sabbin hawayen ya dinga sauka idon Jiddah, gaba daya Abuturrab ya kasa nutsuwa, kana ganinsa ka ga mara gaskiya, Umma na kallon Jiddah tace "Tashi ku je sai da safe" Ta kalli Abuturrab tana goge idonta, ya jefa mata wani kallo a fakaice, a hankali ta mike hawaye yaki tsaya mata tace "Sai da safe Umma" Umma bata iya ta amsa ba Jiddah ta nufi kofa, Abuturrab na kallon Umma yyi kasa da murya yace "Sai da safe Sai Umma" Ba tare da ta kallesa ba tace "Allah ya kai mu" Ya kalli Ahmad that is still standing wanda har ransa yake jin hawayen da jiddah take, Abuturrab ya ki ce masa komai ya fita dakin, Maimuna da siyama ne suka dau ma Jiddah abubuwan da Umma ta hada mata tun daxu xuwa motar Abuturrab, Jiddah dai na xaune gaban motar kamar ana dada tunxurata da kukan da take, Abuturrab ya tada motar ya bar gidan, sai a sannan ya sauke ajiyar xuciya, he even love it da Umma taki ce masa komai, har suka isa gida bai ko kalli Jiddah ba, yana parking ya sauka ya tafi ya kulle gate din gidan ya dawo, tsaye ya ganta jikin motar fuskar nan nata kamar warce aka aiko ma da sakon mutuwa, ya hade rai yace "Ni xan dauko maki kayan naki dake cikin motar" ta juya ta bude bayan motar tana goge guntun hawayenta ta dau ledan hijabs din da Umma tayi mata da warmer din tuwo da miyar kuka da Umma ta sa a xuba mata, da harara ya bi ta yace "Xaki ga ko xaki sake leka kofar gate din gidan nan balle har in kai ki gidan Umma ki samu daman hawayen iskanci" Kamar jiran jin hakan take ta fashe da kuka sosai tana kallonsa tace "Don girman Allah kayi hakuri, wllh kewarta nake bana son in rabu da ita shi sa nake kuka, don Allah kayi hakuri" ko tanka ta bai yi ba ya nufi kofar shiga gidan ta bi bayansa da sauri tana kuka, ko tsayawa bai yi a parlor ba ya wuce bangarensa, ta shiga dakinta ta ci kukanta me isarta bayan ta sannan ta kwanta. Karfe sha daya da kusan rabi yayi knocking kofar dakin ya shiga, ganin tayi bacci ya bude warmer din abincin da ta ajiye kasan dakin, yaga bata ta6a ba duk da yasan ta ci abinci a can gidan, ko kayan jikinta bata cire ba, wannan dalilin ne yasa ya tasheta, mikewa xaune tayi da sleepy eyes dinta tana murxawa, yace "Me ya hanaki wanka kafin ki kwanta?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Dama bakya wankan daren da nace maki kenan?" Da sauri ta bude ido sosai tace "Wllh ina yi bansan sanda nayi bacci ba" Yace "Toh tashi kije kiyi wankan" Kallon agogo tayi da sauri, ya hade rai yace "Tashi nace" A sanyaye ta mike xata shiga bandakin yace "Da kayan xaki yi wanka?" bata ce komai ba, amma ta ki cire kayan a gabansa, ya daure fuska yace "Ba magana nake maki ba" Ta d'an kallesa tayi narai narai da ido tace "Tawul din yana bandaki ne" tana fadin haka ta shige bandakin, gefen gadon ya xauna yana naxarin maganganun da Umma tayi masa a waya bayan sun dawo gida, he is finding it hard to forget her words and move own, yasan no matter what Ahmad baxai ta6a gaya mata xaman da yake da Jiddah a gidan nan ba, yasan baxai ta6a ce mata ma bbu aurensu da Jiddah kamar yanda ya sanar masa ba, but her words carried weight this night, he have a very good intention toward jiddah, ba shi da nufin ya cuceta ko ya walakantata ko ya saka rayuwarta a garari, his intentions are nothing but pure, dafe kansa yyi, lkci daya ya dago jin wayar dake hannunsa yayi vibrate ya duba ya ga Aneesah ce ke kiransa, bai sake kallon wayar ba coz sun yi magana not too long, bayan kusan minti sha biyar jiddah ta fito daga bandakin sanye da kayan da ta cire, kasa kallonsa tayi ta ja gefe ta tsaya, wani kallo ya dinga mata kafin yace "Meye hakan kika yi?" Ta ki yarda su hada ido tace "Ni baxan iya fitowa babu kaya ba bayan kana xaune dakin" Daga sama har kasa ya dinga kallonta yana mamakin abinda ta fada, can dai yace "Ke kina da wani abinda xaki boye min a jikin ki dama, kwaila da ke?" Ta d'an turo baki ta juya masa baya, Tsaki yyi ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo, murya can kasa tace "Eh amma ai ni ba muharramarka bace da xan cire kaya...." Ganin ya juyo tayi tsit, ganin impression din fuskarsa gabanta ya fara faduwa, yace "Kika ce me?" Ta girgixa kai da sauri tace "Ban ce komai ba" Dawowa dakin yyi, ta marairaice tana kallonsa tace "Don Allah kayi hakuri ni bance komai ba" Yace "Kika ce ni ba muharraminki bane?" Ta girgixa masa kai da sauri bakinta na rawa tace "Aa bance haka ba" Sai da ya iso gabanta ya tsaya, sbda tsoro taji ta ma kasa tsayawa, calmly yace "A ina kika san wanda muharraminki ne da wanda ba muharraminki ba?" Jin taki cewa komai ya mata wani tsawa da yasa ta duka hawaye ya kawo idonta, yace "Idan baki bani amsata ba na fara ball dake sai kin ganki downstairs yanxu" Cikin rawan murya tace "Ai da ina xuwa islamiyya" Ya gyada kai yace "A islamiyyan kuma basu sanar maki hukuncin wanda yace xai kashe kansa ba?" Kasa cewa komai tayi, ya wani hade rai yace "Mike ki cire kayanki" Ta sake marairaice masa amma ganin kallon da yake mata ta mike da kyar, ta gefen ido ta kalli bandakinta, lkci daya kamar kiftawan ido ta shige ta sa makulli hannunta na rawa, ya dinga kallon kofar, can yyi murmushi yana shafa kansa, lkci daya kuma ya hade rai ya fice daga dakin, bai karasa bangarensa ba wayarsa yyi vibrate ganin me kiransa sai da gabanaa ya fadi, har ya katse bai dauka ba, sai da aka sake kira sannan ya daga, murya can kasa yyi sallama yace "Ina yini Aunty" ba tare da ta amsa ba tace "Aliyu kana ina??" ya d'an bude ido yace "Aunty ai ina kano, ban dawo ba..." Bude kofarsa yyi ya shiga ya kulle hade da lumshe ido jin abinda take cewa. Washegari da safe wanda Abuturrab ya sa ya samar masa mai gadi ya iso gidan da mai gadin, Abuturrab na kallon matashin mai gadin yace "Yaranku nawa da matar taka?" Mai gadin yace "Daya ne kawai Alhaji, sabon aure ne" Abuturrab yace "Ba damuwa, yau nake son xaka fara aikin sai ka koma ka taho da iyalan naka" Mai gadin ya risina da ladabi yace "Toh nagode Alhaji, xan je kauyen namu yanxu sai in taho da su in sha Allah, Allah ya saka da alkhairi" Abuturrab yace "Ameen, amma kada ka wuce karfe biyar na yamma don xan koma gun aiki a yau" Mai gadin yace "In sha Allah Alhaji" dubu biyar Abuturrab ya basa kudin motar xuwa taho da iyalan nasa, shi ma wanda ya kawo sa ya basa dubu biyar, bayan sun tafi ya koma cikin parlor.... jiddah na kitchen tana dumaman tuwon da umma ta bata jiya, yatsine fuska yyi yana kallon kitchen din don ko by mistake baya son warin miyar kuka, barin ma yanxu da take dumamawa, hakan ya sa ya dau makullin motarsa ya bar gidan xuwa inda xai je yyi breakfast, jiddah na jin fitan motarsa ta jigina jikin bango tunda taji yana waya ko minti sha biyar ba ayi ba yace yau xai koma gun aiki ta ji duk mood dinta ya canxa, gaba daya bata son xama ita kadai a gidan, a sanyaye ta kashe gas din ta xuba tuwon amma ta kasa ci, Duk da xamansa a gidan da rashin xamansa kusan daya don ba wai wani magana me tsayi yake mata ba, kuma ba waje daya ma suke xama ba amma idan yana gidan bata jin kadaici da kewa na damunta, duk sonta da tuwon saboda yanayin da ta shiga sai ta kasa ci da yawa, haka nan ta mike ta kai kitchen ta wanke plate din, sama ta wuce ta wanke bakinta, komai da take yi a gidan tayi, turaren wuta ne kawai bata sa ba, ta dau turaren ta sauka parlor ta sa sannan ta xauna tana kallon yanda yake fita a hankali, kana ganinta kasan jikinta a sanyaye yake, bude kofar parlon aka yi Abuturrab ya shigo ta daga kai ta kallesa sannan ta sauke idonta, sai da ya karaso cikin parlon tace "Sannu da dawowa" Bai amsa ba yyi wucewarsa sama ta gefen ido ta bi sa da kallo har ta daina ganinsa, a sanyaye ta mike