← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 84

Sashe 19

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ganin shi yayi cikin wani daki mai duhu sosai yanda ba ya iya ganin komai can haske ya bayyana ya ganta tsaye da bakaken kaya da bindiga babba tana mishi murmushi meyasa kk son sanin ko ni wacece ?? Ya kalleta da mmk ina son insan mekikeyi a gidanmu ?? Ta bata rai xuwa nayi in kasheku araxa ne ya kalleta wani laifi muka aikta miki da kikeson ganin bayanmu ?? Babban dalili ne ina son daukar fansan iyayena da kuka kashe min su yanxu xan kasheka suma inkashe su Ta nunashi da bindiga .......a firgice ya farka ya hada gumi sosai yana ajiyar xuciya sai yanxu ya fahimci mafarki yayi me ba tsoro tashi yayi yana tunanin mafarkin yarasa me xaiyi laptop ya janyo yana duba abinda ya dace yayi istargram ya bude yana dubawa ya ga mahboob ya dora pix dinshi da Jennifer mutane da yawa sunyi liking suna xuxuta Kyan hoton ya duba yaga pix din yau kwana 3 da dorashi comments yake bi yana jin haushin xuxuta kyan Jennifer da sukeyi idonshi ya sauka kan wani comment da yagani ....kai menene hadinka da SULTHANA??? ya xare ido yana kallon comment din sulthana ?? Kanshi ya daure da sauri ya duba profile na mutumin daya ga sunashi Elmustafha ya duba yaga abinda yake son gani sauka yayi saga IG din yana jin dadin abinda ya gani dan xai tai maka masa sosai dabara ta fado masa yayi murmushi ya kwanta yasan Sam shida bacci kuma sai ya gano wacece jennifer ??

Washegari da safe bayan sunyi break fast sun fito shida mahboob haisam ya kalli mahboob am mahboob ina son kabani laptop dinka da kake chat oh ! Tana daki na wullar da ita kasan kwana 2 dinnan dady ya bani aiki na kula da sababbin ginaginan shi ban sami lokaci na duba social network ba hamdala haisam yayi yanxuma cen xan wuce jiyma fa sai 6 na adawo yau ban San ma lokacin da xan dawo ba ya wuce sai na dwo OK Allah ya dawo da kai lafiya kai tsaye dakinshi ya wuce ya dauko laptop din bai sha wahala ba dan yasan code dinshi ya bude istargram yana jin fargaba dan baisan mai xai tarar ba test ya gani masu yawa da notification
Test din ya bude wani test ya fisgeshi na Ammar ibn Muhammad ..hi guy meya hdaka da Hindu ?? Kasan wacece ita kai gaggawar goge pix din nan idan kuwa ba haka ba xakayi nadama kuma xaka Sa kanka cikin tashin hnkl

By
*UMMEEY*
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

43&44

Kallon shi sukeyi xuciyoyinsu cike da mmkin ganin su haka da sauri Jidda ta juya tabar wajan zahra ta bita murmushi yayi hannunsa rike dana jenny yai wajan Momy cikin farin ciki yace Momy jenny taxama Yar ki ya ruko hannun Momy ya mika mata hannun Jennifer Jennifer taxama tamu ta fada min tana son ta musulunta fuska Momy ta saki hade da fadin alhmdllh nagode wa Allah rungume jenny tayi ruby ma takara so ta rungume ta naji dadi sosai ta ruko hannunta sukai cikin gidan xuciyar Jennifer tass da ita duk da tana cikin kunci Momy tace zan kira dadynku na fada mishi zansa khaleel yanxu yaje ya taho da Malan Dr Ahmad Sani ningi yaxo ya baki Kalmar shahada da duk abinda ya kamata dai toh Momy ngd a a karkiji komai Jennifer kin zama tawa ina jinki kamar yata Momy ta mike bari na hau sama ruby ta taso kusa da ita ina cikin farin ciki jenny yau xaki karbi Kalmar shahada murmushi tayi itama nima haka ruby xuwa anjima kinxama mu mun xama ke ta mike itama bari naje nayi wanka nagaji itama mikewa Jennifer tayi ta shiga dakinta aciki ta samesu kowacce fuskarta a daure zahra ce ta rufe kofar Jidda cikin kuka nan gidan kune ? Shiru tayi dan bata da amsar bata ke wacc e irin munafukan yarinya ne ? Zahra da take a tsaye ta janyo akwatin kayan jenny tace yanda kikaxo haka xaki koma yau yau din nan kibar gidan nan tunda bana ubanki bane cikin kuluwa jenny tace dole na bar muku gidanku dan nima nagaji da cin mutunci barina gidan baxai xama karshen rayuwata ba duk da ina talaka to xuciyata ba talaka bace ta janyo akwatinta ta fito ba kowa a falo gab da xata fita ta hango suwaiba da sauri ta karaso jenny me ya faru hawaye ya sauko mata suwaiba masu gida sun koreni su wa ?,zahra da Jidda salati suwaiba tayi jenny ta juya ta bar gidan

******* **********

Gidan hindu ta sauka tana ta ruko jakarta hawaye na xuba a falo ta tadda sulthana tana kallo ta wullar da jakar kayanta ta shiga daki tana kuka sosai ta fada kan gado ta rushe da kuka sulthana ta biyo bayanta ta tsaya bakin kofa tana kallonta tana kuka karaso wa kusa da ita tayi ta rike mata hannu xatayi mgn itama kukan ya kufce mata kiyi hkr jenny haka Allah ya kaddara mana dole mu dauki wannan kaddarar jarabawa ce daga ubangiji Allah muyi hakuri mu cinye akwai kyakkyawar rayuwa nan gaba Allah baya jarabtar mutanen banxa hindu ta fito daga wanka ganin suna kuka yasa itama ta karaso kusa dasu ta rungumesu duka dolene muyi kuka dan munga rayuwa kuyi hkr yan uwana addu'ace mafitar mu dai dai lokacin haisam ya shigo sunyi matukar bashi tausayi ya tsaya yana kallonsu xuciyar shi a raunane jenny ta kallesu baku San me nake jiba ni kadai nasan irin feelings din dana keji yanda kikeji hk kowa yakeji hindu tace tana share kwalla a xuciye jenny tace kuma sai kin min fada ? Sulthana ta hararesu hade da yin tsaki ta nuna Jennifer jenny kike ko jinnu sunanki ya dace dake jinni cike da jin haushi jenny tace ke kuma ifrituwa what ? Ifrituwa ? Dariya hindu tayi kun radawa kanku sunan da ya dace daku ifritu ta kumayin dariya yadace da ke ta nuna sulthana akufule tace ke kuma kwankwamai mikewa hindu tayi ta nuna sulthana da yatsa wacece kwankwamai ? Itama mikewa tayi kece kwankwamai wani abun xakiyi ? Haisam ne yace dasu ya isa haka kuna bani mmk yanxu yanxu fa kuka gama kukan halin da kuke ciki baxa Ku taba zama lfy waje daya ba oh ya rabbi ya rike kai sulthana ta Matso kusa da shi sorry ya haisam bai amsa ba jenny naga akwatin ki a falo me ya faru ? Masu gidan ne suka koreni xaro ido yayi bangane ba ? Zahra da Jidda ya salam ! Sbd me ? Suna zargin muna soyayya da ya khaleel janyo stool yayi ya xauna al'amarin ya khaleel dinne da daure kai kinsan haka ya taramu nida mahboob yai mana warning mu fita harkanki ban gane ba ya haisam ya girgixa kai eh shiyasa kika ga mahboob ya dan canza miki ni kaina banda nasan Jidda xai aura zanyi tunanin ko sanki yake lumshe ido tayi ina addu'a Allah yasa kada zargina ya tabbata jenny jikin Jennifer a sanyaye ta tashi inaga ba Ku fahimce shi bane murmushi yayi ki tashi mu koma gida kiyi hkr ni kaina wani Sa in inna kalleki inajin kunya da kuma nadamar abinda nai miki a baya ya haisam kabar tuna baya komai ya wuce ni kai ne kaxame min fitila wacce tasa nasan wacece ni abu daya nake so kai min kanuna Sam baka son inda nakeba koda zakaji suna cigiya ta yai shiru plx ya haisam shikenan xanyi yadda kikso ya mike xanje gida dan Allah ki kula da kanki kada kuyita fadace fadace murmushi tayi baxanyi ba yana kokarin fita sulthana tace ya haisam ba sallma OK hindu zan tafi sai na dawo kwafa tayi ba hindu bace sulthana ce cikin ko inkula yace OK ya fice
Chapter 19 · 0% Book details