← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 84

Sashe 84

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ranar suna tana cikin y'an'uwa suna hira taga kiran wayan ya khaleel ta bar wajan hiran ta fito harabar gidan ta xauna suna waya dashi a lallai sai taxo masaukinsu ya ganta dan tun asuba rabon ta dashi rarrashin sa takeyi sbd tasan muddin taje baxai bar tadawo da wuri ba da kyar ta rarrashesa akan ya jirata xata xo ammafa sai da yamma tana gama wayan tayi ajiyar xuciya tana murmushi
wata zazzak'an murya taji tai mata sallama a hankali ta waiwaya kyakkyawar matashiyar mace tagani me kyau sanye cikin abaya tayi rolling d'in kanta da gyalen abayan hannunta rik'e da jaka madaidaiciya kalan stone d'in abayar ta tunda taxo wajan ya d'umi da k'amshin jikinta.

amsa mata sallamar jannat tayi tana mmk ganin tana mmk yasa tayi murmushi ta mik'o mata hannu alamun su gaisa

"sunana JASRA BELLO MOD'IBBO munxo sunan Zahra ne mijinta abokin mijina ne, naga kema y'ar 9ja ce"

murmushi jannat tayi tana tuna sunan tabbas tasan sunan a kano
"sunana JANNAT ADAMU CHED'E"
ware ido jasra tayi cike da mmk tace

"mashaa Allah tabbas nasan sunan nan a Kano na kuma san sunan ahhh...."
tayi dariya bata k'arasa ba dariya itama janna tayi
"...a ina kika san sunan?"

".... awajan Ummee Garkuwa"
tak'ara sa tana kallon jannat
far tayi da ido
"tabbas hakane a novel d'inta Jennifer ko ?"
d'aga kai jasra tayi had'e da xama kusa da ita
"naji dad'in ganinki jannat dan nima ina son ganin Ummee Garkuwa ina son bata labarin kaina ta rubuta kamar yanda tayi naki"

"karki damu zan had'aki da ita "
"naji dad'i kuwa ki bani numb d'inta yanxu in ban ta kura miki ba"
"ba komai babu takwara ga numb d'in 080*********** "

"ngd sosai jannat bari na kirata mu gaisa tun yanxu dan gsky na matsu mu had'u da ita"

murmushi sukaiwa juna jasran ta sunkuyar da kanta tayi dialing number ta shiga ta d'an jima tana ringing sannan aka d'aga

Ummee Garkuwa:"assalamu alaykum"
Jasrah : "waalaikumus salam, dan Allah ina magana da Ummee Garkuwa?"
Ummee Garkuwa:"en itace ya kike?"
Jasrah:"lafiya lau ya jama'a?"
Ummee Garkuwa:"Alhamdulillah"
Jasrah:"na amshi numb d'inki a hannun jannat Adamu ched'e'

Ummee Garkuwa:"masha Allah kina tare da mutanen kirki"
Jasrah: " gaskiya kam hakane na amsa ne dan nabaki labarin kaina da kaina rikitaccen lbr mai ban tausayi ban haushi harma da takaici mai abin mmk da kuma soyayya mai karya xukata"
tak'arasa kamar xatayi kuka

Ummee Garkuwa:"tofah bari na gyara xama kin san mu da kibamu naman d'awisu k'ara ki bamu lbr"
dariya tayi jasrah

Jasrah:"kiyi hkr Ummee lbrn baxaiyiyu awaya ba sai na dawo 16 ga watan MAY in shaa Allah"
b'ata rai Ummin tayi kamar tana ganin ta
Ummee Garkuwa:"tohm shikenan Allah ya kaimu lokacin ngd sosai"
Jasrah:"ni ce da gdy zan kira latter ngd sosai byeee"
ta kashe wayan dai dai lokacin da jannat ta mik'e suka jeru tare suna hira suka shiga cikin gidan sunan.

kwanansu tara suka dawo daga sunan zahra da y'arta taci sunan umma Nabila watansu fawazz da sa'ud goma sha d'aya suna tafiya harda gudu ma dan sunyi wayo Muhammad miskilin yaro komai nashi na babansa sak ranar hindu ta haihu ta haifi namiji tunda ta haihu suke cikin hidima sosai hindu suna xaune lfy da abokiyar xamanta meenat suna mutunta juna sati nayi aka sawa d'an suna Abubakar sadik sun sha shagali sosai abin sai wanda ya gani dady da Abba kam cikin murna da godiyar Allah suke ta ko ina Allah na axurtasu da jikoki haka Umma da Momy dangi ya had'u ya cure sun maida kansu tamkar ciki d'aya sun had'a kansu suna kuma k'aunar junansu d'aya baxaiyi abuba batare da shawarar d'aya ba Alhamdulillah komai yayi yanda akeso sukam sai godiyar Allah hindu na kwance tana bawa d'an sadik nono mai gadin su yai sallama wai wani mutum yana sallama da ita da mmk ta fita wanda tagani ne yasa tak'ara sa da sauri kuka tasa
"Baba"
"naam hindu, Alhamdulillah Allah ngd maka dana ganki ahaka najin dad'in had'uwa da iyayenki da kikayi na kuma ji lbrn komai y'ata haka nakeso talatu Allah ya toni asirinta"
"hakane baba amma ya akayi haka ka fito daga prison ?"
jinjina kai yayi
"shareef alhussain ne ya satoni daga cen akan naxo na taimaka masa mu sato wani diamonds a gidan kayan tarihi na dubai d'in nima nagudo nan nasan bai isa yaxo nan yai min wani abun ba,
na tuba yanxu y'ata ba xan koma ko ina ba ina nan k'asata"
hindu na kuka ta cigaba da bashi lbr
nan da nan ta bashi lbrn komai ta kuma kira Abba tasanar dashi da kansa Abban yaxo suka tafi tare sbd ya mutunta shi kamar yanda yaiwa sauran da suka reni sauran y'ay'ansa.

agajiye ta dawo daga kasuwa falo tasa meshi shida Muhammad daya ke baccin agefan sa y'ar rainonta ta ajjiye fawazz ita ma ta ajjiye sa'ud da duk sukayi bacci tana k'ok'arin shiga ciki ya khaleel ya janyota jikinsa hannunsa kan cikinta yana shafawa yana kallonta zaro ido tayi tana kallon sa d'aga mata gira yayi
"yau zanyi wata ajiyar ta musamman dan 3ple zan ajjiye"

ware ido tayi sosai tana kallonsa dariya tayi ta xame kanta a hnkl
"ba ruwana Ummee Garkuwa tana jinka"
tab'e bakinsa yayi
"ina ruwana da Ummee Garkuwa bata son ke matata bace ? ki shirya beautyna yau fa sai na miki kyakkyawar ajiya ta musamman!"

TAMMAT BI HAMDULLAH

abin da yawa ina gaishe da kowa da kowa musamman masu bibiyar Jennifer da kuma way'anda suka bani shawarwari ngd sosai sai mun had'u awani novel d'in
*Ummee Garkuwa*
Chapter 84 · 0% Book details