← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 84

Sashe 63

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

bayan ta shirya ta fito tana d'ingishi tanufi falo hangoshi tayi xaune kusa da breakfast d'insu mmk ya bata ta k'araso ta xauna nesa dashi.
taso ta bashi dariya ganin yanda take kunbure kunbure bai tuntsira ba amma sai da murmushi ya sub'ce masa.
kusa da ita ya janyo breakfast d'in ya xuba mata abincin da yai musu mmk sosai ya bata dama ya iya girki irin haka ?kamar tayi mgn ta waske dan haushinsa takeji.
"barka da tashi beautyna"
kamar baxata yi mgn ba da kyar tace,
"yawwa"
motsin bakinta kawai ya kalla yasan abinda tace dan muryarta bata fito ba.
d'eban breakfast d'in tayi tana ci tmkr bata son ci.
tsura mata ido yayi cike da birgewa tsakanin daren jiya xuwa yanxu shi kad'ai yasan yanda yakeji game da ita.
ganin tak'i cin abincin da d'an yawa yace,
"plx beautyna kada ki wahalar min dakanki ki ci abincin nan"
k'uluwa tayi aranta tace wahala ta wuce wacce kaimin jiya)
ya girgixa kai yayi kwata kwata ta canza masa wani yanayi narashin jin dad'i yaji shi ciki.
ya matso kusa da ita ya rik'o hannunta
"narasa wacce kalar mgn zan fad'a miki bansan irin adadin gdyr da zan miki ba bani da abinda zan biyaki dan kin fi k'arfin duk wata kyauta da zan miki,
ya girgixa kai yana jin tabbacin hakan.
"kin fi k'arfin komai dan kin min abinda baxan iya miki komai ba sai kyakkyawar addu'a ita kad'aice xata biyaki tsare min kanki da kikayi"
ya lumshe ido ya janyo ta jikinsa taso ta kwace ta kasa dan baya mata rik'on rago rik'eta yake gam ajikinsa tamkar wanda xa'a kwace masa ita.
"kin min hidimar da addu'a ce kawai kyautarki da kuma rayuwa ta kin samu wani babban matsayi wanda banyi tunanin shiba kin xama sirrina kinsamu wani matsayi da mutuncin wanda har abada baxasu gushe ba duk lokacin dana kalleki ina ganin matsayinki da mutuncinki kwance akan fuskarki,
narasa dame zan saka miki?
na baki kaina rayuwata bani da wani sirri bayan ke jannah ! ban san ta inda zan fara miki bayani ba dan kin wuce duk iya abinda zan iya fad'a"
tausayin shi lokaci d'aya ya kamata haka ya dink'a fad'a mata manya manyan sirrikansa da fad'a mata duk wasu abubuwa daya mallaka yakuma sheda mata da sunxama mallakinsu tare shida ita.
lif tayi ajikinsa idonta a rufe tana jin k'aunar mijinta tuni ta nemi jin haushin tarasa sbd sassanyan magangun da yai mata way'anda suka kashe mata jiki sosai

yinin ranar haka ya hanata komai wai baya son ta hawala shi yai musu girkin lunch abincin ma abaki ya batashi bai son tawahala ko kad'an shi xai mata komai tun tana mmkin wai yau khaleel d'in data sani mai miskilanci shine yake ta mata wannan rawar k'afar da hidimta mata har ta daina mmkin dan abin nashi sai da ya wuce tunani fur yak'i xuwa wajan meeting d'inshi da president wayoyinsa ma kashewa yayi da kyar da nuna masa b'acin ranta sosai ya tafi cikakken awa biyu baiyi ba ya dawo wai shi baxai iya wuce 2 hours baiji d'uminta ba hakanma da kyar ya jure bai son abinda xai hanashi jin k'amshin jikinta.

i dedicated dis fage to u Jameela Muhammad Ali (maman bobo)
[2/28, 6:44 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

99&100
*Ummee Garkuwa*
Ko wa ranshi cike da farin ciki, tun ba haisam ba kaman ta nitse
kafin wani lokaci sun shak'u da junansu sbd xaman waje d'aya musamman Alhaji Adam ya maida y'ay'an dady dana Abbu harda na papa tamkar nashi duk abinda xaiyi sai yai shawara da dady kasancewar gidan babban gida ne duk yamma suna xama a gerden wanda wajan yake tamkar falo grass ne tsararru sukayi k'awanya awajan cen gefe fulowowi ne masu shegen kyau kala kala ga kukan tsuntsaye way'anda suke a wajan suka taimaka wajan k'awat gerden d'in duk yamma suna zama dukansu suyi hira suku ma tattauna abinda ya dace wajan matan ya nesanta da wajan da mazan suke zama abin gwanin ban sha'awah sai wanda ya gani

Saturday
tun da wuri ya khaleel ya shirya xuwa abuja taron da xai wakilci Abba sam xuciyar shi ba dad'i sbd baya son barin jannat bashi da yadda xaiyi ranshi ab'ace yake,

tana xaune a d'aki tayi jugum tana tunanin tafiyar da ya khaleel xaiyi a yau tausayinsa takeji ita kanta tana jin ba dad'i bata da yadda xatayi hjy murja ce ta shigo ganin tayi jigum yasa ta ware ido cike da mmk take kallonta,
"jannat baki shirya bane tun d'axu ?
da mmk take kallon hjy murja ta girgixa kai,
"to tashi maza ki shirya kina nufin shi kad'ai xai tafi ne ? tashi ki shirya ku tafi"
ajiyar xuciya tayi wani mugun dad'i ya xiyarceta ta nok'e kanta ak'asa kunya ta hanata tashi,
ganin bata da niyyar tashi yasa hjy murja tak'ara sa wajan kayanta ta janyo k'aramar akwati ta d'ebi kayanta ta xuba ta naimi duk wasu abubuwa da ake buk'ata ta xuba ta waiwayo tana kallonta,
"tun kafin rai na ya b'aci tashi ki shirya"
ganin ba wasa a fuskarta yasa ta mik'e ta canza kaya tunda bata dad'e da fitowa daga wanka ba batayi makeup ba mai kawai ta shafa da powder rik'o hannunta hjy murja tayi suka fito daga d'akin a babban falo suka tadda mutanen gidan cike da rashin fahimta suke kallon hjy murja da jannat da kanta ya ke a k'asa,
Abba ya kallesu yayi murmushi yasan murja akwai kula da yaran nan musamman akan abinda suke so,
hajiyarmu ce tace
"toh ina xuwa haka jannat ?da sauri hjy murja tace,
"hajiyarmu xasu tafi abuja ne ita da mijinta"
"oh hakane fa ubangiji Allah ya kiyaye hanya"
momy da dady murmushi sukayi suna jinjina kirki da kula irin na hjy murja hjy Nabila ma murmushin tayi tana jin dad'in kulawar murja akanta da y'ay'anta shiyasa take kara tunda tasan duk wata kulawa suna samu daga wajanta
waje suka fito tare da mutanen gida suka tsaya dai dai wajan da motar da xata kaisu airport

ranshi a b'ace ya fito daga b'angarensa hangosu yayi tsaye bakin motar daxata kaishi airport ya k'araso had'e da k'irk'iro yak'en dole Abba yace,
"yauwa khaleel ka fito ?
"eh Abba na shirya"
"ok toh ga security nan xasu bika sbd su baku tsaro yanda na fad'a maka dai haka xakayi ubangji Allah ya karemin ku ya dawo da ku lfy"
duka mutanen wajan suka amsa da "amin"
ya shiga mota idonshi akanta yana tuna adadin missing d'inta da xaiyi bai gama rufe k'ofa ba yaga hjy murja ta bud'e mata k'ofar motar ta shigo ciki a kunyace,
murmushi ya kufce masa tuni ya nemi b'acin ransa ya rasa da murna ya kalleta sam ya manta iyayensu na gefe suna kallonsu,
"beautyna zaki min rakiya ko ?
kyafta masa ido tayi, ina murna ta hanashi kula,
"Alhmdllh naji dad'i sosai da wannan rakiya" dai dai lokacin da driver yaja motar su hjy suna musu addu'ar Allah ya tsare,
suna fita daga gidan ya janyota jikinsa yana kallonta itama kallonshi take da murmushi a fuskarta
"harna fara tunanin halin da zan kasance na rashinki kusa dani"
far tayi da ido,
"ni kaina na shiga wani yanayi na rashinka da zanyi"
"wow!"
ya rungomata sosai yana murmushi mai sauti,
da sauri ta kufce jikinta had'e da xare ido kallonta yayi da rashin fahimta da ido ta nuna masa bafa suka d'ai bane a motar tab'e baki yayi ya janyo ta jikinshi a kunnanta ya rad'a mata,
"ina ruwa na dashi babu wanda xai hanani shak'ar k'amshin matata mai dad'i"
marairaicewa tayi shafa lip dinta yayi ya girgixama mata kai
"kiyi hkr baxan iya xama kusa dake ban jiki ajikina ba"
ta kalleshi ya kashe mata ido d'aya

a haka sukaje airport basu b'ata lokaci ba suka hau jirgi yana rungume da ita har suka isa Abuja tare da security d'in da aka had'asu kai tsaye gidan Abba na cen suka tafi dan anan yace su xauna shi kanshi gidan xagaye yake da security jinjina kai khaleel yayi yana tausayin Abba gaba d'ayan shi arikice yake axxaluman mutanen nan sun rikita shi bashi da kwanciyar hnkl ko kad'an
Chapter 63 · 0% Book details