Sashe 63
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta wuce sama ta shiga dakinta ta kwanta tana kallon fuskarta ta madubin press din dakin. Da yammacin ranan tana tsaye jikin window aka bude kofar dakin, tunda ta kallesa sau daya ta dauke idonta, yana bakin kofar a tsaye yace "Shuka kika yi wajen nan da kike tsayawa ko da yaushe?" Tana wasa da fingers dinta ta girgixa masa kai, juyawa yyi ta bi sa da kallo ganin jakar hannunsa, da sauri ta bi sa tace "Tafiya xaka yi?" Ya juyo yace "Kina bukatar wani abu ne?" Lkci daya jikinta yyi wani sanyi, shi dai kallonta yake yana lura da ita duk a lkci daya, sauke idonta tayi saboda hawayen da ya kawo idonta, yace "Nace kina bukatar wani abu ne" ta girgixa masa kai hawayen dake makale idonta ya gangaro ta juya da sauri ta koma ciki, da ido ya bi ta, kafin ya bi bayanta xuwa dakin, durkushe ya ganta ta daura kanta saman gado, da mamaki yake kallonta, can yace "Ke kina da lafiya kuwa" kin dagowa tayi tana shessheka, ajiye jakar yyi yana kallonta, can ya karasa kusa da ita ya tsaya yace "Tambayar ki nake, kina da lafiya kuwa?" Still taki dagowa, ya daka mata tsawa yace "Baki ji na ne" mikewa tayi hawaye na kai koma a idonta, ya dinga kallonta kafin yace "Me aka maki?" Ta girgixa masa kai, ya mata wani kallo yace "Me aka maki nace?" Cikin rawar murya tace "Ba komai" rungume hannu yyi yana kallonta, can yace "Kina bukatar wani abu ne" Wasu sabbin hawayen na xubo mata cikin rawar murya tace "Tafiya zaka yi ka barni ni kadai babu kowa, alhalin tsoron gidan nake ji" kallonta kawai yake ya ma rasa me xai ce mata, can dai yace "Shine yasa kike kuka?" Ta gyada masa kai tana kallonsa with tears in her eyes, yace "Ohk, ynxu in tafi da ke kenan?" Tayi shiru still crying tana kallonsa, yace "Bude baki ki bani amsa, in tafi da ke kenan yanxu?" A hankali ta gyada masa kai, daga sama har kasa yake kallonta, tausayinta yake ji har kasan ransa amma bai nuna hakan ba, to ina ma xai kai wannan yanxu wani yayi xaton matarsa ce?? Ta ina xai fara tafiya da ita? Ita dai kanta na kasa, bayan few seconds yace "Ina wayar da na baki" juyawa tayi a sanyaye ta nufi gaban madubi ya bi ta da kallo, har ta dauko wayar ta dawo, ta mika masa, amsa yyi ya shiga call log, yace "Matso" ba musu ta matso kusa da shi tana kallonsa, ya hade rai yace "Wayan xaki kalla ba ni ba" Kallon wayar tayi, ta madubin press din dakin ya kallesu, duk tsayinta iyakarta kirjinsa, jin bai ce komai ba sai kallon wayar take ta daga kai a hankali ta d'an kallesa, ganin inda yake kallo ta kalli madubin ita ma, a hankali ta d'an koma baya ganin dab take da shi ta sunkuyar da kanta, dauke idonsa yyi daga madubin, as if bai son maganan yace "Ga number na nan, duk idan kina son wani abu ko kina da wani magana sai ki danna nan sannan ki sake dannawa ki kirani" Kai kawai ta gyada masa ya jefar da wayar kan gado ya nufi kofa ta bi sa da kallo sabon hawaye na taruwa idonta har ya fita, yau din ma ta waje ya kulle kofar parlon duk da kasancewar mai gadi da matarsa da yaronsu dake gidan yanxu. Kuka sosai Jiddah tayi bayan tafiyarsa, taji komai bai mata dadi a duniyar ynxu, kullum ita kadai kamar mayya a gida babu kowa, tun tana tsoro sosai har tsoron ya ragu, tana sallan isha ko abinci bata ci ba ta kwanta ta takure cikin duvet, nan da nan bacci ya dauketa.... Abuturrab na xaune saman gadon hotel wajen karfe goma da rabi, ya gama abinda yake a laptop ya ajiye yana duba agogon wayarsa, call log dinsa ya shiga har yyi dialing number sai kuma ya katse, mikewa yyi ya kashe wutan dakin ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya, jawo wayar yyi ya d'an yi dube dubensa, sai kawai ya shiga call log din yyi dialing number, he just can't because he have a problem with conscience, abu kadan ke sawa conscience dinsa yyi judging dinsa... Karan wayar ya farkar da Jiddah, bacci ne sosai idonta haka dai ta dau wayar dake saman gadon tayi picking sannan ta kai kunne ta rufe ido bata ce komai ba, jin shirun yyi yaww Abuturrab yace "Ni xan gaisheki" ta bude ido cikin muryar bacci tace "Aa" nan da nan ya gane ta fara bacci, ya dai ce "Me kika ci?" Shiru bata amsa ba, yace "Kee?" Tace "Uhn" yace "Kin yi bacci ne?" Kai kawai ta gyada masa ba tare da tace komai ba kamar yana ganinta, shiru yyi, bayan wani d'an lkci yace "Amma sae da kika yi wanka??" Tuni Jiddah tayi nisa baccinta, bayan few seconds yace "Jeeddarh" jin shiru ya katse wayar kawai ya ajiye sannan yayi rub da ciki nan da nan shi ma baccin ya daukesa. Washegari Jiddah na kitchen yau dai shinkafa da miya take yi tunda ya koya mata yanda ake amfani da blender, ji tayi kamar ana bude kofar parlor, ta tsaya kitchen din tana saurare har taji an shigo parlon, da sauri ta fito, ido hudu tayi da Ahmad tare da Maimoon, kallonsu kawai take da mamaki, ya sakar mata murmushi yace "Toh ko dai mu koma ne?" ta girgixa kai da sauri tace "Aa sannunku da zuwa" Duk suka karasa parlon yana kallonta yana murmushi, Maimuna na kallon Jiddah ita ma tana murmushi tace "Sannu da gida Aunty Amarya" Murmushi jiddah ta kirkira ta karaso ita ma cikin parlon, har ranta taji dadin ganinsu, Ahmad ya xauna yace "Ya gidan Jiddah?" A hankali tace "Lfya lau, ina yini?" Yace "Fine Alhmdlh, dama an kawo mai gadi gidan ne?" Kallonsa kawai Jiddah ke yi kafin tace "Nima ban sani ba ai" Tausayinta Ahmad ya ji, can yace "Toh baxa a kawo mana ruwa ba?" Tashi Jiddah tayi tana murmushi a kunyace ta wuce kitchen ta kawo masu har da lemo, tun jiddah na kin sakin jiki, har daga karshe ta sake gaba daya, Ahmad ya dinga mamaki ganin ashe tana da baki, ga zakin murya kamar zaabiya, sosai Maimoom taji tana son Jiddah, har abinci sai da ta kawo masu, ana kiran azahar Ahmad yace mata xasu wuce don yau ma xai koma Abuja, lkci daya mood dinta ya canxa, Maimoon sai taji tausayinta, makullin gidan Ahmad ya mika mata yace "Su Maimoon xasu dinga xuwa taya ki hira a kai kai idan captain din baya gari so kar ki damu kinji" kasa basa amsa tayi don har hawaye ya kawo idonta, dariya ta basa, yyi kasa da murya yace "Amma fa kar ki sanar masa xuwan mu kinji? Wataran idan naxo tafiya xanyi dake daga gidan gaba daya" Ta gyada masa kai, a haka suka tafi duk yanda ta so daurewa ta kasa sai da tayi kuka. Bayan la'asar wajajen karfe biyar ta gaji da xaman dakin da tsayuwar window ta fito, kallon hanyar da xai kai ta part din Abuturrab tayi, tun ranan da suka fito daga wajen bayan ya nuna mata takarda bata sake bin hanyan ba, tsaye tayi tana ta kallon direction din, can dai ta karasa tana tafiya a hankali har ta isa kofar parlonsa ta bude tana lekan ciki, komai na parlon fess ko alamar datti bata gani ba sai wani kamshi ma da take ji, shiga parlon tayi tana bin ko ina da kallo gabanta ya dinga faduwa, can ta karasa wani kofa da ta gani, bude kofar tayi a hankali tana lekan ciki, daki ne da wani babban katifa da bedsheet a kai, babu abinda bbu a babban dakin, karasawa tayi ciki tana kallon wani table da jirgi a kai, xaro ido tayi tana kallon karamin jirgin, dauka tayi da hannu biyu tana jujjuyawa ta kai idonta tana leka d'an windows din jirgin, hotonsa ta gani jikin bangon dakin da fararen kaya ya rike hula tsaye kusa da wani katon jirgi, a ranta tunani ta shiga yi kilan shi ya ta6a ganin jirgi tunda gashi yayi hoto kusa da jirgin, ita dai a sama kawai suke hangosa dan mitsili, kallon fuskarsa ta dinga yi, lkci daya gabanta ya fadi tana ganin kamar xai iya magana a hoton, a hankali ta juya, taga wani kofa ta karasa ta bude ta ga wani makeken bandaki da abu kamar katon glass a ciki har tana iya hango ciki, kwata kwata bandakin ba irin nata bane, ga shi da girma sosai, ko ina a bushe yake sai kamshi bandakin yake, a hankali ta rufo kofar sannan ta bude wani kofar da ta gani daga can end, xaro ido tayi ganin view din, karamin balcony ne, ta dinga bin gidan da kallo daga kasa wanda ke shimfide da carpet grass ga wasu flowers a gefe, sosai wajen ya mata kyau ba kadan ba, ta kalli wani babban gidan dake opposite dinta suka yi ido hudu da wani dake xaune shi ma a balcony, laptop ne gabansa da drink, shi dai kallonta kawai yake, ta Sunkuyar da kanta da sauri ta juya ta koma ciki ta kulle kofar, da sauri da sauri ta koma dakinta. Daren ranan bayan isha Abuturrab na Abuja a gidansa sbda weather bai bari sun koma kano ba, Aneesah ce xaune kusa da shi a dakinsa, yace "Kince kina da lectures da safe, why not sleep now?" Ta hade rai tace "Toh ae it's not a crime idan nayi bouncing lectures din ko?" Ya gyada mata kai yace "Haka ne...." Lamo tayi ta lumshe ido kusa da shi, ya ci gaba da abinda yake, bayan few minutes ta bude ido tana kallonsa tace "In tambayeka mana captain" Yace "Ina jin ki" tace "This days kamar u are not longer eager being with me, why?" ya buda ido sosai yace "Why do u say so?" Ta marairaice tace "Haka naga alama, or do u have anything in mind?" Murmushi yyi yace "Yaushe rabon mu hadu? It's almost 10 days now" ya ja hancinta yace "And ke kin fiye ma mutum jan aji