← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 84

Sashe 11

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kwance adaki suwaiba na karatun kur'ani duk tabi ta rude tana saurarenta hnklinta amatukar tashe jikinta har rawa yakeyi wayarta tai kara tana dubawa taga sunan Momy aladabce ta daga ....Jennifer xo ina son ganinki ....
Ta amsa da toh ganinan Momy da sauri ta mike tai bangren momyn ababban falo ta sameta a xaune Jidda tayi matashi ta cinyar ta tana kallon tv tashigo falon suka gaisa yauwa Jennifer xakuje kasuwa tundaxu na aiki danjuma shiru bai dawo ba ga yamma xatayi kuma ba kowa sai haisam da khaleel nasan bakwa shiri da haisam khaleel xai kaiki da sauri Jidda ta daga kanta daga cinyar Momy Momy nima xani murmushi momy tayi svd kinji nace khaleel ne xai kaita sarkin kishi tayi dariya aa Momy bana son ya dinka kallon wasu yanmatan ne a kasuwa ko su su gane minshi kwara na bi abina rike haba Momy tayi oh ! To sai kibishi kiyi ganinsa ta mike bari naje na shirya ta ayangance take tafiya kamar batason taka kasa bakin ciki ya dami Jennifer bata maraba da wannan tafiyar Sam ! Koka dan batayi farin ciki da itaba Momy ta kalli Jennifer kije ki shirya nai masa mgn toh tace ta mike tai bangarensu ranta abace ta koma daki ta canza kaya gown tasa ta atamfa blue da adon yellow ajikinta daura dankwali na bata wuya dan bata saba sakashi ba karamin gyale yellow tasa tai rollin din kanta dashi powder kawai tashafa a fuskarta ta fito ranta abace xata hada tafiya da Jidda da kuma ya khaleel ta runtse ido tasan yau kam sai sun sata takaici babban falo ta koma ta taddashi xaune shida Momy yana sanye da 3 quarter blue black da Riga maroon wacce ta kamashi me kajeran hannu ta fuskanci yana matukar San 3 quarter dan in dai ba wajan da xashi me matukar muhimmanci bane tofa shigar shikenan kwas kwas sukaji da takalmi ta sakko itama sanye cikin wando pencil da riga brown ta Dora kimono gown asamansu sai dan karamin gyale da ta yafa tayi Kyau sosai runtse ido Jennifer tayi cikin tashin hnkl musamman kallon dataga ya khaleel yana mata ga mmkinta sai taji yace Jidda kije kisa hijab ta turo baki tana diren diren kafafu tana shagwaba wanne irin hijab ya khaleel nida ba sallah zanyi ba OK toh babu inda xaki cikin kukan shagwaba ta kwabe baki Momy 😫😫kinga ya khaleel ko ?? Wai baxai je dani ba ni wllh sai naje Momy tace haba khaleel ka kyaleta mana tunda ta riga ta shirya mikewa yayi baice komai ba yafita Jidda tabi bayanshi tana cigaba da kukan shagwaba da dire diren kafafu murmushi Momy tayi ta mikawa Jennifer jakar kudin da xatai siyayya da list din abinda take bukata ta amsa ta fito fuskarta a damke haushin Jidda ya kamata tana kallon lokacin da ta budewa ya khaleel mota sannan ta xagayo ta shiga gaba jikin Jennifer asanyaye ta bude baya tashiga ta rufo mator tana dai daita zamanta cikin motar list din abinda xata siya ya fadi ta sunkuyar da kanta xata dauko dai dai lokacin da Jidda ta Dora kafarta aka taya khaleel da sauri Jennifer ta dago ta jingina da kujerar motar dama tasan kawai yau cinikin bacin ranta xaayi yaja motar suka fice daga gidan Jidda tana xuba masa hira kala kala shi dai yana binta da uhhim ko um ko yace himm a haka sukaje kasuwar a mota Jennifer ta barsu ta shiga ciki bata bata lokaci ba ta gama ta hangosu tsaye ajikin mota taxo gab dasu ya bude mata but taxuba kayan kwala mata kira taji anyi kafin ta waiwayo taji an rungumeta tana waiwayowa taga Janata kawarta a skul cikin murna ta kankameta Jennifer kina nan ?? Ta tmbayeta cike da murna tunda muka gama skul ba'ajin lbrinku wani ne ya karaso kusa dasu sanye cikin coat ash colour ya dafa kafadar Janata yana murmushi Jennifer wannan shine Emanuel yayana da yace karatu a England ya mikowa Jennifer hannu su gaisa da sauri ya khaleel ya mika nashi suka gaisa hade da jifan Jennifer da harara mmk ya kamat ita jidda mmk tayi suka gama gaisawa hade da musayar numbers sukayi sallama suka shiga mota

Bayan sun dawo gida ta koma wajan Momy tana falo ita dasu zahra suka shigo tabar Jidda acen wajan ya khaleel tana zama ta shigo ta xauna akan kujera hade da fadin wash ! Momy mun dawo Jennifer ta mike tana shirin tafiya Jidda tqce ta hau sama ta wanke mata toilet Momy tace a a bari sa'a taxo ta wanke miki zahra tace no mom kibari ta wanke tunda itace a nan ta nufi upstairs xata hau Jidda tace kinga kada kiyi wahalar wanke pants din ki hada har pad din ki xubar kai kawai Jennifer ta daga mata ta wuce cike da takaici tana bude toilet din ta ganshi faca faca ga karnin jini haka ta gyara toilet din pants me hade da pad Wanda tai amfani dasu gasu nan xube ta hade su ta xubar xuciyarta na tashi dan tatsani karjin jini tagama xata fito Jidda tashigo dakin cikin fara'a kin gama ko ? Ngd ta miko mata turare Jennifer ta amsa hade da godiya ta fita tana komawa dakinsu ta wuce toilet ta kwara amai tana jinjina wannan kaxantar ta fuskanci Jidda na da kirki kamar Rubayya

Da daddare suka shigo itada suwaiba dan debe kayan da masu gidan suka ci abinci a dining suna jin hirarsu kamar ko yaushe cikin nishadi da jin dadi dady yace haisam gobe fa xamu tafi Dubai tare dakai da tare da khaleel xamu tafi kasan yanxu yayi bakuwa ba shi ba barinta dariya dukansu sukayi tana jin muryar zahra harda kyalkyalawa da sauri Jennifer ta kwashe sauran kayan ta fice ranta bace

Washe gari da yamma suna babban falo dady da haisam sun shirya xasu tafi Jennifer ta shigo falon tana hawaye lafiya Jennifer ?? Momy ta tambayeta cikin muryar kuka tace rashin lafiyar David ce ta tashi suna asibitin nassarawa zanje nagansu dady yace ayya ! Sorry Allah ya bashi lfy dukansu suka amsa da amin banda haisam da mmkinta yasashi cikin bahagon tunani dady ya xaro kudi masu yawa yabawa Jennifer ta amsa tai gdy ta fito daga falon suma suka fito suka shiga mota driver yaja me gadi ya bude gate dai dai lokacin da xasu fita haisam ya ganta tashiga adaidaita sahu ya runtse ido cikin fargaba dan yasan inda xata shin idan sun hadu da ita acen me xatai musu ? Kasheku xatai xuciyarshi ta bashi amsa kan wane dalili ? Abinda yakasa Sani kenan

By
*UMMEEEYY*
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

25&26

Al'amarinta ya daina bashi mmk sai ta'ajjubi kansa ya daure sosai ya rasa kalan tunanin da xaiyi ya samu mafita ya kwantar da kanshi jikin kujerar mota ranshi na suya shin me xatai musu in sunje cen ?? Meyesa anan take boye muguwar akidarta a can take bayyanawa ?? Oh rabbi ! Kanshi ya daure tamau ahaka suka isa airport xuciyar na suya basu dade ba jirginsu ya tashi fargabarshi ta karu sbd rashin sanin matakin da xata dauka akanshi musamman shi dayake kuntata mata

Cikin dare suka isa direct gidansu na cen suka wuce dakinshi ya zarce yai wanka ya sauya kaya ya bude jakar shi ya dauko laptop din mahboob dan bai mayar mishi ba sbd baya son ya San komai akan Jennifer yafison sai ya ganota Kafin ya tona mata asiri yagama danne dannenshi ya ajjiye laptop din ya kwanta yana kallon rufin dakin girgixa kai yayi hade da futar da iska daga bakinshi ya gyara kwamciyar da yayi ahaka barawo bacci ya kwashe shi

Washe gari suka shirya dady ya wuce wajan meeting shi kuma ya tafi wani company dan cen dady ya turashi yaje sugana da masu companyn kan wani aiki da xasuyi musu a darare yaje atunaninshi kowanne lokaci xata iya kawo masa farmaki yagama duk abinda xaiyi sai yamma ya dawo ya tadda dady agida shima ya dawo

Kwnansu 3 a Dubai har yanxu fargabar Sa bata yankeba dan ko alama basu hadu da ita ba tunaninshi yarinyar ta Sa musu ido tana kallon duk abinda sukeyi tunda duk inda sukaje sai sun ganta tun yana fargabar haduwarsu har ya dake so yake su hadu yasan wacece ita ?? Da daddare suna falo shida dady suna kallon news dady yana yanka lemon bawo yana sha cikin kulawa ya kalli haisam da hnklinshi ke kan tv tunaninshi kuma na cen yadda xasu kare da Jennifer haisam ya waiwayo ya kalli dady naam dady kana lafiya kuwa ? Naga kwana biyu kana yawan tunani kamar kana cikin damuwa gyara xama haisam yayi akan kujera ya kishingida dady bakomai ina lfy katabbata ?? Dady ya tmbyeshi na tabbata dady ya fada yana Sosa gashin kansa OK to haka akeso gobe nake son wucewa Singapore sbd aikin da nafara ina son naje agama shi akan idona kaikuma sai ka tsaya idan companyn cen sungama kaduba kayan ka gani sai ka tura su 9ja xuwa jibi sai ka koma gida to dady Allah ya kaika lafiya amma dady yayi shiru yana kallon wta talla da akeyi a chanal din da suke kallo ina jinka dady ya fda yana kallonshi kallo na kulawa ina son zanje umara zan wuce cen daganan OK to Allah ya kaimu ngd dady murmushi yayi ya cigaba da shan lemon shi yana jin soyayyar yayanshi tamkar hancin cikinsa Wanda inbashi ba rayuwa
Chapter 11 · 0% Book details