← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 84

Sashe 51

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

bayan suna da sati d'aya suna xaune a falo hishma tana hannun hajiya murja Afra na hannun hajiyarmu Nabila na kusa da mijinta suna hira cike da farin ciki hajiya Nabila tace,
" hajiyanmu ki shaida na bawa murja hishma halak malak dana yayeta ta rik'eta a hannunta kafin Allah ya bata dan na d'an d'ana rashin y'a nasan hakan xai sanya ta cikin farin ciki,
ai kam tana kawowa nan hajiya murja ta fashe da kukan farin ciki cike da farin ciki Alhaji yace "Nabila na jinjina miki kinyi namijin k'ok'ari Allah yai miki albarka,
itama hajiyarmu mmk tayi kamar ta xubar da hawaye tace,
"Nabilata Allah yai miki albarka kin biyani labila kin gama min komai kin birgeni ta waiwayo kan murja data ke rungume da hishma tana kuka,
"murja ki yi hkr ki daina wannan kukan dan kin cancanci abaki hishma sbd alkairinki da mutuncinki tunda kikaxo gidan nan kike mana biyayya da girmama mu cikin yaran nan kikai ta mana hidima babu abinda yake ranki najin haushi ko akasin haka kowa ya san da wannan duniya ta sheda hakan babu abinda xamiyi mu saka miki irin haka, ubangiji Allah ya baki naki y'ay'an suka amsa da "amin
jikin murja asanyaye tace " ina kukane na farin ciki dan wllh banta b'a jin cewa bani na haifi yaran nan ba ina jin su kamar tsokata ina jin soyayyarsu fiye da yadda nake son kaina ubangiji Allah ya raya min su jikinsu asanyaye suka amsa da "amin

mutane da yawa sunyi farin ciki da wannan kyauta da hjy Nabila tai wa kishiyarta hjy murja cikin kuwa harda dangin Nabilan dan suna matukar son murja saboda tsananin kirkinta uwa uba soyayya da wahalar da jikinta datakeyi dan ta farantawa Nabila,

ranar da sukayi arba'in haka akayi ta sadaka da abubuwa na ban mmk iri iri akayi shagali sannan aka watse kowa yana addu'ar Allah ya raya yan biyu AFRAH itace (jannat) HISHMA itace (Hindu)

bayan kwana goma dayin arba'in hajiya Nabila ranar ad'akin alhaji take ta gama ba yan biyunta nono tasasu agadonsu wanda yake gefen nasu gadon da daddare suka kwanta bacci,
washe gari aka nemi yara sama ko k'asa aka rasa tun sunayi isu isu har abu ya wuce xatonsu tuni hjy murja ta yanke jiki ta fad'i asume tana kururuwar y'arta Hishma kan kace me nan da nan lbr ya karad'e ched'e estate ana dube dube lungu da sak'o na ko ina sai da akayowa ched'e estate mugun chaje ba yara babu batunsu adamu tuni xuciyarshi tafara bugawa itama hajiyarmu jiri ya fara d'ibanta ta fara layi ta yanke jiki ta fad'i sanadiyyar haka ta kamu da ciwon b'arin jiki d'aya azababban fad'a ya kaure a ched'e family nan da nan suka shiga xargin juna ana ta xargi kowa da wanda yake zargi hjy Nabila kuwa kukan ma kasa yinshi tayi sai na xuciyarta wanda sanadin shi yasa xuciyarta ta kunbura

wasa wasa sai da aka kwashe wata biyar cif duk wanda ka gani cikin su hud'un nan sai ka tausaya masa alhaji adam da mahaifiyarsa da uwar gidansa da amaryarsa sun kad'e sun rame babu mai walwala bare mgn ana haka ciki ya b'ullo jikin hajiya Nabila nan da nan aka hau rabi da rabi wato farin ciki mai had'e da bak'in ciki cikin sai da yai wata hudu basu san dashi ba sbd mummunan yanayin da suka tsinci kansu,

haka aka reni cikin cikin kulawa da ta ka tsantsan bayan wata tara ta haifi y'arta mace aka sa mata sunan maman murja khadeeja suka b'oye sunan suke kiranta da jasrah yarinyar kamarta d'aya da mahaifinta wato kamar yayyanta da suka b'ata shekara d'aya da akai neman duniya aka rasasu har masu binciken da suka fi kowa iyawa aka d'auko da ga abroad basu gane kan abinba haka dai suka hkr akaita rok'on Allah akan ya bayyanasu duk lokacin da suka kalli fuskar yarsu jasrah sai sun xubar da hawaye dan kamarta da y'anuwanta har ta b'aci babu abinda ya banbanta su cikin farin ciki da bak'in ciki aka cigaba da rainon JASRAH (sulthana)
cike da kulawa da tsaro na musamman dan har camera aka bi aka like xagayen gidan da bak'in k'ofar get d'in nashiga ched'e estate gaba d'aya wajan b'angaren Alhaji Adamu xagaye yake da sojoji masu tsaron gidan, amma dake mai son abinka ya fika dabara bayan kwana hamsin aka wayi gari da sojojin da mutanen cikin gidan da masu gadin ched'e estate har da mak'otan gidan ched'en suna wani irin axababban bacci wanda suka k'i farkawa sai da taimakon manyan likitoci aka kuma nemi Jasrah aka rasa sama ko k'asa innalillahi wa inna ilaihi raji'un abinda dangin ched'e suke kira kenan dan abin ya wuce tunaninsu koke koke da masifaffen tashin hnkl nan da nan fad'a ya kaure atsakaninsu cike da zargin kawunan su da aibata junansu,

sai dare Adamu da matarsa hajiya nabila suka farka sbd abin yafi shigarsu sosai sauran sun farka da wuri, farkawar su jin mummunan labarin b'atan jasrah hajiya Nabila komawa tayi asume dan sai da tashafe awa biyar bata farkaba shi kam Alhaji kasa komai yayi sai k'unar xuciya haka ya dinka fitar da numfashi sama sama kamar xai daina fidda shi hajiya zainab ma tuni b'arin jinkita ya xuke sbd fad'uwar da ta kuma yi sbd jin mummunan labarin hjy murja itama suman tayi,

dangi ya rikice fad'a ijunan su ijunan su har ta kai ga ana bawa hammata iska dama gasu rigimammu haka suka dinka fad'a abubuwa suka had'u su kaiwa alhaji yawa ga masifar rashin y'ay'ansa da tunanin mai yanke masa jindad'insa ga axabar fad'an danginsa tarasu yayi ya fashe da kuka yace xai bar kasar ya gaji ba xai iya ba suna cikin masifar ya kwashe iyalinsa da matansa da mahaifiyar shi ya bar musu 9ja gaba d'aya sanadiyyar tafiyarshi sanadin wargajewar dangin basu bar estate dinba amma sun xama mak'iyan juna su kansu iyalin Adamu ched'en danginsa suke zargi sanadiyyar hakan hajiyarmu take xaune akan wannan keken mahaifiyar ku kuma har yau acikin cuta take sauk'i kam sai dai daga Allah mahaifinku kam sanadiyyar barin shi 9ja kenan dan ko ya shigo ta baya iya wuce kwana biyu nema da bincike babu wanda ba a yiba har yau ba asan wanene ya aikata hakan ba cikin hikima ta Allah sai gashi ya dawo mana da ku dolene kam mu godewa Allah ta k'arasa da kuka mai ban tausayi,

gaba d'aya jikinsu sanyi yayi lokaci d'aya suka sa kuka cikin wani yanayi na jin tausayin iyayensu jannat ce tace " haryamxu ba'asan waye ya aikata hakan ba ? d'aga mata kai hajiya murja tayi,
" lallai tsugunne bata k'are ba tunda ba'asan kowa ye bane ta fashe da kuka tacigaba da cewa,
" nan da kowanne lokaci xa'a k'ara rabamu da ku kunsan irin wahalar da mukasha akan azababban sihirin dake jikinmu ?
awajan Kristen na tashi su suka reneni kan addininsu basu cutar dani ba illah gata da suka bani da kyar Allah ya taimakeni na amshi musulunci da taimakon mijina da iyayensa ga hindu cen tana fama da damfara da kwace kud'in mutane tana abu kamar namiji wannan ganin nakuma sai da ta damfare babban yaronka Abba wannan sulthana ce ba uban da tabari kowa rashin kunya ta ke masa, wahalarmu bata k'are ba tunda har yanxu ba'asan mai aikata hakan ba a tsorace dukansu suke kallonta cike da gamsuwa da bayaninta dukkansu maganganinta sun tsorata su sunkuma basu mmk da mugun takaici na rashin sanin tak'amai mai wake xaluntarsu shin yanxu kenan wani aiki sabone agabansu ? lallai kam dawowarsu xaisa mai aikata musu wannan muguntar yafara sabon shiri na yadda xai k'ara rabasu wai shin tayaya xasu gane waye mai ha'intarsu me sukai masa yake son jefa rayuwarsu cikin masifa yake gaba da farin cikinsu innalillahi wa innalaihi rajiun TSUGUNNE BATA K'ARE BA !

by
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

85&86
Chapter 51 · 0% Book details