← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 84

Sashe 32

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru sukayi kowacce da abinda take sak'awa aranta,
Abin ya matuk'ar d'aure musu kai,
Sulthana ce tak'atse shirun,
Y'an uwa menene abinyi ? Abin nan ya bani mmk ni sam ban yadda da maganar wannan mai k'asumbar ba,
Hindu ta kalleta nasan osasa abokin mariki nane na yadda da abinda yace sosai sbd nasan wanene shi,
Ajiyar xuciya, tayi kudin daya nema ne bamu dasu ko Rabin su ma ni banda shi,
Ni abin ya isheni wllh, takarasa maganar da hawaye,
Gyda kai sulthana tayi kiyi hkr sis hindu ko mai yayi xafi maganinshi Allah ni kaina narasa me yake min dadi nakuma rasa mafita,
Sukayi shiru dukansu xuciyar kowacce tana kuna hade da sakawa da warware wa basu da mafita basu da yadda xasuyi,
Jannat ce ta katse shirun da sukayi,
Mudage da addu,a mu cigaba da fadawa ubangiji Allah yana kallon kowa yana kallon xuciyar kowa Allah ya kawo mana dauki Allah ya baiyanar mana da iayayenmu, dukansu suka amsa da amin,
Hindu tace plx sulthana kada ki fadwa kowa xancen nan, koda kuwa dady ne ko Momy
Da sauri ta kalleta sbd me ?girgixa kai tayi muyi tunani plx, bayin Allah nan suna iya bakin kokarinsu wajan taimakon mu da kyautata mana kada mu k'uresu, kud'in da osasa yafada sunyi yawa, mubar abin iyakarmu tunda mu ya shafa,
Sulthana tace gaskiya sunyi mana taimako sosai sun maida mu yayansu sun d'auki damuwarmu sun maida ita tasu wannan kam dole mu b'oye,
Jannat tace hakane sis idan suka san zancen d'aga hnklinsu xasuyi, akan xasu bashi kud'in kuma sunyi yawa, addau itace mafita Allah yaka womana k'arshen wanann masifar,
Ku tashi mu shirya kada dare yai mana asanyaye suka mik'e kowacce tana jin d'aci aranta ta na kuma d'okin sanin suwaye iyayensu haka suka gama kwashe kayan babu wacce taiwa wata mgn acikinsu akan haryarsu ta komawa ma haka sukayi xugum babu hirar kirki sai sak'e sak'en xuciya,

Gab da magruba suka dawo gida jikinsu asanyaye alwala suka dauro sukayi sallah jannat ta dad'e tana xuba addu,a akan Allah ya kawo musu mafita, bayan ta idar da sallah tayi jigum ad'aki tana tune tunane har akayi isha'i ta mik'e ta yi sallah had'e da yin adduar data saba tana idarwa ta kishingida bacci ya fara daukanta k'arar wayanta ne ya tasheta, tana dubawa taga Mr coffee ne tasan abinci yake jira takai masa kafin ta daga wayar ta katse da ta tashi ta tashi kitchen ta d'eba masa abiincin Sa ta had'a masa coffee ta nufu b'angarensa,
Sallama tayi ta shiga yana kishingide jikin kujera yana sanye da 3quater jikinshi ba riga yana kallon labarai kallo daya tai mishi ta kauda kai,
Ajjiye kayan tayi tana kokarin xuba masa coffee,
Ke" ta kalleshi,
Ki cire hijabin,
tarasa meyasa kullum taxo sai ya ce ta cire hijab dinta, ba yadda taso haka ta cire hijab din kanta ba dankwali sai fakin din gashinta da tayi ta xauna, ta dauko cup ta xuba masa ya amsa yana sha tana xuba masa abinci karar wayarshi sukaji da take a bed room dinsa,
Ya kalleta kadan,
" tashi ki dauko min, a hnkl ta mike ta nufi bed room dinshi ya bi bayanta da kallo yana mmkin kyawun dire datake dashi,
Lumshe ido yayi a hnkl ya furta jannah kina da tsari da halitta me Kyau ngd wa Allah daya mallaka min ke,
Ta dawo hannunta rik'e da wayr ta mik'a masa ya xiro hannu xai amsa hannunsu sukayi karo da juna yaji hannun laushi kamar auduga ya amsa ya duba, Jidda ce d'an k'aramin tsaki yaja ya ajjiye wayar,
Mikewa tayi xata sa hijab, ya dago kai yana kallonta,
Muryarshi asanyaye,
"Ina xaki ?? Ta kalleshi suka hada ido,
" daki zan koma,
Xauna muyi mgn,
Xama tayi tana kallon kafet din dakin,
"Daxu ina kikaje ??
Da mmk ta kalleshi,
Hotoro mukaje ban ma je gidan Maman David ba,
" da ixinin wa ?
Xaro ido tayi tana mmk, da ixininka mana, na tambayeka kuma ka mince,
Girgixa kai yayi,
Bana son yawo tafiyar bata da amfani, ni ban San kin tmby niba,
Ranta ya baci ta bata rai, idonshi akan tv yana shan coffee yace baki fadamin xakije hotoro ba, daga yau ma babu inda xaki k'ara xuwa, kina ji ?
Turo baki tayi batare da ta amsa ba,
Waiwayowa yayi yana kallonta ta hada rai ta turo karamin lip dinta, ya tsurawa lip din ido yanda sukai Kyau,
Ajiye cup din yayi ya janyo ta kusa dashi,
"Bakiji abinda nace ba ?
Asanyaye tace,
Naji " sbd ya tsura ta da manyan idanuwansa sannan yana gab da ita hannunta cikin nashi yana murxasu a hankali, ta marairarice tana k'ok'arin fusge hannun, daya hannun nasa yasa yashafa karamin lip dinta,
Ta matsa tana kokarin tashi, ya kalleta,
Ina zaki ?
Turo baki ta kuma yi, daki xani bacci nakeji,
Da hannunshi ya dawo da ita kasa, kamar xatai kuka tace plx ya khaleel ka sakeni.....kafin takai karshe taji bakin ta cikin nashi yana shansu da sauri sauri kamar yana shan alewa, tayi tayi ta kwce kanta ta kasa sbd ya rike ta gam ajikinshi, ya Dade yana shan lip dinta sannan yasaketa hade da tsura mata idanuwa, yana mata kallon yarinya amma tsarin dirinta yana Sa yana jin feeling dinta, ganin ya saketa yasa ta mike da sauri xata fice sam ta manta hijab dinta,
Daukar hijab din yayi hade da mikewa yabita bakin kofa dashi dakyar
Yace, "karbi hijab dinki, ta miko hannu xata amsa ya rike hannun gam tana kokarin fisgewa ya janyo ta jikinshi da karfi kamar xai tura ta cikin cikinshi jinta ajikinshi yasa yai ajiyar xuciya yana jin tamkar ana kara masa soyayyr ta, ahnkl ya xamota daga jikinshi, itakam duk ta rude jikinta sai rawa yakeyi ya kalleta ta sunkuyar da kanta kasa ya dago da fuskar suka kalli juna,
Asanyaye yace mata,
" kifad'i abinda ke ranki?
Da mmk ta kalleshi ta kasa kauda idonta sai da tace masa "me kakeso nace?
Hannunshi biyu yasa ya tallbo fuskarta,
Abinda kike boyewa arnki, ya kalli kirjinta yanda yaga yana bugawa yai ajiyar xuciya baiyi tunanin ta kai haka ba,
Tureshi tayi, sbd jin haushin mgnrsa, da fada tace masa, wanne àbu nake boyewa ?
Cikin ko inkula yace yace, Wanda kikeso,
Runtse ido tayi mgnr ta mata zafi har yanxu yana nan da wannan tunanin ? Dole kam ta sauya Dan taga abin xai wuce gona da iri,
Rike kugu tayi tana kallonshi, ni babu Wanda nakeso babu kuma abinda nake b'oyewa,
Aurenka kuma bani na xab'a ba kusan dolenshi ma akaimin, ta juya ta bude kofa ta fice hade da yi masa Harar sama da k'asa
Wani mugun mmk ne ya kamashi ya xauna yana nanata xancen,
" kusan dole akai mata ?
Gaba daya yaji kanshi wani iri ta bashi mmk baiyi tunanin ta iya tsiwa hakaba,

Da matukar jin haushi ta nufi bangarenta ta kwanta tana mmkin halin khaleel haushin sa sosai ya kamata ta gaji da wannan rainin wayon, kallonta kawai yake bai sonta ba,
Tsaki taja xaka sha mmk na, ta kwanta ranta abace cike da jin haushin shi,

*****************
Washegari da rana suna dakinta inda suka saba zama suwaiba ta shigo sbd tana koyawa jannat karatu, bayan sun gaisa, sulthana ta kalli hannunta da mmk tace suwaiba ina son henna waye yai miki ?
Zama suwaiban tayi tana murmushi ni nayi sulthana, wow ina so kiyi mana nida Anty jannat banda waccen ta nuna hindu Dan ko kin mata ba Kyau zaiyi ba, kin ganta cen duk itace mummunar mu,
Dariya sukayi banda hindu datake hararar sulthana, da dariya suwaiba tace haba duk kamarku daya ni kaina da yanayin shigarku nake tantance ku, Baku da banbanci, bari naje na hado kayan kunshin in dawo,
Bata dade ba ta dawo tai wa sulthana me Kyau sannan ta fara yiwa jannat ana gama mata na hannu wayarta tai kara hindu ta dauka ganin Mr coffee yasa tace jannat waye kuma Mr coffee? lokaci daya sukayi dariya da suwaiba, kar ta katse fa " ajjiye kwai hindu tunda lalle ne a hannuna haka wayar tai ta kara har ta tsinke sai wajan 4:00 tagama musu lallan mai Kyau dake gwana ce suwaiban ta kware sosai yayi Kyau

Toilet tashiga tai wanka kafin ta fito suma sun tafi wankan ta dakko kayan daxata Sa ka English wears ne murmushi tayi da ta kalli kayan yayanta Emanuel ne dayaje jos ya siyo mata su atsaraba satin da xasu shiga wannan wahalar rayuwar bata taba Sa kayanba body hock ce pink me karamin hannu da siket dinta bai karasa sauka kasa ba sun mata Kyau sosai ta tsaya gaban mudubi tana taje kanta bude kofa akayi ta xaci su sulthana ne ganin shi tayi cikin madubin ta hade rai tai kamar bata ganshi ba ya xuba mata ido Hannunshi sanye cikin aljihu,
"Bakiga miscalled dina ba ?
Banxa tayi dashi kamar bata jiba,
Mmkinta yake, bakyaji ina mgn ? Ya fada da fad'a,
Ya b'una fuska tayi mgnr takace bata da amsa,
Kadan yarage yasaki baki sbd mmk,
Mikewa tayi tana gyara xaman siket dinta, ya karewa shigar ta kallo tai mata Kyau ya kalli kirjina gabanshi sai da ya fadi,
Adake yace meyasa baki daga ba ??
Far tayi da ido "sbd bani da abinda zance,
Ta gama kaishi karshe a mmk tambayar kansa ya fara yi dama haka ta iya tsiwa ?
Har ya juya xai fita sai kuma ya dawo hade da fincikota, jikinta na gogan nashi idonta kir akanshi, ki kawo min coffee dakina ina jiranki, fincike jikinta tayi ta kasa sbd bakaramin riko yai mata ba, shiru tayi tana kallonsa, da tsawa yace ko bakiji ba murguda baki tayi, da mmk ya saketa lallai yarinyar nan ta shammaceshi, ta koma nesa dashi, ya fice daga dakin, tayi dariya ta cigaba da taje gashinta, mutun sai kafiya da riqak'k'en ra'ayi taja karamin tsaki
Chapter 32 · 0% Book details