← Book details Jiddatulkhair Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 205

Sashe 192

Jiddatulkhair Complete Hausa Novel · about 3 min read

gama gaisawan taso mu tafi... It's getting late" Hansai ta gwalo ido tace "Ku tafi ina?? To wllh wllh karyarka ya sha karya Malam, babu inda 'ya ta xata daga tsakar gidan nan, ko taku daya baxata yi daga nan ba wllh, ku je ina?? Lallai sannunka...." tana huci ta kare maganar ta dago Jiddah da xumar shigar da ita daki tana cewa "Tashi don ubanki, idan kin sake fita ko nan da kofar gida Allah ya tsine min albarkan da yayi min...." Daga kasa har sama Abuturrab ke kallon Hansai da wani expression, can yace "Kin manta ita din matar aure ce?" Hansai ta mulmulo wani uban xagi tace "Fadi duk uban da ka kashe ni me iya siyar da gidan nan ne in biyaka, a gidan ubanwa ta xama matar aure?? Ka dau min ya ka tafi ka lalatata kace min matar aure ce??" Abuturrab na kallon Jiddah yace "Zo mu tafi" Jiddah hawaye na sauka idonta ta kallesa sannan ta kalli Hansai dake kokarin janta xuwa cikin daki, cikin kuka tace "Baabarmu...." Hansai bata saurari me xata ce ba ta wanka mata wani mummunan mari da yasa taji diff, ta kuma kai mata wani tana huci tace "Rufe min baki don ubanki" bai san lkcn da ya karasa compound din ya fincike Jiddah a hannunta ba yace "Kinyi na farko kinyi na karshe, kin kuma ci albarkacin ki na matar babanta da wllh sai na rama mata" Daga haka ya nufi soro da Jiddah, Hansai ta lafta wani uban ihu ta bi bayansu tana kunduma xagi tace "Idan Jiddah ta sake barin gidan nan shegiya aka haifeni, wllh babu inda xata je kuma ka cika min 'ya ta" Ganin ta yo kansu Abuturrab ya kwasheta da kafa sai gata wanwas a kasa, ya bude front seat ya saka Jiddah dake ta kuka a ciki sannan ya kulle ya xaga ya shiga driver seat, Xulai ce ta fito da katon tabarya tana ihu wai jama'a su kawo masu dauki, Hansai ta mike a rikice ta amshe tabaryan, da duk karfinta ta buga glass din bangaren da Jiddah take, ihu Jiddan ta fasa a tsorace ya fixgota jikinsa tayi lamo, don sai da glass din yyi tsawa, Hansai ta shige gaban motar kamar mahaukaciya tana cewa "Da dai ka tafi da Jiddah gwara ka kasheni, ka kasheni nace d'an banxa... xan ga ta inda xaka bi ai, sai dai ka takeni, babu inda xaka kai min ya ta d'an yankan kai..." Abuturrab yyi reverse sosai sannan ya taho a guje, wani uban tsalle Hansai tayi ta kauce sai gata da Zulai kwance a kasa, ya ja motarsa a guje ya bar layin, kuka kawai Jiddah take kamar ranta xai fita, har suka fita titin hayi bai ce mata komai ba....
Chapter 192 · 0% Book details