← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 205

Sashe 198

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 6 min read

yake ke ai sai da izini, mu din dai" Daga haka ta fice, Jiddah ta bi ta da kallo. Bayan sati daya Jiddah suka gama exams suka yi hutu ta dawo gidan Umma yin hutu... Ranan friday ita da Maimoon da Safiyya suka shirya xa su gaida Ummi, Da yake driver baya nan, Umma ta basu kudin adaidaita tana sake jaddada masu kar su kwana saboda Islamiyya gobe, Maimoon tace "Haba Umma karfe biyar na yi xa mu juyo, har sun nufi kofa Maimoon ta kalli Jiddah tace "Anya baxa ki sa Hijab ba Jiddah?" Safiyya tace "Saboda me?" Maimoon tace "A'a ba saboda komai ba, gani nayi ya fi mutunci" Daga sama har kasa Safiyya ta kalleta tace "Shi yasa naga kin sa Hijab din ke ai" Jiddah tayi ficewarta bata sake sauraron Maimoon ba, Safiyya tace "Duk wani harka na iyayi kin fi kowa iyawa" Maimoon tace "Aa daga magana sai cibi ya xama Kari, ni dai ba kawai suggestion na kawo ba" Safiyya tace "Why didn't u suggest that for ur self??" Maimoon tayi ficewarta tayi banxa da ita. Suna isa gidan direct bangaren Ummi suka wuce, Aneesah na xaune parlon da kanwar mamarta Safara'u da ta tare a gidanta tun bayan da Aliyu ya bar kasar, Ummi ma na parlon alamar dai su ma xuwansu kenan, Maimoon na ganin Aneesah ta hade rai tana kallon Ummi tace "Ummi ina yini?" Ummi tace "Lafiya lau Maimuna, daga gida ku ke haka?" Maimoon tace "Ehh wllh Ummi, Hajja na nan?" Ummi tace "Hajja ai tana Bauchi" Maimoon tace "Ohk" daga haka ta wuce dakin Ummi, Aneesah ta bi ta da kallo, Jiddah ma ta durkusa ta gaida Ummi, Ummi ta amsa da fara'a, wani kallo Aneesah ta dinga yi ma Jiddah kamar ta ga kashi, Jiddah ta kasa kin gaida Safara'u ganin babba ce, Aneesah na jin ta gaida Safara'u tayi ma Safara'un alamar kar ta amsa ta hanyar ta6a ta da sauri, ai ko Safara'u taki amsawa, Safiyya ta gaida Ummi sannan ta gaida Aneesah da Safara'u ta mike ta wuce dakin Ummi, Ummi na kallon jiddah tace "Tashi ki bi su ko" Mikewa jiddah tayi ta bi bayansu, Aneesah dai sai kallonta ta gefen ido take, ta rasa dalilin da yasa da taga Jiddah sai hankalinta ya d'an tashi, Safiya ce tsaye tana kallon Maimoon tace "Me yasa baki gaida Aunty Aneesah ba?" Maimoon da ke kwance kan gadon Ummi ta mike tace "Wacece kuma Anty Aneesah? Me na hada da ita da xan gaisheta?" Safiyya tace "Matar Yaya Aliyun??" Maimoon tayi wani dariya tace "Ta jira dai taga matar tasa ta ainahi... Wannan matar me yi ma mutane kallon rainin hankali da walakanci ne xan gaishe da, ji fa ranan da muka je gidanta abinda ta mana har xaki ce in gaisheta, a da nayi vow har in mutu baxan sake komawa gidan yaya Aliyu ba, amma dai nayi istigifari kwanan nan don can ne ma dabar mu idan Allah ya so nan ba da dadewa ba, sai ta raina kanta wllh, don ni tattara kayana ma xanyi in koma gidan sai dai in Umma ce ta hanani ko shi ya korani" Daga Safiyya har Jiddah dai kallonta kawai suke, ta murguda baki ta mike ta fice daga dakin yanda xata sake bin gaban Aneesah ba tare da ta gaisheta ba, ai ko Aneesah ta bi ta da kallo kasa kasa xuciyarta na tafarfasa har ta fita parlon. Kamar yanda suka sanar ma Umma karfe biyar suka fara shirin komawa gida, Ummi ta basu kudin mota sannan tace "Amma fa ku shiga ku sallami Aunty duk da bata dade da dawowa ba" Sallama suka mata suka fita, Jiddah tayi pretend kamar xata je ta sha ruwa, Maimoon da Safiyya suka shiga part din Aunty, Tana xaune parlonta da Aneesah da Safara'u, suna gaisheta ta mike rai bace tace "Wato ke Maimoon don baki da kunya baki gaji kunya ba ita Aneesar xa ki gani ki ki gaisarwa ki wuce don Ubanki??" Maimoon ta tsaya tana mata kallon tara saura amma taki cewa komai, Aunty na tafe hannu tace "Maxa fitar min daga parlor kada in rotsa maki kai, shegiya fitsararriya kawai" Aneesah tace "Ae kawai da kin kyaleni da ita Aunty, ita karamar alhaki ma?? Wllh so nayi watarana Allah ya kawota gidana in mata koran kare, uwar me gaisuwarta xai kare ni da shi dama?" Maimoon tayi wani dariya tace "A gidan yayan nawa xa ki yi min koran kare??" Aneesah ta mike tana huci tace "Kya dai je ki nemi yayanki amma ba Aliyu ba, idan kuma da akwai abinda ya fi koran kare wllh sai na aiwatar gareki in har rashin hankalinki ya ja ki xuwa gidana, don wannan gidan a yanxu ko shi Aliyun ba shi da wani say a kansa, yau da Ramlah ko Nafisah ko Aisha ce suka ki gaisheni shine xan ji takaici amma banda ke karere gayyar tsiya" Maimoon tayi wani shewa tace "To mu xuba dake shege ka fasa, kuma wannan gidan da kike takama da shi sai ya gagareki xama kwanan nan ba da wani dadewa ba wllh, abota xa ki kulla da sleepless night very soon..." Da gudu Maimoon ta fice daga parlon tana murguda baki ganin Aunty ta yo kanta tana kunduma mata wasu axababben xagi kamar bamagujiya, ita dai Safiyya na tsaye kamar shashasha, Safara'u kuwa sai dannan xuciyarta take tunda Aunty da Aneesah nayi ita bai kamata ta sa baki ba, Aunty tayi mata tsawa tace "Fita kema, gantalallu gayyar tsiya kawai...." Safiyya bata ce komai ba ta fita daga parlon, tuni Maimoon ta ja Jiddah suka fice daga gidan ranta fess ta fesa masu rashin kunya iya rashin kunya, sai da suka nufi titi Safiyya ke cewa "Wllh baki ji Maimoon, baki jin magana, Umma ta hanaki wannan halin kin ki, idan ma sun xageki meye na biyesu bayan kin san ba sa'anninki bane su??" Maimoon tana tafe hannu tace "Ba ruwana da tsufansu, ai ance respect begets respect, Respect should only be given to he who deserves ita, wato dai he who respect his or her self, basu yi respecting din kansu ba balle inyi respecting dinsu, haka kawai a xagi ubana dake kabari a kan wata banxa jaka can kaxama da ita kike expecting inyi shiru kamar ban san ciwon kai na ba?? To wllh ban rama yanda nake so ba ma, sai ranan da muka fara bata sleepless night a gidanta sannan xata gane ni ba kanwar lasa bace..." Wani shewa Maimoon tayi cike da farin ciki, Safiyya tace "Ke da wa xaki bata sleepless night din" Maimoon ta bude hannu tace "Ohoo a xuba ido a gani, shi sa Jiddah asirinta a rufe taki shiga nima da na sani wllh kawai ce ma Ummi xanyi to amma inyi wucewata, uwata ce ita da dole sai na gaisheta??" Safiyya tace "Ni dai ba ruwana ki daina wnn halin da kike...." Maimoon tayi gaba ta ki sauraran Safiyya kuma, Jiddah dai tafiyarta kawai take bata ce masu komai ba, a ranta kuwa taji dadin dubaran da tayi na shigewa kitchen da yau har da ita xa a hada a xage ubanta dake kabari. Bayan kwana biyu Jiddah na xaune kan darduma ta idar da isha Maimoon ta shigo rike da wayarta dake kare kunnenta, ta nufeta ta mika mata wayar tace "Kema ku gaisa, Safiyya ma sun gaisa, har da Umma ma sun gaisa" Jiddah na kallonta ta amshi wayar, screen din ta fara kalla ta ga "Yaya A" ta kai wayar kunne tayi shiru, Maimoon tace "Toh kiyi magana mana ai bai katse ba fa" daga daya bangaren taji yace "Shiru kika yi?" Lokaci daya ta dau muryarsa wanda hakan ya ja mata faduwar gaba, ta d'an hade rai a hnkli tace "Ina yini" Yace "How are you?" Tace "Lafiya" juyawa Maimoon tayi ta lallaba ta fita dakin....
Chapter 198 · 0% Book details