← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 84

Sashe 43

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

11:00 ta tashi taiwa wanka ta saka kaya material ne blue da kwalliyan silver ya karbeta Dan colour din skin tone dintane ta fito babbn falo ta hangosu xaune suna hira dukansu harda Anty Safiyya, yau kam ba umman Jidda da yan'uwanta ta gaishe su suka amsa musamman Anty Safiyya da kulawa take amsa gaisuwar kije kiyi breakfast kada yunwa ta lahantamin y'ata, murmushi jannat tayi ta k'arasa dining tayi breakfast, Momy tace d'auki na yayanku ki kai masa yau ma baifito ba, kunya ta kamata ta d'auka ta fita kanta ak'asa tak'arasa b'angarensa tai sallama tashiga d'akinsa ya fito daga wanka yana d'aure da towel ganinta yasa yasaki murmushi itama murmushin tayi ta sunkuyar da kai ta ajjiye kayan tana gaishe shi ya amsa yana kallon shigarta da tai mata Kyau ya karaso kusa da ita ya janyota jikinshi, yana shinshinar wuyanta yana jin daddad'en savon kamshin dayaji tanayi yarasa gane kalan k'amshin Dan ko ina na jikinta kamshin yakeyi, ya saketa yana mata wani kallo dan yau ganinta yake kamar ba itaba, kanta ta sunkuyar ya dago da fuskar, muje ki shafa min mai, ya janyo hannunta suka shiga bed room dinshi ta shafa masa man tana jin kunya shikam yana so ta saba dashi sosai Dan tarage jin kunyarsa, tana gama shfa masa suka hada ido tai dariya ta juya da sauri xata fice ta waiwayo, ka saka kaya ina jiranka a falo, ya bita da kallon sha'awa yana jin dad'i ya tashi ya shirya cikin shigarsa ta kana nan kaya top yasaka ash colour da blue black jeans ya fito ya sameta remote a hunnunta tana canza channel, ya xauna ta xuba masa breakfast dinsa yana yi yana kallonta yana gamawa, ya mike, tana kallonshi ya janyo hannunta suka koma bed room dinshi, tsoro ya kamata dan lokaci daya taga ya canxa mata janto jikinshi yayi, ahnkl yake mata mgn kamar rad'a, kalamai yake mata da wata iriyar murya dabasan yana da itaba yana shafar jikinta ya xame dankwalin kanta, yannu yasa ya xuge xif din rigarta, gabanta ya fadi ta janye jikinta da karfi,
Ya kalleta da idanuwansa suka fara canxa kala,
No ! No ! Jannat plx nagaji da dauriya, jikinta ya fara karkarwa dan wani irin xaxxafan kiss yake mata cikin wani yanayi, yana maganganu, ina sonki jannat ina son kamshin jikinki, yafara haukata ta da wani Salo na daban tafara mayar masa da martanin kiss din daya ke mata,
kmar ta tunxirashi, ya fara wuce xatonta, tayi tayi ta kwace kanta ta kasa, tasaka masa kuka agigice dolenshi ya hkr dan bayason jin kukan ko kadan haka ya rungumo ta jikinshi yana shafa bayanta tana ajiyar xuciya, ta mike ya kuma rukota, beautyna kada ki rabani da lallausan jikinki plx ya maida ta jikinshi yana jin kamar ya maida ita cikin cikinsa sun dade a hakan da kyar ya kyaleta ta fito tana jin tausayinsa,

Washegari dady ya tarasu a falonshi na sama dan shida kansa yake b'oyewa bayasan rigimammin k'annansa su San abinda yake faruwa, ya kallesu dukansu,
Zantafi Abuja munyi waya da Alhaji Nasir ministern man fetur xamu hadu da President dan shi kadaine mutumin da xai iya ganin Adam ched'e bata re da wani shamaki ba cike da murna suke masa addu'ar Allah ya dawo dashi lfy yaji dad'in yanda yaga sunata nishad'i sosai mahboob ya kaishi airport ya wuce abuja yana tabbatarwa da kansa samun nasara

Yana sauka ya hadu da drivern Alhaji nasir ya kaishi gidansa suka tattauna Dan amininsa ne tare sukayi kuruciya bayan sungama suka tafi wajan President sbd yasan da xuwansu kai tsaye gidanshi suka wuce suka sameshi a falonsa na musamman da yake saukar baki way'anda suke da muhimmanci,
Yana ganinsu ya saki murmushi, Dr bashir rabona dakai shekara shida kenan kullum kana nan a yanda kake, dariya dady yayi yabashi hannu suka gaisa bayan sungama gaisuwa, President ya kuma kallon dady,
Dr bashir meyasa kaki yadda da shawarata? Siyasa ta dace dakai danshi mulki yana neman mutane irinka masu adalci ina fata xuwan nan dakayi kaxone dan ka fada min ka yanke ahawara xaka shiga siyasa Dan ka kwatowa talakawa yancinsu ?
Girgixa kai dady yayi dan sam bai son xancen ya kalli President ba wannan bane ya kawoni ina son wani taimakone,
Da mmk President yake kallonshi yanxu bashir dan kana son abu awajena sai ka kirashi da taimako? Murmushi dady yayi, ina son kai min hanyar da xanga Adamu ched'e
Ajiyar xuciya President yayi yana jinjina kai yai murmushi yana kallon dady,
Ni kaina rabon dana Sa ched'e a idona na manta shima irinkane ba ruwanshi da yan siyasa tsakanin mu dashi idan muntashi kanfen mu kirashi awaya mu tambayeshi kudi ya bamu muyi canfen dashi waya kwai xamuyi yasa aturo mana wani xubin ma ko ka kira wayan yaransa ke d'agawa ganin ched'e ba karamin babban aiki bane yanxu xakaji cen gobe ka jishi acen,

By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

75&76

Bayan yagam a
Mr.president ya kira adamu yace su hadu gobe sa da mmk Momy da dady suke kallonsa dan basu San da xaman Shiba, Jim yayi yana kallon kafet din falon kamar yana naxarin ta inda xai fara fadawa dady inda asalin maganar take ya dago kai ya kalli dady cikin yadda da abinda xaice,
Hindu da yan'uwanta y'ay'an Alhaji ADAM CHED'E ne, dafe kirji Momy tayi cike da kad'uwa da jin sunan mikewa tayi tana kallon sadik osasa tamkar wani tababbe,
Dan karamin tsaki dady yaja yana yiwa sadik mugun kallon ya raina musu wayo, su Kansu su jannat gani suke rainin hnkl ya shigo lamarin, kallonsu osasa yayi ya gyada kai Dan ya fahimci irin kallon da suke masa dady ya bata rai, kaga Malan nifa ba sa'anka bane ba kuma cewa mukayi kaxo kamaidamu sakarkaru ba muna son jin iyayen su jannat shine xaka fadi abinda hnkl baxai dauka ba, idan kai baka da hnkl to nan duk masu hnkl ne,
Ga mmkinsu kwashe wa da dariya osasa yayi, a kufule dady ya mike xai bar falon da sauriv ya tashi ya ruko dady, kayi hkr Alhaji ka xauna, naga yanayin Ku duk ya nuna Baku yarda da abinda na fada muku ba amma ga Hindu cen Ku tmby ta ta sanni tasan ya tsarina da kuma rayuwa ta take ciniki mukayi akan hakan kuma ta biyani, babban abinda na tsana ha'inci banayi ba kuma aimin sannan ni mai adalcine duk da nakasance babban tagadiri, wani mugun kallo da dady ya kuma jifan shi dashi, da mmk ya maimaita mgnr shi, ciniki kukayi kuma anbiyaka ? Ya kalli su Hindu kowacce ta sunkuyar da kanta,
Gyada kai dady yayi fuskarshi a murtuke Dan ya fahimci osasa babban Dan duniya ne, Ina jinka,
Xama osasa yayi akan kujerar da ya xauna tun farko,
Banxo da wasa ba bakuma wasa ko karya ne ya taramu ba xan kuma maimaitawa Ku yarda dani wllh baxan fadi son xuciyata ba domin a dacen mu yaran wacce tasamu aikin nan ne na rike Hindu ta dauki abokina jamus Wanda ya rike Hindu akan tana son ya rike mata ita har karshen rayuwarta, jamus mutun ne mai tausayi shi da kanshi yaso ya d'aukar wa Hindu fansa lokacin dayaga yaxama rikakken D'an daba Wanda duniya take shayi sai kuma hukuma ta cafkeshi baxan iya fad'a muku Wanda yai muku wannan D'an yan aikin ba Dan har gove ina tsoranta sbd tafini hatsabibanci ko shedan haka yaga wannan Mutanen ya kyale amma mahaifinsu shine Alhaji Adam chede, ya mike tsaye aikina ya kare tunda na fad'a muku, dady shima mikewa yayi fuskarshi cike da damuwa,

Ganinshi awajan mu babban aikine domin babu Wanda yasan takamai mai k'asar da yake xaune, girgixa kai osasa yayi manyan mutane irinsu baxa xaune guri daya sbd makiya,
Cire hula dady yayi ni babban yaronsa kawai nasan cinikayya ta taba hadani dashi,
Murmushi osasa yayi zan baka wata muhimmiyar shawara kada Ku fadawa kowa wannan xancen kada kowa yasan dashi ciki kuwa harda su Kansu dangin cheden Dan kowa munafiki ne, da mmk dady ya kalleshi, gyada masa kai osasa yayi tabbas mutun biyu xan Baku shawara akan duk rintsi da su xakuyi mgnr daga Adam ched'e Sai uwargidansa hjy Nabila ched'e
Ya juya Alhaji ka kiyaye kayi ta katsantsan kuskure data xakayi akan yaran nan kashiga cikin masifa,
Mmk ya hana dady mgn,
D'age kai osasa yayi, idan da akwai abinda yafi masifa ma xa a iya jefa ka ciki muddin mak'iyan yarannan suka gano suna cikin gidanka ka kara kiyayewa sannan Ku kuma Ku kiyaye fita barkatai, Allah ya baku sa'a ni dai in kunyi sa'ar ganinsu plx kada Ku manta dani Ku taimakamin da muk'amin koda masinjan ched'e dan nasan na haye, ya karashe maganar dai dai lokacin daxai fita, dukansu suka bishi da kallo,
Jigum sukayi kowanne da irin tunanin daya keyi,
Sulthana ce ta katse shirun,
Dady ina jin sunan nan Adam ched'e ko ched'e family suwaye su hk ?
Kallonta dady yayi shi kam jinsa yake wani iri ya kauda Kansa yana kallon labulan falon,
Chapter 43 · 0% Book details