← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 205

Sashe 59

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu kowa babban parlon, Ahmad ya xauna saman kujera yana bin parlon da kallo snn ya kalli Abuturrab yace "It looks very good.. " Kitchen Abuturrab ya nufa ya bude fridge ya dau ruwa, fruits din da ya bar mata na cikin fridge har sannan, ya juya ya fita ya dawo parlor ya xauna yana bude ruwan hannunsa, Ahmad yace "Mu yi magana ta fahimta Captain..." Abuturrab ya kallesa bayan ya sha ruwan hannunsa, Ahmad yace "Tell me ur plan on this innocent girl" Abuturrab yace "I have no plan then to make her somebody useful in life, daga nan kuma sai tayi aurenta idan ta samu miji...." Ahmad ya masa wani kallo yace "How Captain? By locking her up for days ita kadai a gida?" Abuturrab yace "I wanted enrolling her in a schl but ni fitan ne gaba daya bana so ma, so it's better i get a lady with better teaching qualification ta dinga koyar da ita a nan gida, i will also get another lady da xasu dinga karatun islamiyya tare duk a gida" Bude baki Ahmad yyi yana kallonsa, can yace "Why? Why dont u want her to go to school and islamiyya with her mates?" Abuturrab ya mike yace "Haka nan kawai, ra'ayina ne" Daga haka ya haura sama, Ahmad ya bi sa da kallon mamaki kafin ya kauda kai, a nan kuma yaji ya fara tantama anya Abuturrab ya saki yarinyar nan ma kuwa, but kuma yasan Captain to be someone that is very straightforward in yayi xai ce yayi, idan kuma bai yi ba xai ce bai yi ba, baya karya. Abuturrab na tafiya sama ya kwankwasa kofar dakin nata kafin ya bude, tana tsaye jikin window ta juyo da sauri, suna hada ido ta sunkuyar da kai, yace "Ki sameni kasa" Daga haka ya juya ya fita, Abaya ne jikinta blue, sosai kayan ya amsheta, a kwanaki kadan din nan da take shafa cream da Abuturrab ya siya mata tana wanka da shower gel ainahin haskenta yake kara fitowa ko ina na jikinta yyi smooth, wanda rashin fita ta shiga rana ya kara contributing da kyan fatar nata, slowly ta nufi kofa kana ganinta kasan she isn't happy, yau gaba daya ta tashi da kewan yan gidansu duk da basu ta6a nuna mata so ko na minti daya ba amma har kukan kewansu sai da tayi daxu, Abuturrab na komawa parlor ya xauna, Ahmad dae sai kallonsa yake, bayan some minutes ya mike da sauri tunawa da yyi ba karamin aikinta bane ta sakko ba hijab, ganinta yayi tana saukowa stairs, Ahmad ya juya yana kallonta, Abuturrab ya koma ya xauna, ta karaso cikin parlon ganin Ahmad ta sunkuyar da kanta ta rakube kasa jikin kujera cikin sanyin murya tace "Ina yini" Yana kallonta babu ko kiftawa da murmushi fuskarsa yace "Lafiya lau Jiddah ya kike?" Tana wasa da gefen mayafinta, ita ma tana d'an murmushi tace "Lafiya lau" Ta d'an saci kallon Abuturrab dake kallonta suna hada ido ya jefa mata wani kallo ya dauke kansa ita kuma ta sunkuyar da kanta a hankali tace masa "Ina yini?" Bai amsa mata ba, Ahmad dake kallonta yace "Amma kin ci abinci?" Cikin sanyin murya tace "Eh na ci" Abuturrab ya kallesa yace "Is that question necessary??" Bai jira cewar Ahmad ba, ya kalli Jiddah babu yabo bbu fallasa yace "To sai anjima, tashi ki tafi" Mikewa tayi ta wuce sama tana tafiya a hankali, Ahmad ya bi ta da kallo, sosai yaji tausayinta har ransa, he can see she is sad, she looks so unhappy, ya dawo da dubansa kan Abuturrab dake hararansa, Daure fuska shi ma yyi yace "Abuturrab ka taimaki yarinyar nan sbda kaga ana neman cutarta right?ka taimaketa because she is sad, frustrated and almost depressed a gidansu, to ka gaya min bambancin gidansu da wannan gidan ynxu, didn't u notice how sad she looks fisabilillah, how on earth will u lock a being for days ita kadai a gida bata ganin kowa, ai sai wani cutar ya kamata wllh, baka san babu abinda ya kai wannan yanayin da ka barta ciki saurin kashe mutum ba ko, she have nobody to share anything with, just reason it fa, ta yaya xata yi ta rayuwa ita kadai, plss think of a more better solution tunda baka son kaita gidanmu ko gidanku..." Abuturrab yace "Idan ta fara karatu she won't look unhappy anymore" Ahmad bai kuma ce masa komai ba, Abuturrab yace "Ni fa can gidanmu xan wuce yanxu" Tabe baki Ahmad yyi ya mike yace "Dama idan abu ya samu yarinyar nan Aliyu kada ka kirani da sunan kana neman shawara ko wani abu" daga haka ya nufi kofa, Abuturrab ya mike ya bi bayansa. Sai bayan isha Abuturrab ya dawo gida, yana shigowa parlor ya kulle kofar parlon ya wuce sama, part dinsa ya fara wucewa ya ajiye ledan hannunsa, sai da yyi wanka ya canxa xuwa pajamas dinsa, mintuna ba da yawa ba yyi yana waya da Aneesah daga bisanni yace "Xan kira ki anjima" Daga daya bangaren ta marairaice tace "Ni ban yarda da xan kiraki anjiman nan dinka ba, just tell me karfe nawa xan sake kiranka" Yace "Wani d'an aiki nake son yi a system, idan na gama ai nace xan kira" A hankali tace "Toh Allah ya sa, but it's always xan kiraki anjima daga nan kuma shikenan sai gobe" Yace "Uhn xan kira don't worry" Daga haka ya katse wayar, mikewa yyi ya dau ledan abincin ya fita bangarensa, sai da ya fara knocking din sannan ya bude kofar dakin ya shiga, kwance ya ganta ta takure waje daya ta rufe har kanta, ya ajiye ledan hannunsa ya karasa ya bude duvet din, rufe fuskarta tayi da hannunta taki juyowa, tsayawa yayi yana kallonta, can yace "Kee" Still taki juyowa, ya hade rai yace "Baki ji na ne?" A hankali ta dago ta mike xaune amma bata yadda ta kallesa ba, kallon idanuwanta da suka yi ja ya dinga yi, can yace "Kuka kika yi?" Wasu hawayen suka taru idonta, ta ki yarda ta kallesa, yace "Ba magana nake maki ba" Ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, da mamaki yake kallonta, ganin irin kukan da take, ya xauna gefen gadon yana kallonta yace "Gaya min me ya faru" Ta girgixa masa kai kawai tana kukan a hankali, dauke kansa yayi, yayi shiru, bayan wani d'an lkci ya sake kallonta yace "Dago kanki ki kalleni" Taki dagowa, ya mata tsawa yace "Dago kanki nace" Da sauri ta dago hawaye na sauka idonta amma ta kasa kallonsa, ya mike ya koma side din da take kallo suka hada ido, a hankali ta sauke idonta, speaking very calmly yace "Toh gaya min me yafaru, kina son wani abu ne?" Ta girgixa masa kai yace "Kukan me kike yi then?" A hankali tace "Babu komai" Bai kuma ce mata komai ba, can ya kalli ledan da ya ajiye yace tashi kije ki dau abinci ki ci, ganin bata tashi ba ya hade rai yace "Tashi nace" Mikewa tayi ta nufi gun ledan ya bi ta da ido, yau ma riga da wandon ne na bacci jikinta, tana isa gun ledan yace sa darduma ki xauna a nan ki ci, ta tafi gun darduman ta dauka sannan ta dawo ta shimfida ta xauna a kai, daurewa kawai take amma ji take kamar ta fashe da kuka, ta bude ledan taga tuwo ne da miyar kubewa irin na ranan, sauke idonta tayi ta kasa kallonsa, ganin bata da niyyar fara cin abincin yace "Malama abinci nace ki ci" A hankali tace "Xan dauko ruwa" Ya mike ya fita xuwa kitchen ya dauko mata ruwan ya dawo, yana ajiyewa ya koma ya xauna, tashi tayi ta tafi bandaki ta wanke hannunta sannan ta dawo ta fara cin tuwon a nutse, shi dai kallonta kawai yake, he just have a special pity for women, bai son ganin hawayensu even by mistake, it get him weak, and sure yasan maganganun da Ahmad yyi masa daxu babu karya ko daya a ciki but he cannot let her stay with his mum or Ahmad's mum, he will get another solution.... Tana gama cinye tuwon daya xata rufe yace "Daya kika gani a wajen?" Ta girgixa masa kai tace "Baxan iya cinyewa ba" Yace "Kara daya" Bata masa musu ba ta fara cin wani dayan, amma bata iya ta cinye ba kuma bai tilastata ta cinye din ba, ta mike ta dau sauran abincin da ruwa ta fita daga dakin, mikewa yayi ya bi bayanta ya xauna main parlor ya kunna Tv, bayan few seconds ta fito kitchen din xata wuce sama ya nuna mata kujera yace "Dawo ki xauna nan" Tace "Xan wanke baki" yace "Je ki wanke ki dawo" Tafiya tayi saman ya maida dubansa kan tv, tana sakkowa ta tsaya tana kallonsa ya nuna mata kujera yace "Xauna" xaunawa tayi, ya ci gaba da kallonsa, tun tana daurewa sbda baccin da ya fara damun idonta gashi ta kasa gaya masa har daga karshe ta d'an kwanta still pretending to be watching d movie da bata ma san abinda ake a nan ba, da haka bacci ya dauketa, duk yana lura da ita amma bai ce komai ba, he gets she's so lonely, abinda ke damunta kenan, shi kuma he doesn't have intention of spending any of his time together with her, yau ma don kawai kukan da yaga tana yi ne yasa ya kasa jurewa, har karfe sha biyu yana kallo parlon, sai a sannan ya tuna da Aneesah da yace xai kira ya lumshe ido ya jinginar da kansa da kujera, sai kusan karfe daya ya bude idon don bacci daukesa yyi a hakan, kallon 2 sitter din da take kwance yayi yaga baccinta kawai take, mikewa yyi ya kashe switch din wutan parlon gaba daya sannan ya kwanta kan 3 sitter ya kashe tv da remote din kusa da shi ya lumshe ido.... Kiran sallahn farko Abuturrab ya tashi, ya fi minti goma xaune kafin ya duba wayarsa ya kunna fitila yana haskata, mikewa yyi ya karasa inda take kwance ya buga kujeran a hankali, bude ido tayi da sauri yace "Tashi ki wuce
Chapter 59 · 0% Book details