Sashe 174
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read
night in gaisa da su" Abuturrab yace "Eh xai ma fi" Daga haka suka fita parlon, a hanya Abuturrab yayi masu take away din abinci, El-Basheer na kallonsa da mamaki yace "Aneesah bata yi girki bane?" Abuturrab yace "Ehh bata jin dadi" El-Basheer yace "Toh Allah ya sauwake" Abuturrab yace "Ameen" sai da suka kusa gidan Abuturrab ya fara xullumin condition din da xai je ya tarar da gidan nasa with El-Basheer. Amma ga mamakinsa yana bude kofar parlor yaji wani kamshin turaren wuta me dadi ya doki hancinsa, ga sanyin Ac da ya cika parlon, suka shiga ciki tare da El-Basheer, the parlor was more than clean, banda kyalli babu abinda kayan kallon parlon suke, bin ko ina Abuturrab ya dinga yi da kallo yana mamakin anya gidan nasa ne kuwa wannan, El-Basheer ya xauna yana sauke wani numfashi yace "Gidan Amare daban yake, so cool" Daga sama Aneesah ta sauko da atamfa riga da skirt da ya kamata ta kashe dauri, fuskarta kuma tayi light make up, tayi kyau sosai kamar a sace a gudu, da murmushi ta karaso cikin parlon tace "Sannunku da xuwa, bako muka yi captain" El-Basheer yace "Fatan mun same ku lafiya amarya?" Tana ci gaba da murmushi tace "Alhmdlh, u are welcome" karasawa tayi kusa da captain ta xauna gefensa tace "Welcome my captain" Yana gyara xama yace "Yauwa thank you" Murmushi bai gushe a fuskarta ba ta mike ta wuce kitchen, sai gata ta dawo da ruwan gora biyu da drink sai cups, ajiye masu tayi tace "Ga ruwan sanyi" El-Basheer yace "Thank you Aneesah" Ta xauna one sitter tana kallon captain dake ta danna wayarsa, El-Basheer ya dau ruwa ya fara sha, tace "A kawo abinci yanxu?" Sai da captain ya daga kai ya kalleta jin abinda tace, tayi fari da ido tace "Eh, ko sai anjima" El-Basheer yace "Aa kawo min ni dai, Captain sai ya ci take away din da yayi" Ta mike ta dau ledan take away din ta wuce kitchen tana cewa "Shi ma baxai ci ba, ga dai abinci nayi" Captain ya bi ta da kallo, manyan warmers kusan biyar ta kawo parlon ta dire kan carpet, ta koma ta dauko plates, da serving spoon ta ajiye masu tana murmushi tace "Bismillah" daga haka ta wuce sama, El-Basheer ya sauka kasan carpet yana bude warmers din, Abuturrab ma sae kallon warmers din yake, wani lafiyayyen fried rice ne a warmer daya, dayan kuma wainar shinkafa sai tiriri yake, ga hadadden miyar taushe dake ta kamshi, wani warmer kuma peppered chicken ne that looks so enticing, last warmer din pepper soup din kayan ciki shi ma sai kamshi yake, kallon foods din kawai Abuturrab yake, tuni El-Basheer ya fara diban abubuwan da xai diba, Abuturrab ya ci gaba da danna wayarsa, sai kuma ya mike ya wuce kitchen, ko ina fess a kitchen din babu kayan wanke wanke, ya fara dube duben inda xai ga take away din da ta dauke a parlor bai gani ba, hakan ya sa ya bude kofar kitchen yaga a bola ta jefar, ya fi second biyar yana kallon ledan abincin kafin ya gyada kai ya kulle kofar ya fice daga kitchen din, ya dawo parlor ya xauna, El-Basheer yace "Kai baxa ka diba abincin ba?" Ya girgixa kai yace "Na ci abinci a can gida ai" Yace "Ohkk" Abuturrab da El-Basheer suna tare parlon har kusan magrib, ita dai Aneesah na sama, duk da yunwan da Abuturrab ke ji amma ya ki cin abincin, ana kiran magrib suka yi alwala a toilet din downstairs, Abuturrab yyi mamakin ganin toilet din ma fess, ana idar da sallah bayan sun fito masallaci El-Basheer yace ma Abuturrab xai koma can gida don su gaisa da su Ummi tunda gobe da safe xai koma, Abuturrab yace "Toh bari in dauko makullin motar" yana shiga ciki ya dauko makullin motarsa ya fito suka wuce can gidan, El-Basheer ya nufi bangaren Ummi don gaisheta, shi kuma ya tafi dakin Hajja, Hajja na gyara labulayenta Jiddah kuma na durkushe tana sa turaren wuta a garwashin da Mai aiki ta kawo ma Hajja a kasko, Hajja na ganinsa tace "Aliyu wllh bauchi da naje baka ga wata yar yarinya da na maka sha'awa ba, duka duka yarinyar bata wuce Jiddan nan ba, amma abinda yasa ban ce masu komai ba saboda ban san irin tsaftar yarinyar ba, kaga yanxu shi Bashir warce nake sa ran hadashi da ita nasan tsaftarta, to ita wancan gaskiya ban sani ba" Abuturrab dai bai ce mata komai ba, Hajja tace "Duk kwanan nan da kai nake kwana a raina nake tashi, saboda nasan kana cikin jarabawar auren mata kazama, amma in sha Allahu ka sha kurumin ka ina nan ina maka fafatuka, yanda na samar ma Bashir yar kirki me tsafta kai ma haka xan samo maka, Shi kansa Kabiru yyi farin cikin wannan xabin da nayi ma Bashir, uwarsa kuma babu abinda xance da ita sae dai ta ci kanta ni ba ta ita nake ba... Yanxu Usman nake jira ya dawo inji ynda xa a yi, ko shi ne xai xama waliyyin yarinyar to... Bashir kuma yace min shi dai a shirye yake ko gobe ne a daura, amma ae ba gaggawa ake ba ina laifin ma nan da sati uku" Abuturrab yace "A ina kika samar masa matar?" Hajja ta wani kallesa tace "Aa wannan kuma ba ruwan ka ae, wllh Kabiru yace min ya amince indai Bashir din na so, ae karfin xuwa na Bauchin kenan..." Abuturrab ya shafa kansa ya ki cewa komai, can ya kalleta yace "Toh ban ci abinci ba, yunwa nake ji" Hajja tace "Aa ba ma ga yunwa ba a gidan nan, ga dai abinci kaca kaca ka wani ce yunwa, bari wannan yarinyar Nafisah ta shigo ta xubo maka, naga lafiyayyen girki aka yi a gidan, ae Hauwa dama Allah ya hore mata iya sarrafa hatsi" Yace "Sae Nafisa ce xata ban abinci?" Hajja tace "Aa nima sae in je in xubo maka, meye a ciki" yace "To ita warcan baxata iya xuba min ba" Hajja ta kalli Jiddah dake duke da turaren wuta kusa da ita har sannan tace "To ke tashi ki xuba masa" Jiddah ta wani 6ata fuska, Hajja dae sae kallonta take, can ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido, Hajja ta rike ha6a a hankali tace "Sae naga kamar ta fara kiwiya ita ma, to ni dae fa kar ta sa inji kunya a kan abinda nake shirin yi, ko dai tana boye wasu halayyanta ne ban sani ba" Mikewa Abuturrab yyi ya fita daga dakin... Yana shiga kitchen din ya kulle ta juya tana Kallonsa kamar dama tasan xae biyota, ya rungume hannunsa yace "Yanxu ma ki fita ta inda kika fita daxu" Ita dai bata ce komai ba ta ci gaba da dibar masa abincin a hankali, yace "Bude kofar ki fita nace" still taki kallonsa, tsawa yayi mata yace "Baki ji na ne" Ta kallesa kamar xata yi kuka tace "In fita in je ina?" Yace "Inda kika je daxu" Ganin ya nufota ta tafi ta bude kofar ta fita tana kallonsa xuciyarta na bugawa, banda hasken wata babu wani haske a wajen, fitowa taga shi ma yayi bayan ya kashe fitilar kitchen din, bata san lkcn da ta tattare skirt dinta ba da xumar fallawa a guje yayi hanxarin cafkota da sauri, sannan ya kulle kofar kitchen din, iyakar tsorata ta tsorata a lkcn, ta marairaice masa tayi kasa da murya tace "Don girman Allah kayi hakuri ka sakeni... Wllh yanxu Umma xata fito mu wuce gida kar ta fara nemana, tace min yanxu xa mu tafi" Yace "Toh ta nemeki din mana ina ruwana??" Kasa ce masa komai tayi amma scene din ranan a kitchen din gidansa ne ke dawo mata wanda hakan yayi mugun daga mata hankali, duk a tsorace take, ya daure fuska yace "Saboda nace ki daina gaisheni na lura har wani nishadi kike duk sanda kika gani, kuma confidently kike wucewarki..." Tayi narai narai da ido tace "To amma ai kai kace in daina gaisheka, kuma abinda kace min ai shi nake yi" yace "Amma kuma ai murna kike don baki gaisheni?" Ta kasa ce masa komai gabanta na mugun faduwa, sai kuma ta fara kauda fuskarta saboda saukan breathing dinsa da take jiyowa don dab da ita yake, yace "Ohk ni kike dauke ma fuska?" Ta fashe da kuka tace "Ni don girman Allah ka sakeni ana jirana, don Allah fa nace maka...." Tana ganin xai juyo da fuskarta saitin nasa ta rufe fuskar nata a jikinsa hankali tashe tace "Don Allah kayi hakuri bana so wllh" wrapping dinta yyi jikinsa yace "Xan sake ki amma sai kin bani amsar tambayar da xan maki yanxu" Banda bugawa babu abinda xuciyarta ke yi tana jiran jin tambayar tasa, ga kamshinsa me dadi da ya cika hancinta, duk taji ta kasa ci gaba da tsayuwa, xata xame kasa yace "Kee" a hankali tace "Na gaji don Allah ka bar ni in tsugunna" da bango ya hadata ta rufe idonta da sauri, sai kallon fuskarta yake a duhun, taji yace "Duk xaman da muka yi dake a gida daya ki lissafo min abubuwan da na maki na rashin adalci..." A hankali ta bude ido tana kallonsa, yace "Ina sauraronki" Ta girgixa kai tace "Aa babu" ya dafa shoulders dinta yace "Karya kike" Tace "Ba karya nake ba, ban tuna abinda ka min na rashin adalci ba" Yace "To ina son ki tuna sai ki gaya min" Tayi shiru, shi dai kallonta kawai yake, murya can kasa tace "Amma me yasa kake ta6ani bayan kasan ni ba muharramarka bace, nasan kuma ka fini sanin hukuncin...." wani xaro ido tayi jin cold lips dinsa a wuyanta, da duk karfinta ta turasa shi kuma ya rungumeta gaba daya, ai kam neck dinta ya sha kisses iri iri ba a cewa komai tun tana iya turasa har ta hakura ta kasa komai, switch din fitila da aka kunna a kitchen ya sa ya saketa da sauri, without looking at her ya bar wajen, xamewa tayi kasa ta hade kanta da gwiwa amma hawayen ma ta nemesa ta rasa sae sauke