← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 84

Sashe 24

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****************
Wasa wasa kullum khaleel ya xauna bashi da aiki sai tunanin yarinyar nan ba yanda baiyi ba ya share ya kasa da kyar akai 1 week da kyar ya samu ya xakulo dabara sbd yaji daxu Momy tana anemo mata Wanda ya iya girki kafin bikin Abu yaxo da yamma ya shirya ya nufi unguwarsu kai tsaye rumfar Maman david yaje bai samu Jennifer anan ba sai Maman david din yatarar ga mamakinsa yana xuwa yaga Maman David da sauri taxo wajanshi dan ta ganeshi sannu da xuwa oga amsawa yayi sannan ya xauna ta gaishe shi da girmamawa ya amsa shima tace me xa a baka yayi Jim ya dago kai kenan ya hango almarai ya dan saki numfashi ya xaro Damin kudin ya mika mata abawa wayen cen almajiran da murna ta amsa bayan ta raba musu duka abinci ta kawo kudin wai sunyi yawa yace ta barshi da murna ta fara gdy ta xauna nesa dashi kadan ta hau surutu ai oga Allah yaska muku da alkairi irin taimakon da kukeyi megidana ma a companyn Ku na takalmi yake gadi ajiyar xuciya khaleel yayi dan yasamo mafita yayi murmushi kadan bakomai akwai mgnr dana keso muyi gyara xama tayi inaji,
Sunana khaleel Dr bashir,
Bude baki tayi da mmk Kaine khaleel ?
Daga mata kai yayi
Momyna tana son Yar aiki wacce xata dinka yi mata girki ko kina da wata hanya daxaki mata naga kin iya girki sosai,
Washe baki tayi cike da murna sosai ma oga khaleel ina da hanya dan ina da y'a Jennifer itama ta iya girki sosai, Hamdala khaleel yayi cike da jin dadi, OK amma kafin nan naga cen gabanku kadan sun bude catering skul ko ? Inaso taje cen tayi training na 3 months kafin tafara aiki dan Momy kafin ta dau mutun tana kai shi catering yai training, jim Maman David tayi dan bata da kudin daxata iya biya mata hakan yakaranta a fuskarta yasa yaxaro damin kudi Wanda yasan yafi na catering din yawa ya mike hade da mika mata gashi aje ayi mata register, ta amsa tana xabga gdy

Wannan shine dalilin zaman Jennifer gidannan kuma tunda taxo na fuskanci tana sona tun ban yarda sonta nake ba har sai da na yaddarwa kaina ta tsunduma son jenny so kuma ba na wasa ba naso na aureta na maida ita cikakkiyar mace ya girgixa kai hade da cije lebenshi sagir kasan banta ba burin soyayya da karamar yarinya ba ? Babban burina shine auren mace wayayyiya wacce at least ace tagama degree dinta tasan rayuwa tasan menene aure, tana da cikakken hnklinta, bani da burin auren yarinyar da komai kai xaka koya mata ciki kuwa harda soyayya batasan yaxatayi ta farnta mk ba kana fishi da ita itama tana fushi da kai, dariya sagir yayi da sauri khaleel ya galla masa harara kaifa dan iskane dariya kakemin ?
Sorry abokina ina mmkin yanda akayi bakasan yaran yanxuba tarr suke ganinka abinda yaran xasuyi wata babbar baxatayi ba, tsaki khaleel yayi baxaka ganeba sagir !
Kayi hkr khaleel
Cije lebe yayi bakasan me nakeji ba Kalmar nan ta hkr da ka fadamin jinayi kamar ka Debi narkak ken ruwan dalma ka xubamin ajikina,
Wani irin xaro ido sagir yayi hade da fadin Allah ya kawo sauki

***************
Dady ya tarasu kaf mutanen gidan a babban falo harda su hindu sulthana da jenny yayi gyran murya yana kallonsu 1 by 1 shikadai yasan wanne irin yanayi yake jin kansa,
Alhamdulillah na tarakune anan dan mu tattauna gagarumar matsalar da muke ciki kan rashin lfyr Jennifer ya kalleta kallo na tausayawa Jennifer ! Yakira sunanta ta amsa kanta akasa mun yanke shawarar xamu auraar dake ga musulmi kan shawo matslarki kin amince ? Gabanta ne yai mummunan faduwa da sauri tace eh jikinta na rawa Hamdala dady yayi sannan ya kwshe yadda sukayi da malan yasanar dasu, kije kiyi tunani Jennifer idan kina da Wanda kikeso Wanda kika yadda da ingancin addininsa nan da xuwa gobe ki fadamin da kyar ta iya bude baki sbd nauyin d yai mata tace toh
Sulthana ce tace dady nima kaimin auren plx ! Da sauri hade da mmk dukansu suka kalleta murmushi dadi yayi sulthana ! Yakira sunanta kiyi hkr itama Jennifer kinji babban dalilin daxaisa ayi auren, dady nima myb in ammin auren matsalata ta yaye ka auramin ya haisam ! Dariya ta subcewa dady ! Ta shagwabe fuska plx dady ina sonshi, ki yi hkr akwai time in dai yana sonki lokaci kuma yayi tsab xan aura miki shi,
A a dady ko baya sona kai mishi auren dole dani, tsawa haisam yai mata baki da kunya ko ? Wani kallo tai masa tunda kasani maimai cin me kk ? so kafasan bani da kunya name xaka tmby ni ita ? Kunya tayi yamma ni nayi kudu tafada hade da murguda masa baki girgixa kai dady yayi cike da tausayinta mace da akasani da kunya ita anxare mata ta ta da karfin sihiri, dady ta katse masa tunaninsa cikin fuskar tausayi ni nasan baxai soni ba ! Sbd bani da kunya ni fitsararriyace amma ina sonshi ni kaina bansan lokacin Dana ke futsara ba ta fashe da kuka me tsuma rai dady inaji dama babuni na tsani kaina kai da Momy ne kadai kukemin kwarjini amma koya kallo daya nake mishi da kaina, cikin matukar tausayawa Momy tace kiyi hkr sulthana kowanne mutun da irin kaddararsa in shaa Allah komai xai wuce kutashi kuje kuyi sallah ankira dukansu suka mike kowa da abinda yake sakawa aransa

***************
Suna kwance karfe 3 na dare sulthana ta tashi ta dauro alwala tana fitowa daga toilet ta kalli yan'uwanta su 2 da jenny da da hindu suna barci hnklinsu kwance wata kiyayyarsu taji me xafin gaske frige ta bude ta dauko ruwa me sanyi ta juye musu shi ajikinsu pirgit suka tashi ganin itace tai musu aikin yasa hindu ta mike a kule ubanwa yasaki ki xubamin ruwa ? Da kallon raini tace ubanwa yasaki ki mike kafa kina barci cikin kwanciyar hnkl kamar baki da wata matsala a rayuwa alhali kin fi ubanwa Iowa matsla kitashi ki fada wa ubangiji bukatanku, da jin haushi hindu tace shine xaki tasheni da ruwan sanyi
Tsaki sulthana tayi ki godewa Allah daba tafashash she bane
Wanka mata mari hindu tayi
Wani kara sulthana tayi hade da kaiwa hindu duka da roban ruwan sanyin data tashesu, takaici ya kama jenny ta fashe da kuka hade da rufesu da duka dukansu suka kacamai da fadan gaske irin Wanda suka farayi daren ranar da suka dawo hotoro karar fadan nasuce ya tashi mutanen gidan dukansu sukayo dakin nasu hnklinsu atashe samun sukayi sun kacame da fada akai akai su rabu suka ki hnklin dady atashe ya kira ya khaleel yana xuwa ya kwatsa musu tsawa suka tsaya da fadan dady hnklinshi atashe yace meya hadaku cikin Daren nan ? Hindu tana haki tace dady wannan shegiyar futsararriyarce muna bacci ta xuba mana ruwan sanyi,
Cikin fada sulthana tace niba shegiya bace, kece dai shegiyar futsarariya,
Jenny ce wawuro center table din dakin kwara na kasheku na huta dan jaraba dadyna yana muku mgn baxaku daina ba,
Da sauri sulthana ta janyo lokar mirror din dakin wllh kina bugamin nima zan buga miki,
aguje hindu ta bude Jakarta ta xaro bindiga ta nunasu da ita wannan shine kuskuren da muka kara yi haduwa waje daya kun manta maganin da boka ya bamu muka xuba akofar wancen gidan bamu xuba anan ba wannnan magnin shiyake rage mana karfin kiyayyar juna nagaji ! Nagaji ! Kwara na kasheku na kashe kaina mu huta ta nuna su da bindiga

By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

51&52

A raxane dady yace hindu ! Menene haka ? Yan 'uwanki ne fa ? Ki ajjiye bindugar nan, ta kalli dady fuskar ta a daure tana xubda hawaye tace, dady baxamu gyaru ba, baxamu ga iyayenmu ba, ka barmu mu mutu mu huta, mutuwa itace kawai hutunmu, cikin fada khaleel yace, ki ajjiye wanann bindigar, kada ki kuskura ki harbesu, girgixa masa kai tayi yaxama dole kodan mu rabaku da wahala, jenny ta harareta ta rike kugu ki harba wayake tsoran baraxanarki ?? Dariya sulthana tayi hawaye na xubar mata amma kafin kiyi Harbin ki duba bulet din kiga xai isheki ?? Tayi tsaki kin San fanko ? To hk bindigar nan take, nida jenny mun kwashe bullet din mun watsa shi a toilet munyi flushing sbd shegiyar baraxanar da kikewa mutane da bindigar, sai ki harba mugani,
Sauke hannunta tayi, ta xauna gefen gado hade da ajjiye bindigar kusa da ita amma kun shammaceni banxaye barayi,
Jenny tace abinda kikeyi ne mukai miki, dan kece cikakkiyar barauniya,
Dady da sauran yan gidan kallonsu kawai suke suna mmkin wannan ikon Allah, sun fara cacar baki ya katsesu,
Tunda abin yxama haka zan raba muku wajan kwanciya xuwa gobe amma kafin nan ke hindu jeki dakin zahra ke kuma sulthana kije dakin rubayya,
Cikin shagwaba sulthana tace a dady ni dai dakin waccen me ji da kan xani ta nuna xahra naga tunda muka xo gidan nan take wani fusge fusge a dakin ki nakeso na kwana kikai min wani rashin kyautawa na miki dukan tsiya dan bani da mutunci, ta gallawa xahran harara, tsaki xahran tayi, tayi gaba kafin dady yayi mgn sulthana tabi bayanta, dady yace sulthana axauna lfy plx,
tace to dady karka damu,
Ajiyar xuciya dady yayi yabi bayansu da kallo Rubayya tace hindu, xo muje suka tafi aka watse akabar jenny ta rufe dakin ta rungume filow tana tausayawa rayuwarsu bata da buri arayuwarta yanxu irin ta musulunta taga iyayenta hawaye ya sauko mata ta runtse ido Allah ka kawo mana agaji Allah ka cikamin wannan burin nawa tasa kanta jikin filow yanda taga rana haka ta karashe daren bata runtsa ba

****************
Washe gari da safe misalin 11:00 malan ya kawo musu magunguna na karya sihiri kowanne iri Wanda shari'ah ta yadda dashi ya fada musu yanda xasu dinka amfani dashi dukansu amma banda jenny dake suma abin ya ishesu yana kawowa suka fara amfani dasu babban burinsu shine suga iyayensu
Chapter 24 · 0% Book details