Sashe 179
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 1 min read
bandaki ban san na ma yi stain ba, kuma bedsheet din ma yayi stain" Maimoon sai xare ido take, sai kuma ta kara fashewa da dariya tace "Toh sai yace maki me da ya gani?" Jiddah tace "Ni bai ce min komai ba, kawai xuwa yayi yaje ya siyo pad din" Maimoon ta tabe baki tace "Ai ko shi yaga duhu, yanxu dai wannan pad din sai kiyi wata biyar ma kina amfani da kayanki bai kare ba, har mu ma mun samu, kinsan fa shi ya Aliyu bai iya siyayyan hankali ba, don ma ba pack din gaba daya ya siyo maki ba, amma don Allah da wani ido kika kallesa bayan yaga period dinki" Jiddah ta ji kamar ta fashe da kuka, Maimoon tace "Idan nice ke wllh ko a gyalena fuskewa xanyi ai bani nace ya gani ba" Jiddah dai bata kuma cewa komai ba amma ita kanta tasan taji kunya sosai ba kadan ba, she wish that never happen... Har yamma da aka sallami Jiddah Abuturrab bai koma asibitin ba, Ahmad ne yayi driving dinsu ya maida su gida, Umma har lkcn bata san Jiddah ta fara period ba, balle Ahmad, suna komawa gida Jiddah ta wuce daki ta kwanta sai bacci.....