← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 205

Sashe 69

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 5 min read

Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you

Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240

Abuturrab ya dau throw pillow dake gefensa ya jefa ma El-Basheer da ya bi Jiddah da ido, sae a sannan El-Basheer ya dauke idonsa, sai kuma ya daga kafada as if counting his words yace "Ita ce.... Ex-wife din taka?" Abuturrab na kallonsa da wani expression yace "Does that warrant u to stare at her that way??" El-Basheer yyi shiru yana danna wayarsa kamar baxai ce masa komai ba, sai kuma ya kallesa yace "Naga kamar ganinta ya fi jin ta ne, ita ce yar hayin rigasar?" Abuturrab ya masa wani kallo ya dau remote yana canxa channel, El-Basheer yace "Ko dai a gidanka ne ta samu transformation din nan, she's got a beautiful shape" Abuturrab ya mike, sounding fed up yace "Stop this plss El-Basheer... U r sounding lousy" El-Basheer yana shafa gashinsa yace "Lousy? Ohk sorry about that" Abuturrab ya dinga kallonsa da wani expression that is expressing how really angry he is, ya koma ya xauna yana canje canjen channel, El-Basheer ya bi parlor din da kallo yace "I need something cold to take now, haka kake treating visitors?" Mikewa Abuturrab yyi ya wuce kitchen, El-Basheer ya bi sa da kallo, fridge ya bude ya dau bottle water daya sannan ya fito, sama ya wuce yana cewa "In dai ni xan kawo maka ruwa xaka dade baka sha ba" El-Basheer ya bi sa da kallo yana d'an murmushi, can ya girgixa kai, bude kofar dakin Jiddah Abuturrab yayi ya shiga.... xaune ya ganta ta takure waje daya, tana ganinsa ta gyara xamanta tayi narai narai da ido tana kallonsa, ya ajiye ruwan gaban mirror ya juyo fuska a tamke yace "Me nace maki daxu?" Shiru tayi, yace "Ba ce maki nayi kar ki fito ba all through?" Hawaye ya cika idonta tace "Ruwa ai naje in dauka, ba ce min kayi in daina shan na bandaki ba" Yace "Me ya hanaki dauka daxu da kika sakko" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Xo ki dauka" mikewa tayi ta tafi gun madubin ta dau goran ruwa, yana kallonta yace "Sannan ba nace kada ki sake sa irin kayan nan a gidan nan ba?" Ta kallesa tace "Ai daxu ka gaya min, ina ce daga yau kace.." Bai kuma cewa komai ba ta koma inda take ta bude ruwan, sai da ta sha ruwan sannan ya juya ya fita dakin, tsaye ya ga El-Basheer a parlor hannunsa rike da kwalin lemon chivita yana sha, Abuturrab ya xauna yace "What will u be taking for lunch?" Xaunawa El-Basheer yayi yace "Naaah... I'm full, i just need rest" Abuturrab yace "Okay mu je sama" Mikewa yayi ya fara tafiya sama, El-Basheer ya mike ya bi bayansa rike da lemonsa, Abuturrab ya kai sa part dinsa, xaunawa El-Basheer yayi gefen gado cikin bedroom din bayan ya rufe lemon hannunsa ya ajiye yace "Tsarin gidan yayi sosai, the Architecture is really good" yana fadin haka ya kwanta, Abuturrab dai na tsaye gaban madubi yana kallonsa ta madubin, can dai yace "Xan je in dawo yanxu!!!" El-Basheer ya dago yace "Ina xa ka?" Yace "To get lunch" daga haka ya nufi kofa ya fita, yana isa kofar Jiddah ya bude, ya d'an hade rai yace "Dauko Jilbab dinki, ki sameni waje" Daga haka ya wuce, yana cikin mota Jiddah ta fito da Hijab har kasa, sai da ta shiga gaban motar sannan yayi horn, mai gadi ya hau bude gate din, jan motar yayi suka fita gidan, wani babban eatry ya tafi, ya siya ma shi da El-Basheer fried rice and chicken, Jiddah dae na xaune kan kujeran da ya nuna mata cikin eatry din, sai bin mutanen wajen take da kallo, baka ta6a cewa tare suke da Abuturrab don bai ko sake kallon inda take ba, wani mutumi ne ta ga ya ja daya daga kujeran table din da take ya xauna, ya daga face cap dinsa yana kallonta, ta saci kallon Abuturrab da ke xaune wani table can yana jiran order din da yayi, ta sake kallon mutumin, ya sakar mata murmushinsa me kyau, ta sunkuyar da kanta da sauri, yace "Hello, how are u doing, are u waiting for ur order?" Ta saci kallon Abuturrab taga kallon direction dinsu yake ko kiftawa babu, sosai gabanta ya fadi, cikin rawan murya tace "Yayana na nan fa" Mutumin ya bi eatry din da kallo, kawai gani yayi Abuturrab ya nufosu, ita dai gabanta sai faduwa yake, Abuturrab na isowa yana kallon mutumin babu yabo babu fallasa yace "Didn't she tell u she is married?" Mutumin ya mike yace "Ooh i am sorry plss" Abuturrab bai tankasa ba ya ja wani kujeran ya xauna facing her directly, mutumin ya kara basa hakuri, nan ma yaki amsawa har mutumin ya bar wajen, Jiddah ta saci kallonsa suka hada ido, ya jefa mata wani kallo yace "Ko tausayin rayuwarki baki ji har xaki fara kula maxa ko?" A hankali tace "Ni bani na kirasa ba kawai xuwa yayi" Yace "Toh bari kiji har sai kin gama jami'a kin fara aiki, kafin ki kalli ko wani namiji balle har ki kulasa" Ta gyada masa kai kawai, ya ci gaba da danna wayarsa har aka kawo masa order da yyi a takeaway, without looking at her yace "Me xa ki ci?" ta sunkuyar da kanta tace "Ko meye" tsaki yyi ya mike ya bar wajen, jollof rice yayi mata order da kazar ita ma sannan suka bar eatry din, tana rike da ledan nata ta wuce dakinta bayan sun isa gida, Abuturrab na shiga bedroom dinsa ya tadda El-Basheer a kwance yanda ya bar sa idonsa lumshe, parlonsa ya koma ya xauna.
Chapter 69 · 0% Book details