← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 205

Sashe 135

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Halan dai saurayinta ne?" Maimoon tayi dariya tace "Ehh" Hajja tace "Atoh shi kuma baya gaida mutane ne, ai da sai ya shigo ya gaishemu yayi mana Allah ya sanya alkhairi haka ake yi" Jiddah ta ci gaba da linkinta, Hajja ta gama xuba abincin ta mike tace "Toh a kai masu can dakin, idan ba ni ba babu wanda xai masu haka, kowa na ta kansa a gidan" Maimoon ta mike ba tare da ta tsaya gyara plates din abincin kai ba ta dau tray din sai ga plate daya ya rikito kasa, Hajja ta amshe tray din da sauri tace "Je ki Allah ya isa" Wani kallo Maimoon tayi mata tace "Toh na sani ne?" Hajja tace "Nace maki wani abu ne, cewa nayi kije ke da Allah kawai" Maimoon ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, Hajja tace "Algunguma kawai, wllh da gangan ta kifar, dama bata yi niyyar xuwa ba, yar mummuna da ita kawai, uban me na hada da ita banda dai uwarta kanwar matar d'a na ne, gayyar tsiya kawai, da a Masar ne dama babu wani dangantaka tsakanina da ita nan ne dai komai sai anyi karere" Ita dai Jiddah linkinta kawai take, Hajja ta sake xuba wani shinkafar tana ta mita, har ta gama sannan ta kalli Jiddah tace "Ki dauka ke ki kai masu, nima na so raina ya baci ne, banda haka ga ki, er arxiki irin albarka" Jiddah ta ajiye xanin hannunta ta karasa ta durkusa a hankali ta dau tray din ta nufi kofa, sai a sannan ta juya tace "A ina xan kai masu?" Hajja tace "Suna can parlon Usman" Jiddah ta fita dakin ta kama hanyar parlon Abba, sai da ta fara ajiye tray din ta murda kofar a hankali hade da sallama sannan ta dau tray din ta shiga ciki, waya na kare kunnen Abuturrab yana magana, El-Basheer kuma na xaune saman kujera idonsa a kan phone dinsa, karasawa ciki tayi ta ajiye tray din tana kallonsu tace "Ina yini" El-Basheer na kallonta da murmushi yace "How are u?" Tace "Lafiya lau" Daga haka ta mike ta nufi kofa El-Basheer yace "Who were u speaking with outside Jiddah" ta juyo tace "Yaya Yousuf ne" El-Basheer yace "Who is he?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Family frnd din su Yaya Ahmad" El-Basheer bai kuma cewa komai ba, ta d'an kalli Abuturrab taga yanda ya sha kunu, juyawa tayi ta fice daga parlon. Bayan la'asar aka fara shirye shiryen kai amarya, gidan cike yake dam da jama'a yan kai amarya, motoci sun fi ashirin a compound da kofar gida duk na yan kai amarya, wajen Hajja aka fara kai Aneesah dake sanye da alkyabba fuskarta a rufe, aka xaunar da ita saman carpet Hajja na daga xaune kan tabarma ta daura kafa daya kan daya, tana kallon Aneesah tace "Ni dai bani da abinda xance, amma da a Masar ne kawai ce maki xa ayi ki bi yan uwansa da iyayensa sau da kafa, to sai ki ji dadin xama da shi, duk abinda yake so shine abun sonki.... Kinga dai shi me yan uwane barkatai kuma duk baxa su ki xuwa gidansa ba don haka kika iya allonki ki wanke, ko ni nan duk sanda na ga dama xanje gidansa tunda ni na haifi ubansa kuma a hannuna ya taso daga bisanni ya fita waje koyon tukin jirgin sama..." Aunty dake tsaye daga bakin kofa sai hararan Hajja take kamar ta kifa mata Mari, Aneesah dai sai satan mutanen dake dakin take da kallo duk da fuskarta a rufe yake, Jiddah ta gani xaune gefen gado rike da jakar da Hajja ta bata, ganin kallonta Jiddah ke ta yi ta wani tsuke fuska kamar tana ganinta, ita dai har ranta taji ta tsani jiddah, bata ta6a jin tsanar mutum yanda take ma Jiddah ba, she just hate her with passion, Hajja ta gama surutanta mara tushe aka daga Aneesah dake ta kallon Jiddah har lkcn, aka fitar da ita daga dakin, next aka kai ta gun Ummi, Ummi ma tayi mata duk nasihar da ya kamata, Umma ta daura da nata, daga karshe aka kai ta gun Abba da Uncles din Abuturrab, sai wajen hudu da rabi aka kai amarya mota, Hajja ta saka ma kofarta makulli ta mika ma Jiddah tace "Jefa min a jaka sai Allah ya mana dawowa kuma, mu xa mu kai ta" Saurayin Safiyya ne ya tafi da su Maimoon da Jiddah da safiyyar sai Nafisah gidan Abuturrab, tun da yayi parking out side gate Jiddah ke kallon gidan, kamar bata ra6a rayuwa a gidan nan ba, kofar gidan cike yake da motocin kawo amarya, Maimoon da su Jiddah suka samu suka shiga compound din, Jiddah dai na biye da su a baya har suka shiga parlon, taji gabanta ya fadi, komai na parlon an sauyasa xuwa sabo, jama'a ne cike parlon ana ta gud'a, Maimoon ta ja su Jiddah suka wuce sama, dakin da Jiddah ta xauna ta bude taga few mutane a ciki, kayan dakin ma duk an canza suka fito suka bude sauran dakunan da duk aka xuba ma furnitures, duk da Abuturrab ya sanar ma Aneesah ta gaya ma iyayenta ba a bangarensa xa a xuba mata furnitures din daki ba, taki sanar masu, can kuma suka kai kayan dakinta, Jiddah dai sai kallon parlon Abuturrab take, har sannan hotonsa na kayan pilot na parlon, ta rasa me yasa memory ke ta dawo mata, ba karamin kudi iyayen Aneesah suka kashe mata na kayan daki ba, don duk dakuna hudun dake gidan sun xuba kaya, can karshen gado ta xauna fuskarta a lullube Jiddah dai kallo daya tayi mata ta fita daga dakin ta bar su Maimoon a can ta koma downstairs ta xauna a parlor tana bin ko ina da kallo. Sai kusan karfe shidda aka fara watsewa daga gidan amarya shi ma Hajja ce ta fara sallaman mutane su tafi kada a 6ata ma yarinya gida, gidan ya rage daga Umma, Aunty, Aunty Nafisah da frnds din Ummi, sai wasu family, Jiddah dai sai jiran lkcn da Hajja xata tafi ta bi ta take don taga alamar su Maimoon basu da niyyar tafiya don har Saurayin Safiyya ya wuce, tana ta xaune parlor har magrib hakan yasa ta mike ta shiga bandakin dake parlor tayi alwala ta fito tayi sallah, bayan ta idar ta tafi sama ta bude dakin da take tunanin su Maimoon ke ciki xaune ta gansu suna ta hira, Tace "Wai baxa mu tafi gida bane?" Nafisah tace "Aa mu dai kila ma a nan xa mu kwana" Xaro ido Jiddah tayi, can tace "Toh ga jakar Hajja ni xan tafi" Maimoon tace "Toh wa xai maida ki gidan?" Jiddah tace "Akwai dari biyar din Umma a jakana xan yi amfani da shi" daga haka ta fita, xata sauko downstairs suka kusa cin karo da Aunty sake haurowa sama rike da abinci, sosai gabanta ya fadi ta koma gefe da sauri, Aunty ta kalli downstairs taga babu kowa parlon, fuska murtuke tace "Uban me kika taho yi gidan nan ke kuma?" Jiddah dai ta kasa cewa komai gabanta na faduwa, Aunty tace "To don ubanki sauka ki kama hanyar ki, ke a wa xaki biyo yan kawo amarya, munafuka kawai mayya, nace ke a wa??" Jiddah ta fara sauka a sanyaye, hankadeta Aunty tayi har sai da ta kusa faduwa, cike da tsanarta tace "Maxa fita, ke da gidan nan ai sai dai hange daga nesa" Jiddah bata ce komai ba ta sauka da sauri ta nufi kofa ta fita compound din gaba daya, duk jikinta yayi sanyi, slowly take tafiya a dogon layin wanda ko wani gida da fitilu farare da ya haska layin kamar rana, mota ne ya dallareta ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da tafiya a hankali, reverse taga motar na yi yana komawa baya, ta kalli motar don bata ta6a ganin irinsa ba, lkci daya aka sauke glass din motar, ta dinga kallonsa, murmushi ya sakar mata yace "Hi...." Ta fara wasa da hijab din jikinta ta sake satan kallonsa, bude motar taga yyi ya sauka ya xagayo ta inda take yace "Assalamu alaikum" amsawa tayi a hankali, yace "Sorry na tsayar dake a layi ko?" Tace "Um" yace "Kin ganeni kuwa" ta sake kallonsa, d'an murmushi kawai tayi bata ce komai ba, Yace "Ina xa ki da daddaren nan?" Tace "Gida" da mamaki yace "Ba can bane gidan ku dama" ta kalli gidan Abuturrab da yake nuna mata, sai kuma ta girgixa kai tace "Aa, gidan yayanmu ne" Ya wara manyan idanuwansa yace "Ohh, shi yasa na daina ganinki kenan" murmushi tayi masa nan ma, yace "Toh mu je in ajiye ki gidan naku ynxu" Tace "Aa ai ban sanka ba" Yace "Really? Duk sanin da kika min a balcony?" Murmushi tayi tana kallonsa, ya bude mata front seat yana kallonta, sauke idonta tayi ta shiga motar ya kulle sannan ya xaga ya shiga driver seat, reverse yayi suka bar layin yace "Ya sunanki?" A hankali tace "Jiddah" As if counting his words yace "Jeedderh!!" Ta kallesa ya sakar mata murmushi wanda har sai da dimple dinsa ya lotsa ya kai fuskarsa dab da ita yace "I am Ali"
Chapter 135 · 0% Book details