← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 205

Sashe 178

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya shiga dakinsa bayan yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya, kwance ya tadda Aneesah har sannan tana bacci tun bayan da suka dawo wajen karfe shidda da asuba, Karasawa yyi saman gadon ya kai hannu ya buga gefen gadon, ta bude ido a hankali don tun bude kofar parlon da yayi ta farka, yace "Yanxu babu wani abu da xaki girka a kai asibiti??" Buda ido tayi sosai tana kallonsa sai kuma ta mike xaune tana ci gaba da kallonsa keenly tace "Abu kamar me fa Captain?" Yace "Breakfast...." Bude baki tayi sai kuma ta tafe hannu tayi wani dariyar rainin hankali tace "Saboda Aisha ko Ramlah ce kwance gadon asibiti ba lafiya ko??" Kafeta yyi da ido, ta ja wani tsaki tace "Wllh ka xo da wata bidi'a Captain, kawai saboda ga kanwar uwata Safara'u kwance gadon asibiti sai in tashi da sassafe in fara hada breakfast, to bari kaji wllh ko Maimoon ce bata da lafiya sai na ga dama xanyi girki a kai asibiti balle wata banxa can mara asali, gayyar....." Dakatar da ita yayi cikin tsawa yace "Enough Aneesah, baxa kiyi ba baxa kiyi ba, final!! Kar ki gaya min maganan banxa..." Aneesah ta masa wani kallon banxa daga sama har kasa ta sauka kan gadon ta shige bandaki abun ta tana cewa "Ka xata tun farko da nasan ita ce ba lafiya xan ma fara katse bacci na in fita cikin dare..." juyawa yayi ya fita daga dakin xuciyarsa na tafarfasa, yana komawa downstairs ya kira layin Maimoon, tana dauka yace "Anyi breakfast ne a can gidan?" Maimoon tace "Ehh driver muke jira yanxu ya kai mu asibitin" yace "Ohk, i am coming now" daga haka ya katse wayar, yana isa gidan Umma ya dau Maimoon da Safiyya suka wuce asibitin, har sannan Jiddah bata tashi ba, Umma na kallon Abuturrab yace "Ya ku ka koma gida" yace "Lafiya lau" Maimoon na kallon Umma tace "In hada maki shayin Umma?" Umma tace "Aa ai baxan iya sha a nan ba, tun da kun xo bari kawai in koma gida sai in dawo anjima idan na kintsa" Maimoon ta mayar da cup din tace "Toh shkkn" Umma ta mike, Abuturrab ya kalleta yace "Toh bari in ajiye ki gidan Umma" tace "Toh nagode" Tare Umma ta koma da safiyya da tayi shirin Islamiyya, Abuturrab na kallonta yace "A Islamiyyan xa a ajiye ki ke?" Tace "Ehh" sai da ya fara ajiyeta a Islamiyyarsu sannan ya kai Umma gida, bayan ta sauka daga motar ta saka masa albarka ta wuce ciki, barin layin yayi yana hawa saman titi kiran Ahmad ya shigo wayarsa, dauka yayi ya daga ya kai kunne Ahmad yace "Ka koma asibitin ne?" Abuturrab yace "Aa" Ahmad yace "Ohk anjima xan shigo in sha Allah, ka tambayi Umma if there is anything sai kayi masu tunda kaga ba kowa..." Abuturrab dake ta sauraronsa ya tabe baki yace "Umma tace tana yawan ciwon cikin, and what is the cause?" Ahmad yace "Da ka shiga ka tambayi likitan da yayi admitting dinsu mana" Abuturrab yace "Kai na tambaya" Ahmad yace "Ohk tunda ni ka tambaya bari in baka amsa, duk xamanku tare da ita a gidanka ka ta6a ganin tayi Period?" Abuturrab ya juya ido yace "Period? Meye hakan?" Dariya Ahmad yayi yace "Al'ada" Shiru Abuturrab yyi, Ahmad yace "Toh bata al'ada, da Umma ta ga hakan sai ta kai ta asibiti aka daurata kan magunguna, tun sannan kuma shine take ciwon mara..." Abuturrab yace "Toh dole ne sai anyi jinin?" Ahmad yace "Of course dole ne, although wasu matan basa yi kuma suna haihuwa a haka, akwai mata da yawa da xaka ga a shekara sau biyu suke al'ada kuma suna haihuwarsu lafiya lau babu wani abun dake damunsu, so in her case...." Abuturrab ya katse sa yace "What i want to understand here now is, so ake ta fara al'adan yasa aka kai ta asibiti ko me?" Ahmad yace "Eh mana, ana son sanin ko nata normal ne ko kuma Hormonal Imbalance ne ya janyo hakan, idan Hormonal imbalance ne kaga dole sai an ci gaba da yi mata medication har Allah yasa ta fara din, sannan ciwon maran da take ai jini ya kamata tayi ba ciwon mara me tsanani haka ba" Abuturrab ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Allah ya sauwake" Ahmad yace "Ameen..." Abuturrab yace "Sai anjima" daga haka ya katse wayar. Asibitin ya sake komawa, yana shiga ward din Maimoon ta daga kai ta kallesa da mamaki, a ranta kuwa cewa tayi me kuma ya dawo da wannan mutumin nan, tunda Jiddah dake xaune saman gadon ward din hannunta rike da cup din shayi ta hada ido da shi ta sunkuyar da kanta taki dagowa, Maimoon ta mike tana kallonsa tace "Ga kujera yaya" Yace "Nace maki xan xauna?" Ta girgixa kai ta koma ta xauna a ranta tace oho dai, ya kalleta yace "Ke me ya hanaki xuwa islamiyyar?" Ta xaro ido tace "Toh ai yaya saboda xan tsaya da Jiddah a asibiti ne Umma xata koma gida, kaga babu kowa a nan din" Ya d'an kalli Jiddah da taki dago kanta yace "Tace maki bata ji sauki bane?" Maimoon ta kalli Jiddah, ta washe baki tace "Wai kin ji sauki Jiddoh?" Ko kallonta Jiddah bata yi ba, Shi dai kallonta kawai yake, mika ma Maimoon cup din shayin tayi, Maimoon tace "Har yanxu kina jin aman?" Jiddah ta girgixa mata kai kawai, Maimoon tace "Amma ya isheki?" Jiddah ta gyada mata kai, Maimoon ta amsa Abuturrab yace "Mayar mata ta shanye" Maimoon ta d'an kallesa tace "Cika mata cup din fa..." Dakatar da ita yayi yace "I said give it back to her" mika ma Jiddah tayi, Jiddah tace "Ni amai nake ji" Yace "Eh amsa idan kin shanye sai kiyi aman" Karban shayin tayi a hankali a hannun Maimoon, ya ciro ATM card dinsa a wallet dinsa ya mika ma Maimoon yace "Ki ciro min kudi" ta kallesa da sauri tace "A ina yaya? Ai babu Bank a kusa..." Yace "Ko ma ina xaki ciro kije ki ciro ba ruwana" nan da nan mood dinta ya canxa ta amshi Atm card din ta mike tace "Nawa xan ciro?" Yace "Talatin" Kofa ta nufa tana cika tana batsewa, ya bi ta da kallo har ta bude kofar sai kuma ta juyo ganin kallonta yake ta seta fuskarta tace "Yaya pin din fa?" Yace "Ki kira Ramlah ki tambayeta" Ficewa tayi daga ward din ta kulle kofar, ya kalli Jiddah ganin ta ajiye cup din saman gado ta hade kai da gwiwa, karasawa yyi ya dauke cup din shayin ya ajiye a table yana kallonta, ta dago tana rufe idonta yace "Are u still feeling pain?" Da kyar kamar xata yi kuka tace "Yanxu ya fara" Kafin yace komai ta fara kokarin sauka daga saman gadon ya bi ta da ido har ta shiga bandaki, yana ta tsaye har ta fito daga bandakin amma ta ki karasowa cikin ward din, bayan few seconds yace "An kawo maki wani kayan ne?" Kasa kallonsa tayi kuma taki cewa komai, yace "Magana nake maki" bata dago kanta ba tace "Ai ban sani ba" ya nufi jakar da Maimoon ta kawo daxu ya bude, Hijab ya gani da doguwar riga sai undies da sabulu da sponge, satan kallonsa kawai Jiddah take, ya dau sabulun da sponge ya nufeta ya mika mata, amsa tayi ta juya ta koma bandakin, ya karasa saman gadon ya cire bedsheet din ya bar shi saman gadon snn ya fita ward din, nurses dake reception ya samu bayan sun gaisa da wata yace "Plss ki tura cleaner ward din farko, the bedsheet needs to be changed" Tace "Alright" ya juya ya fita xuwa wani babban kanti dake cikin asibitin, babu abinda ba a siyarwa a wajen, yana kallon matar dake ciki yace "Do u sell Sanitary pads?" Matar tace "Yes" guda uku ya siya ya bata kudi sannan ya juya ya koma cikin asibitin, cleaner din ya tarar a ciki tana canxa xanin gado, bayan ta gama ta fita da na da, ya xauna kan kujera, bayan kusan minti sha biyar Jiddah ta fito daga bandakin, pad din da ya ajiye saman table ya nuna mata ta dinga kallon ledan sai kuma ta karasa ta bude tana kallon abun ciki, bata yarda ta kalli inda yake ba ta tafi gun jakan kayanta ta dau pant tana bobboyewa shi dai kallonta kawai yake, ta mike ta dau pad din ta koma bandaki, bayan ta fito ta dau wani Hijab din ta sa, gaba daya ta kasa kallonsa don wani kunyarsa taji take yi, yana kallonta yace "Kina jin ciwon cikin yanxu?" Ta girgixa masa kai ba tare da ta kallesa ba, bai kuma ce mata komai ba ya fiddo wayarsa yana dannawa, ta gaji da tsayuwarta sannan ta koma kan gadon ta kwanta ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa.... Karfe goma Maimoon ta shigo ward din fuskar nan nata babu annuri ta mika masa kudin da Atm card dinsa, yace "A ina kika samo?" Tace "Nima ban san wajen ba" Ta nufi Jiddah tace "Har kinyi wanka?" Ganin bacci take Maimoon ta xauna kawai, Maimoon tace "Lah canxa xanin gadon aka yi?" Abuturrab dai bai ko kalleta ba, Hannu ta kai kan ledan pad dake ajiye tace "Meye wannan kuma?" Xaro ido tayi ganin pads har uku, ta saci kallon Abuturrab sai kuma ta mayar ta ajiye sannan ta xauna kan kujera, mikewa Abuturrab yayi ya nufi kofa ya fita. Yana fita Maimoon ta shiga tada Jiddah a hankali, Jiddah na bude ido tace "Wa aka kawo ma pad Jiddah? Kuma wa ya kawo?" Jiddah ta bi dakin da kallo ganin Aliyu baya nan ta mike xaune, Maimoon dake ta kallonta ta xaro ido tace "Ko dai Period kika fara?" A hankali Jiddah ta gyada mata kai, Maimoon ta kara xaro ido tace "Kar dai Ya Aliyu gani yayi yaje ya siyo maki pad din, gashi ma naga an canxa bedsheet" Jiddah ta d'an turo baki, Maimoon ta kyalkyale da wani dariya tace "Atoh wllh shi yaga duhu, amma ke garin yaya kika bari ya gani? Tabb" Jiddah ta marairaice tace "Na tashi na shiga
Chapter 178 · 0% Book details