← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 205

Sashe 91

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty ce ta shigo parlon Ummi duk da mutane da ke parlon ta ra6a xuwa cikin daki, Ummi na ciki tana bada sako, Aunty ta ja gefe ta jira har ta gama bada sakon sannan tace "Jiya kaina ya dau xafi kika xo kina tambayar Jiddah, to kin dai ganta ko?" Ummi tace "Mijinta ne ya dauketa" Still Aunty tayi tana kallon Ummi, trying to assimilate tace "Abuturrab din?" Ummi tace "Eh" Juyawa Aunty tayi ta fita daga dakin xuciyarta na tafarfasa, lallai Abuturrab ya gama rainata... Through out ranan da ya kasance mothers eve Jiddah na gida ita kadai, kuma ko a jikinta, sai yanxu ta gane xaman gidan da take ita kadai ma gata ne ashe, xamanta 24/7 a gida babban Rahama ne gareta, tun da Abuturrab ya ajiyeta ya tabbatar ta shiga ciki ya tafi bata sake ganinsa ba. Karfe shiddah saura na yamma bayan sun dawo daga babban event center din da suka yi booking against tomorrow's dinner, su biyar ne a motar, wani abokinsu Umar ne ke driving motar, Abuturrab na kallon Umar kafin su isa hanyar da xai kai sa gidansa yace "Umar ka samu waje ka ajiye ni a restaurant din gaba..." Ahmad ya kallesa da sauri, kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "Me xaka yi a restaurant bayan abincin da muka ci yanxu?" Abuturrab ya gyara xamansa babu yabo babu fallasa yace "Eh xan amshi abinci in wuce gida" Ahmad yace "Me xaka je kayi a gida?" Abuturrab yace "Kamar ya me xanyi a gida? Naga it's almost magrib yanxu ko kana nufin saboda gobe daurin aurenka sai in bar gidana in kwana a wajenka?" Murmushi Ahmad yyi yace "Kai dai ka fadi gaskiya, dama Ummi ta shaida min abinda kayi masu, kawai dai baka son ka bar matarka ta kwana ita daya a gidan, shine xaka amsar mata abinci yanxu ka wuce gida" Abuturrab ya d'an yi shiru idonsa a kan titi yana sake comprehending abinda Ahmad ke ce masa, Umar yace "Ni kuwa yau sai naje gidan Captain naga matar nan tasa mun gaisa" Najeeb ma yace "Same with me... matar da har yau ba wanda ya santa" Da sauri Abuturrab yace "To ai tana gidan biki, sai dai idan can xa mu je" Dariya Ahmad yayi yace "Tana gida bata wani gidan biki, mu je kawai Umar ai nasan gidan" Lkci daya mood din Abuturrab ya canxa amma ya kasa cewa komai, Ahmad na nuna ma Umar hanyar gidan har suka isa, horn Umar yayi mai gadi ya bude gate din bayan ya hango Abuturrab da ya sha kunu cikin motar, Umar na parking Ahmad ya fara sauka, sannan Abuturrab, sauran frnds din nasu uku ma duk suka sauka, tafiya kawai Abuturrab ke yi xuwa entrance din gidan, Ahmad na leading din frnds din nasu yana cewa "Wannan ai ba adalci bane ba a sanar maku biki ba kuma a ki kawo ku gidan amarya" Har wani nishadi yake suna dariya da frnds din suna biye da Abuturrab, Abuturrab na shiga parlon ya dinga bin ko ina da kallo, kamshin girki ne ke tashi a parlon wanda ko ina fess alamar har goge goge tayi bayan dawowarta, kitchen ya nufa ya ganta tsaye kusa da gas, ga miya tana yi a gas din, daga sama har kasa yake kallonta, wanda riga da skirt ne na atamfa jikinta amma ba ankon da ta saka da safe ba, har xai juya ya fita sai kuma ya sake juyawa yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Dama kar ki kuskura ki fito daga kitchen din nan" Bai jira cewarta ba ya fita parlor, su Ahmad na xaxxaune parlon har da kunna TV, Najeeb yace "Duk girkin amarya ne ya cika gidan nan haka, ashe yau xa mu kwashi girki" Ahmad ya hadiye dariyar da ke damunsa ganin fuskar Abuturrab, Abuturrab dai bai ce komai ba ya wuce sama, sai gashi ya sauko rike da folded hijab dinta ya wuce kitchen, mika mata yayi yace "Ki fito ki gaishesu, kuna gaisawa kuma ki wuce sama har su tafi kada ki kuskura ki sakko, saura kuma idan kin xo gaishesu ki xube kasa kamar kina neman gafara" amsan Hijab din tayi tace "Toh" ya juya ya fita, bayan ta saka hijab din ta bi bayansa, kanta a kasa har ta karaso cikin parlon, gaba dayansu kallonta suke, ta tsaya nan bayan kujera, sai kuma ta kasa gaishesu a tsaye don bata saba ba, xagayowa tayi ta xauna saman lallausan carpet din ta gaishesu ba tare da ta kalli kowa a cikinsu ba, amsawa suka yi gaba daya Umar yace "Yau Allah yayi xa mu ga amaryar captain, ashe shi yasan me yasa bai ta6a gayyatomu mu ganta ba" Ita dai kanta na kasa, Abuturrab sai danna wayarsa yake bai ce masa komai ba, Ahmad yace "Toh a kawo mana ruwa matar captain" Kallonsa tayi jin muryarsa, ta d'an yi murmushi sannan ta mike ta nufi kitchen, tray ta dauka ta daura ruwan gora uku da glasses hudu sannan ta fito ta ajiye nan tsakiyar parlon, daga kai Abuturrab yyi ya kalleta ganin tayi abun hankali, he was thinking a hannu xata rike goran ruwan ta kawo, Najeeb yace "Toh ni kuma girkin amarya xan ci" Sosai gaban Abuturrab ya fadi, don ko shi bai ta6a cin abinda jiddah ta girka ba, har Ahmad sai da ya ji faduwar gaba, can dai yace "Bayan wanda muka ci yanxu?" Umar yace "Wanda muka ci daban, wannan kuma na amarya ne" Jiddah dai tayi shiru, Najeeb yace "Ko baxa a bamu ba amarya?" Mikewa tayi tana murmushi ta nufi kitchen, Abuturrab ya kalli Najeeb yace "Yanxu fa ka ci abinci bawan Allah, sannan gwangwani daya ta dafa... ba daga kitchen din na fito ba yanxu, ai bata san xa ku xo ba" Dariya Najeeb yyi yace "Sai ta tsam mana a gwangwani dayan, duk wannan kamshin mu tafi bamu ci abincin amarya ba" Ahmad dai bai sake cewa komai ba, Abuturrab ya d'an saci kallon hanyar kitchen din, bai san lkcn da ya mike ya bi bayanta ba, plate ta dauka ta xuba shinkafar, tana tunanin ko a kai xata sa miyan, amma gidan umma taga waje daban ake sa miya idan an xuba ma baki abinci, hakan yasa ta dau wani bowl din me xurfi ta xuba miyan, tunda ta xo gidan bata ta6a girki da nama ba sai ranan, duk da ba wani girki ma take yi ba tun xuwanta, ganin Abuturrab ya shigo kitchen din ya kulle kofa ta juya da sauri tana kallonsa tace "a saman shinkafar xan xuba miyar?" Ya watsa mata wani kallo yace "Ko kuma a sama kaina ba, ke har wani girki kika iya xaki wani xo ki xuba masu abinci maimakon kice babu kare, ni kike son ki kunyata gabansu?? Ko ruwan shayi ma baki bari ya tafasa ballantana ki iya girki me dadi" Kallonsa kawai take ko kiftawa babu, ya nufi tray din da ta daura shinkafa da miyar, ya dau spoon ya debi miyar kadan ya sa a gefen shinkafar ya juya, sannan ya debi shinkafar ya kai baki, ita dai kallonsa kawai take gabanta na faduwa, ya fi second biyar trying to figure out the taste of the food, sai ya ji girkin kamar na gidan Umma, ko don sbda spices din da tayi amfani da ne, wanda umma ta bada a kawo mata, sake dibar shinkafar yyi ya kai baki, da gefen idonsa ya bi kitchen din trying to be sure ba Umma bace ta aiko mata da abincin, bai ga warmer ko wani abu da xai nuna kawo abincin aka yi ba, ya sake diban shinkafar ya kai baki, rungume hannunta tayi tace "Toh xaka cinye abincin ba a kai masu ba ai" cire spoon din yyi a baki da sauri, ya jefa mata wani kallo, ta koma baya ta turo baki, yace "Wa yayi girkin nan?" Bai san lkcn da yayi tambayar ba, sai yaji tambayar made him sound stupid, daukar tray din yyi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Najeeb ya sauke ajiyar xuciya yace "Ai har mun cire rai nace su tashi mu tafi kawai" Ahmad couldn't hold it any longer, banda dariya babu abinda yake, Abuturrab ya ajiye masu abincin nan middle of carpet yace "Ae nace maku d'an kadan ta dafa, gashi nan tunda yunwa ku ke ji" Najeeb ne ya fara sauka sannan Umar, shi dai khaleel murmushi kawai yake, Ahmad ya mike ya isa gun abincin ya ci spoon daya gabansa na faduwa, exactly tunanin da Abuturrab yyi shi ma shi yyi, kamar daga gidansu aka kawo mata abincin, komawa yayi ya xauna yana murmushi yace "Nima na ci abincin amarya" Najeeb yace "Kafin ka ci na taka amaryar kenan" Umar yace "Wllh u are missing Khaleel kaji dadin abincin nan kuwa" Tasowa Khaleel yyi shima ya ci spoon daya, sosai suka dinga yabon girkin, shi dai Abuturrab na xaune yana kallonsu, sai da suka cinye abincin duk da ba yunwa suke ji ba, sannan duk suka fita xuwa masallaci, Ahmad ne last din fita, kafin ya fita ya nufi Abuturrab yyi kasa da murya yace "Amma daga gidanmu aka kawo abincin nan ko?" Abuturrab yace "What did u mean?" Ahmad yace "Ba Jiddah bace ta girka" Abuturrab yace "Haka ta ce maka??" Juyawa Ahmad yyi ya bi bayansu Umar, Abuturrab ya mike ya dau tray din abincin ya wuce kitchen, har sannan jiddah na tsaye ta jingina da bango, ya ajiye tray din yana kallonta yace "Wa ya aiko maki da abincin nan?" Ta kallesa, a hankali tace "Abincin ya fi karfin ace ni na dafa ko??" Naxarin maganarta ya shiga yi, ta tattara plates da xata wanke a sink sannan ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Sake kallon pot din miyan yayi ya karasa ya bude sannan ya bude na shinkafar, rufewa yayi ya juya ya fita daga kitchen din xuwa masallaci. Ko da suka dawo mosque sun so Abuturrab ya kira jiddah suyi sallama da ita yace ai sallah take, haka nan ko wannensu ya basa kudi ya bata ladan girki, gefen kujera ya ajiye yace "Ta gode" sannan yayi masu
Chapter 91 · 0% Book details