Sashe 175
Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 1 min read
numfashi take... Tunda makullin motarsa na jikinsa gate kawai ya nufa ya fice ya shiga motarsa ya wuce gida, ko kallon Aneesah dake xaune parlor duk ta cika turaren wuta bai yi ba ya haura sama yaki xuwa bangarensa ya bude wani daki ya shiga ya kulle kofar da key ya wuce bandaki direct.... Maimoon ta mike xaune ta kunna switch din dakin dake gefenta tana kallon Jiddah cikin muryan bacci tace "What happened Jiddah?" Ganin Jiddah taki bata amsa kuma taki dagowa ta sauka kan gadon ta nufi kofa ta fita xuwa dakin Umma....