← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 84

Sashe 67

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan ta fito daga wanka tana shafa mai rubayya data ke waya ta waiwayo ta kalleta
"antynmu ance inmiki sannu da xuwa"
da mmk jannat ta kalleta kafin tayi mgn sulthana ta katseta
"anty rubayya ki fad'a mata gsky,
anty jannat bayan tafiyarki ansawa anty rubayya rana"
da murna jannat ta bud'e baki
"mashaa Allah naji dad'i"
sulthana tace "baki tambayeni waye angonba"
"waye angon namu"
far sulthana tayi da ido
"yaya prince A.K Garkuwa"
da murna jannat tace
"ikon Allah naji dad'i sosai"
sulthana ta cigaba da mgn
"ansa rana d'aya da bikinki da ya khaleel wato nan da 2 weeks sai ki shirya yanxu amaren biyar ne " jannat ta ce "biyar kuma?"
zahra tai saurin cewa
"hindu ce cikon ta biyar ita da yaya hafiz k'anin hjy murja ni kad'ai ce nayi saura acikin ku"
wani iri jannat taji tausayin zahra ya kamata muryarta a d'an sanyaye tace.
"bakomai zahra komai lokaci ne idan yayi dole ayishi Allah ya baki nagari"
dukansu suka amsa da
"amin"

washegari da yamma suna gerdin d'in gidan kamar yanda suka saba suna hira jannat hankalinta nakan ya khaleel da suka fita yau tun safe shida Abba da dady wayar sulthana tayi k'ara tana duba screen d'in wayar sunan ya mukarram ta gani ta d'aga yace ta xo yanxun nan yana son ganinta yana kashewa ta mik'e tana mmkin wannan kiran na gaggawa da yai mata a bayan gidan ta sameshi yana waya kana gani kasan da mace yakeyi ganinta yasa ya kashe wayan
"xauna kiji wani abu k'anwata"
murgud'a baki tayi "kawai kafad'amin ba sai na xauna ba"
hararta yayi
"ina nan fa da halina ba canxawa nayi ba ko ki xauna kona nad'a miki duka"
zama tayi tana turo baki
"shikenan sai ace xa'a dakeni danna k'i xama"
dariya yayi
"yi hkr k'anwata kin san me ya faru ?"
k'ara turo baki tayi
"ina xan sani tunda ni ba allan musuru bace"
tak'arasa da murgud'a baki.
dariya ya kuma yi
"ina son wannan siririyar nan wata ke ma ?"
sakin fuskarta tayi tana dariya
"wacce acikinsu fad'i naji?"
"wata siririya zahrah "
wata iriyar dariya tayi.
"zahra ce naji dad'i ya mukarram"
"yanxu sulthana ya xa'ayi ? nifa in san samuna ne a had'a da bikinku har nawa"
mik'ewa tayi
"barmin aikin awajena nasan yadda xanyi"
"yawwa sulthana ina jiranki" ta tafi tana tsokanar shi ya bita da murmushi.

da daddare suna xaune dukansu xa'a fara tattauna abubuwan da xaayi da bikin anan hajiya murja tace "tana son xasu tafi italy ita amaren cen babban companyn daya ke kayan d'aki su xab'i wanda suke so daga nan tana son suje india subawa companyn rajah sarry su fidda irin designing na kayan da xasuyi fitar biki dashi da kuma dubai nam ma suje companyn El'mukhtar suba su aikin kalan kayan daxasu saka na biki da kuma yanayin irin adon sark'ar da xasu saka haka ta d'ink'a lissafe lissafe.
Abba yace
"bakomai xuwa jibi ma xasu fara tafiye tafiyen kuje duk inda kukeso"
kamar wata yarinya suna cikin tsare tsare sulthana tace,
"ya mukarram na fad'a ?"
ware ido yayi yakasa magana dan baiyi tunanin wannan wautar xatai masa ba.
hajiya Nabila ta kalleta dan kowa mmkin mganarta yayi
"fad'i mana"
ta yi dariya
"ya mukarram bari na fad'a"
kamar ya nutse dan kunya.
"cewa yayi wai yana son zahra wai asa ranar auren dashi"
dariya sukayi dukansu
Abbu yace
"ja'iri kalli yanda yake k'ifta ido"
Abba yace
"mai xai hana mukarram in dai tana sonka"
dady cike da murna yace
"nabashi ai mukarram mai xab'awa zahra mijine"
Abbuu yace
"ah'ah Dr sai fa munji ta bakin zahra baxa aiwa y'ata dole ba"
Abba yai dariya yana jin dad'i mara misaltuwa daa gidansa ya kasance ana rayuwar bak'in ciki ta dalilin rasa gudan jininsa yanxu ta dalilin gudan jinin nasa ana rayuwar farin ciki sannan gidan nashi cike da mutanen arxik'i way'anda baxai iya fad'in adadin alkairinsu akanshi ba dan sun reni tsokar jikinsa batare da sun axabtar dasu ba,
Abbuune ya katsewa Abba tunaninsa
"kana ji Alhaji Adam wai sai anyiwa y'ata dole abari muji ta bakin ta"
kansa Abba ya girgixa
"a'ah nima ina bayan Dr Bashir mun bawa mukarram zahra"
itakam kanta yana sunkuye dad'i ya cikata tunda ta ganshi taji yai mata sai gashi shima ya nuna yana sonta itakam tayaya xata k'i wannan santalelen balaraben.
hjy murja ce ta katsesu da cewa
"zahra kina son d'ana mukarram"
murmushi zahra tayi ta rufe fuskarta
jidda datake gefe tace
"tana sonshi gashi nan ta rufe ido tana dariya"
dariya sukayi dukansu
Abba yace
"mashaa Allah nayiwa Allah gdy daya nuna min wannan rana ina jin farin ciki mara misaltuwa Allah ngd maka"
papa dayake gefe tunda aka fara mgn baice komai ba shida maman david da yaransu sai dai in anyi abin dariya suyi.
ya kalli dady
"Dr bashir plx a ina ake siyan form a cike idan xa'a shiga musulunci ? ni dai ina son cike form d'in nan dan xama na daku na d'an wannan lokacin yasa na fahimci addininku addinin gsky ne addinin taimako addinin da baya kyamatar wanda ba d'an addinin ba addini mai cike da tsabta da son junansu addini mai cike da dogara ga Allah addini mai taimakon marasa shi
[2/28, 6:44 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

103&104

*Ummee Garkuwa*

cike da murna suke kallonsa dan basu tab'a tunanin wannan maganganun nasa ba shiru yayi yana kallonsu.
dady yace,
"Alhamdulillah Allah mungode maka,
mr Solomon naji dad'in maganar ka duk da wannan ba abin mmk bane idan aka duba Allah subhanahu wata'ala dan shine mai shiryarwa mun godewa Allah daka kasance shiryayye, sannan shi musulinci tushensa shine imani da Allah
da kayi imani da Allah to magana ta k'are sai kuma kayi shahada ba'a cike form bare asiya don shi addinin mu addinine na aminci da salama da kuma zaman lafiya ubangiji Allah ya dad'a shiryar damu."
nan dady ya bashi kalman shahada ya amsa cike da murna itama maman david aka bata tayi d'aya bayan d'aya aka basu kalmar shahada suka amsa.
jannat tayi mmkin hakan dan tasan su d'in mutane masu ak'ida da son addininsu lallai Allah shine mai shiryarwa ta fahimci dan basu san ya musulman suke bane tuntuni tunda gashi d'an xaman da sukayi tare yasa sun musulunta ubangiji Allah ya shiryar da bayinsa.
dady ya cigaba da mgn,
"menene sunanka?"
"solomon "
"akwai sunan da kk so?"
shiru yayi yana nazari.
Abba ne yace,
"tunda sunan shi Solomon ya xauna da sunan nashi Sulaiman ko ya ka gani ?"
da sauri yace
"eh haka yayi"
maman david tace
"ni sunana sera amma ina son na kuma fateema"
dady yace
"masha Allah fateema suna mai daraja"
ta nuna Emanuel
Abba yace,
"emah kaifa?
kansa a k'asa yace,
"ina son sunan kabeer"
Abba yace
"mashaa Allah kabeer daga yau ka kuma kabeer"
david daya ke kusa da maman shi yace,
"ni dai ina son yusuf"
dady yace,
"masha Allah yusuf sunan annabin Allah suna mai daraja,
ubangijin Allah ya tada kafad'inmu a aljannah"
dukansu suka amsa da
"amin"

Abbu yace,
"mahboob ya dai ? wacece surukar tawa ne ?
murmushi mahboob d'in yayi
"Abba ba yanxu ba tana karatune sai ta gama"
"toh mahboob ubangiji Allah ya kaimu lokacin"
suka amsa da amin
suka cigaba da tattaunawa inda xasu d'auko malamin da xai koya wa su papa yadda xasu kula da addini.

2 days ago
Sun gama shirinsu tsab xasu fara tafiya Italy jannat kam jikinta asanyaye yake tana tuna halin da ya khaleel xai shiga.
d'akinsa taje yana xaune fuskarsa kamar pepper tayi sallama ya amsa batare da ya d'ago kansa ba kanshi akan waya yana dannawa.
aranta tace "yau kam dannan waya akata shi dashi"
kusa dashi taje ta xaune had'e dasa kanta ak'irjinsa
bai kalleta ba still kanshi na sunkuya yana dannan waya
"ya khaleel" ta fad'a muryar ta assnyaye.
bai amsa ba bai nuna wata alama na taxo kusa dashi ba tasan abinda yake yiwa sbd xasu tafi ba xasu dawo ba sai sun gama xuwa ko ina wanda suna dawowa xa'a fara hidiman biki.
muryar ta kamar xatayi kuka tace,
"ya khaleel kana son jefani cikin wani hali?
kasan yanda nakeji idan ranka ya b'aci, idan har baka son tafiyar nan baxan tab'a yinta ba dan baxanso naje wajan da hnklin ka bai kwanta ba"
d'ago kansa yayi ya kalleta.
kamar baxaiyi mgn ba da kyar ya jure yanayinsa yace,
"me kikeso nace? kin san irin yanayin dana ke kasancewa idan bana tare dake?
ba ina jin haushin ki bane ina tausayawa kaina halin da zan kasance idan banji lallausan jikinki ajikina ba"
lumshe ido tayi tana jin ba dad'i ita kanta bata son tafiyar kawai bata da yadda xatayine.
"nasani ya khaleel yanxu ya kk ganin zanyi ko kawai nace ba xani ba?"
fuskarsa yasaki kad'an ya sa hannu ya kwanto ta jikinsa.
"ina sonki jannah!"
kwanciya tayi ajikinsa had'e da sakin numfashi.
"ina sonka sosai ya khaleel"
shafa kanta yayi,
"kada ki damu kuje tunda hidima ce"
ashagwabe tace,
"nifa bazan tafi na barka ba"
cike da jin dad'i ya xaro ido
yasa hannunshi dai dai sai tun xuciyarta.
"ina nan cikin xuciyarki baxaki tafi ki barni ba kullum xuciyoyinmu suna tare da juna"
ranta ajagule ta tab'e baki.
"bana son nayi nesa da kai fa"
ajjiye wayar hannunsa yayi ya kishingid'a.
tabishi had'e da bajewa ajikinsa.
"waya ce miki xa muyi nesa da juna ?"
ya kalli agogon hannunsa
"tashi kije kada suyi ta jiranki"
wani kallo tai masa na mmk.
"korata kakeyi?"
yayi dariya
"bance ba"
ya fad'a yana kallon fuskarta datake a d'aure,
kwanciya ta kumayi ajikinsa.
"toh na fasa xuwa"
mik'ar da ita yayi,
ya shafa lip d'inta
"ina son d'ank'ara min bakin nan naki"
ya janyota yasa bakin shi cikin nata ya tsotse su tass sannan ya saketa yana numfashi.
ta mik'e jikinta a mace.
"muntafi ya khaleel ka kulamin da kanka"
kai ya d'aga mata yana shafa sumar kansa.

tayi mmkin rashin nuna damuwarsa akan tafiyar tasu sosai
ta fito ta samesu sun shirya kafin su k'arasa airport sai da sukaje kasuwa sbd jirgin nasu sai yamma xai tashi.
Chapter 67 · 0% Book details