← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 205

Sashe 66

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bude ido Abuturrab yyi ya tashi xaune yana kallonta da mamaki, ta mike tsaye hannunta a goshinta, ko ina na jikinta rawa yake, duk ta daburce, xata bude kofar cikin tsawa yace "Me ya kawo ki nan??" Kin juyowa tayi hannunta na rawa ta bude kofar xata fita, wani tsawan ya kuma yi mata yace "Kar ki kuskura ki tsallaka bakin kofar nan" fashewa tayi da kuka amma taki juyowa kuma bata fita dakin ba, ya sauka daga saman gadon ya dau jallabiyansa ya saka sannnan ya nufeta, tana jin alamar ya sauka gadon ta juyo da sauri, ganinsa tayi tsaye gabanta, fuska daure yace "Me ya kawo ki bangarena?" Cikin rawan murya ta durkusa tace "Wllh kara naji shine na xo in ga meye, ban san ka dawo ba Allah" Ya rungume hannunsa yace "Wato har nan kike shigowa kenan idan bana nan kenan?" Ta fashe da matsanancin kuka tana girgixa kai tace "Aa bana shigowa, ni ba shigowa nake ba wllh" Yace "Toh ina ruwanki da koma me kika ji da xaki shigo min daki?" Hawayen dake makale idonta ya sakko ta girgixa masa kai kawai bata ce komai ba, yace "Toh tafi ki dauko abun shara, ki share tun daga cikin dakin har parlor sannan ki goge, ki wanke bandakin...." Ta sunkuyar da kanta don har ta ji hankalinta ya kwanta xatonta har marinta sai yyi yau, kofar balcony din dakin ya nufa ya bude yana nuna mata yace "Har nan xaki share kiyi mopping" Gyada masa kai kawai tayi, ya dau wayarsa har ya nufi kofa ya tsaya, ya juyo yana kallonta yace "Kar ki ga na kyaleki yau, billah idan kika sake shigo min bangarena ko da wasa xaki sha mamaki" Kai kawai ta gyada masa a sanyaye, ya juya ya fita, sai da ya fita parlon gaba daya sannan ta juya a hankali ta fita ita ma, downstairs ta sauka ta gansa xaune parlor ya kunna TV, ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, abun sharan ta dauko da mopping bucket tare da mop with duster sannan ta wuce sama, aikin ta shiga yi babu ganda, har xanin gadon sai da ta sake shimfidawa, bayan ta gama da bedroom din ta tafi balcony, kallon inda taga mutumin ranan tayi duk da babu kowa wajen sai kujera amma sai take ganin kamar shi a wajen, ta fi minti biyu tsaye tana ta kallon wajen kafin ta fara share balcony din ta yi mopping ta dawo dakin ta kulle kofa, parlor ta tafi nan ma ta share ko ina ta goge har kayan kallon, tana gamawa ta koma bedroom din ta bude kofar da take tunani bandaki ne, kallon bracelet din hannunta me kyau tayi wanda yau ya kai kwana uku da ta saka shi, ta tafi gaban mirror dinsa ta cire sannan ta ajiye tana kallon turarrukan da ke gaban madubin, kwalabensu ne ya burgeta sosai, they look so unique, ta dau daya daga ciki ta bude ta kai hanci, rufe ido tayi sannan ta bude, da wannan kamshin ta sansa, babu kuma abinda ya fado mata sai lkcn da yake xuwa can wajenta a Hayin rigasa, ta dau murfin xata rufe turaren ya subuce daga hannunta duk kokarin ganin ta kama turaren kan ya kai kasa hakan ya faskara don tuni yayi landing kan tiles sbda irin faduwan da yayi kuma lkci daya ya tarwatse, a tsorace ta ja baya ta dafe kirjinta da ya hau bugawa, lkci daya ta fara yarfe hannu murya can kasa tace "Na shiga uku" hankali tashe take kallon turaren, ta ma rasa abun yi, can ta nufi kofa sai a sannan ta fashe da kuka ta fita part din, downstairs ta sauka ta makale jikin bango tana kallonsa gabanta na faduwa, jin footstep kuma bai ji ta karaso cikin parlon ba ya sa ya juya, sunkuyar da kanta tayi, ya mike yana kallonta ganin hawaye a idonta, satan kallonsa tayi ganin kallon da yake mata ta fashe masa da kuka tace "Don Allah kayi hakuri" kasa daina kallonta yyi, can yace "Me kika min a sama?" Ta kara rushe masa da kuka tace "Don Allah kayi hakuri nace" Ya wani hade rai yace "Me kika yi nace?" Kin cewa komai tayi, ya nufeta, da gudu ta bar wajen ta wuce sama, ya bi bayanta, tuni ta shige dakinta ta rufe kofan da karfi, part dinsa ya nufa tun bai shiga parlon ba ya soma jin kamshin turarensa, ya shiga parlon sannan ya bude kofar dakin, tsaye yayi bakin kofa ya rungume hannunsa yana kallon tsadadden turaren nasa a kasa, Jiddah dai sai zare ido take tana jiran jin ya shigo dakin amma bai shigo ba har sha daya na safe, sai a sannan ta fara jin yunwan da ya dameta, lamo tayi kan gado kamar xata yi kuka tana tsoron fita, tana nan a haka har kusan sha biyu, mikewa tayi daga karshe ta nufi kofarta ta bude a hankali, cikin sanda ta sauka downstairs bayan ta tabbatar baya kasa sannan ta wuce kitchen, indomie ta dauka ta fara dafawa a kitchen din, ko kadan bata yrda tayi making noise da xai sa a san tana kitchen din ba, yanda taga Ramlah ta dafa masu indomie jiya take yi, with ingredients, tana duba indomie da har ya dahu kamar ance ta juya ta gansa tsaye bakin kofa, sake murfin tukunyar tayi a rikice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" end din kitchen din ta tafi ta tsaya tana kallonsa a tsorace kamar xata yi kuka, ya karasa gun gas din ya kashe na indomien, da kuma na kwai dake tafasa, tana ganin haka xata fita kitchen din da gudu, ya tare hanyar, hade hannunta tayi waje daya ta marairaice tace "Don Allah kayi hakuri" yana mata wani kallo yace "Laifi nawa kenan kika yi yau a gidan nan?" Ta hadiye abu da kyar tace "Biyu" yace "Wanne da wanne?" Tayi narai narai da ido ta ki cewa komai, ya hade rai yace "Ina jin ki" Cikin rawar murya tace "Na fasa maka turare" yace "Ehen, sai me?" Tace "Na ji kamar radio na magana shine naje sashinka ka kamani" Ya gyada kai yace "Good, kinsan nawa turaren nan da kika fasa min?" Ta bude ido tana kallonsa amma bata ce komai ba, yace "Toh ki sani cewar tara ki nake, turaren nan kuma sai kin biyani duk yanda za ki yi ba ruwana" a hankali tace "Toh ae ni bani da kudi" yace "Ehh nemosu xa kiyi duk inda xa ki nemo su" ta sauke idonta kasa, kallonta yake daga sama har kasa, ya sauke idonsa kan fingers dinta yaga babu farce alamar tana cirewa a kai kai, ya kalli fararen toes dinta, kallon fuskarta yyi yaga har sannan kasa take kallo, yace "Cire hular ki" sae a sannan ta daga kai ta kallesa amma taki cirewa, ya hade rai yace "Magana nake maki" a hankali ta xame hular, ya dinga kallon bakin gashin nata wanda sak na Fulani, amma duk ya takure waje daya duk da da ribbon ta dauresa a tsakiya ya sauka kasan wuyarta, tun gyaran gashin da Umma tayi mata har ranan bata ta6a gashin ba, ya yamutsa fuska yace "Meye wannan din?" Ta kallesa bata ce komai ba, ya mata tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba" Cikin sanyin murya tace "Gashina ne" Yace "Ke kaxamar wace gari ce, gashin ki ne kika bari haka kamar na mahaukaciya?" Ita dai bata ce komai ba, ya koma baya yana sake kare ma gashin kallo da mamaki, satan kallonsa tayi ya mata wani shegen kallo yace "Sae na tsokale idonki kika sake kallona, kina mace da ke dubi ynda gashin ki ya koma kamar gashin jikin tinkiya?? What nonsense" Lkci daya hawaye ya kawo idonta, strictly yace "Ki gama cin abincin kiyi sllh ki jirani a parlor" Bata ce komai ba ya juya ya fice daga kitchen din, Jiddah bata wani ci abincin ba sae hawaye, daga karshe ta mayar kitchen ta rufe taje sama ta wanke bakinta ta dau gogaggen hijab dinta ta saka ta dawo parlor ta xauna fuskarta babu walwala, sae da ya dawo sallahn Juma'ah sannan ya dau makullin motarsa, ya isa bakin kofar fita sannan ya kalleta yace "In xo in dauko ki ne" mikewa tayi a sanyaye ta bi bayansa, gaban motar ta xauna don bata mance abinda yace mata ba last time da ta xauna a baya, wani saloon ya kai ta, yana xaune mota ya jira har aka gama sannan daya daga workers din ta fito ta sanar masa an gama ko xa ayi mata lalle, yace "Aa, nawa ne kudin gyaran gashin naku?" Ta fada masa ya ciro kudin ya mika mata tayi masa godiya ta koma ciki, ba a dau lkci ba sai ga Jiddah ta fito daga saloon din, walking slowly ta iso gun motar har sannan fuskarta babu walwala, ta bude gaban motar ta shiga, ta rufe bata ce komai ba, kallonta kawai yake da mamaki, gani yake kamar da kyar ta iya rabuwa da halin gidadanci, ya daga kafada don yasan yana magana xata fara hawaye abinda bai shirya gani ba kenan, ya tada motarsa ya bar saloon din, suna tsaye traffic ganin yanda take kallon me tallan Apple a bakin glass din motar yace "Xa ki ci ne?" Sauke idonta tayi bata ce komai, yace "Ba magana nake maki ba?" Ta girgixa masa kai fuskarta a tamke tace "Baxan ci ba" hade rai yyi yace "Keee" Juyawa tayi ta kallesa tace "Nace A'a" Wani mugun kallo ya dinga mata ta dauke kanta, har suka isa gida bata sake kallon inda yake ba, yana gama parking ta sauka amma tana tsoron ta fara tafiya yyi mata masifa, Matar Mai gadi ce tsakar gidan daga kofarsu ganin Jiddah tace "Sannunku da dawowa Hajiya, Ina wuni...., duk yau shiru baki fito ba" gaban jiddah ya fadi sosai, Abuturrab ya dinga kallonta, Jiddah ta yi murmushin karfin hali tana kallon matar tace "Ina yini" daga haka ta fara tafiya da sauri, bin bayanta Abuturrab yyi, sai da ya shiga parlor ganin har ta isa stairs xata wuce sama yace "Dawo nan" juyowa tayi sannan ta dawo gabanta na faduwa, yace "Ta ina kike fita
Chapter 66 · 0% Book details