← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 84

Sashe 76

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wasa wasa yau kwana 4 da b'atan ya khaleel jannat ta rame tayi bak'i kullum cikin axabar kuka take rabon da taci abinci har ta manta data xauna bata da mgn sai sambatu tana sambatun tana kuka tun suna tausayin kansu har sai da suka dawo suna tausayin yanayin data ke ci wanka wannan sai an takura mata takeyin shi bata iya komai data xauna xai sambatu kala kala mai rausayi baxai iya jure sauraronta ba.

yau ma dakyar hjy murja ta tursasata akan ta shiga toilet tayi wanka da kyar ta shiga tana jinjina abin aranta sam baxasu gane bak'in cikin data ke shiga muddin ta ganta a toilet abubuwa da dama take tunawa rayuwar ta da khaleel ta kalli hand shower data ke hannunta ta tuno lokacin da suke wanka
"beautyna da kaina xan miki wanka bana son ki fiya motsi da yawa kada ki bige min ajiyata....."
kuka tasaki sosai had'e da tsuruwa hand shower d'in ido.
kullum suka shiga toilet sai ya jik'ata da ita
tana dariya yana dariya suna facing facing da ita
surutu ta fara yi had'e da kuka mai tsuma rai a toilet d'in
"kin san inda ya khaleel yake ?
kin san halin daya ke ciki ?
suwaye suka rabani da shi ? sun rabani da rayuwa ta tayaya xan rayu bana tare da ruhina ? wacce irin rayuwa xanyi xuciyata bata gangan jikina ?
meyasa kuka rabani da shi ? kina kallo suka rabani da rayuwa ta ? meyasa baki hana ba ? "
kuka sosai takeyi ne had'e da gunji.
"kada kici amanar shi kin manta shine ? kullum kina hannunsa yana ji k'ani da ruwan da kike xubarwa ? kece kika sace min shi ? ni ma kisace ni ! muguwa !! " tai cilli da hand shower d'in tana dukan jikin bangom toilet d'in ta kwara ruwa ajikinta tana murxa soso stiil surutan takeyi tana kallan kumfan hannunta
babu abinda ta tuno sai wasan kunfan da sukeyi ya shafa mata ta shafa masa
kuka ta saki na axaba xuciyar ta na tuk'ik'i
" beautyna kunfa taiwa kyakkyawan jikinki kyau tamkar sbd ke akayi ta, ina sonki jannah ! ko mai kikayi kyau yake miki......"""
ihu tasa
"wayyyyo ! baxanyi wankanba wllh baxan k'arayi ba muddin babu ya khaleel d'ina rayuwar ma baxan rayuwa ba xan
kashe kaina ! ina ya khaleel kaxo kaga kumfa ajikina !! nafi k'aunar mutuwa da wannan rayuwar da bansan inda khaleel yake ba"..
afusace ta kwara ruwa ajikinta garin rarume ta k'ume kanta abango kan yai k'ara nan da nan ya d'aure taji kamar an buga mata k'arfe.

axabar datake ciki tafi wannan bigewar surutu takeyi tana ganin juwa na rashin cin abinci ga kanta yai mugun nauyi ga axabar da xuciyar ta take mata tuni ta fara layi komai juya mata yake
" kana ina ya khaleel kaxo ka ga beautynka jiya ka fad'amin amafarki xaka xo yau meyasa baka xo ba ? kataho ! kasan baxan rayu ba bana tare da kai ? waye ya rabani da kai wanne mugun ne !!? sai na kashe shi ! na kashe kaina na kashe kaina !" ta fashe da kuka tana girgixa kai ta finciko rigarta tana k'ok'arin sakawa tsurawa rigar ido rayi tana gunji na axaba
"jannah ! wannan rigar ina son na ganki da ita a kyakkyawan jikinki kada ki sakata dan banso ki wahala" yasaka mata ita.
wulli tayi da rigar tana nunata da hannu
"harda had'in bakinki ? kada ki cuceni khaleel na sonki ajikina !" ........
runtse idonta tayi tasa rigar ta fito daga toilet d'in ta dawo falo ta xauna ta kalli sallayar dayake sallah ta kalli jama'ar falon

"momy ku dawo min da khaleel ! kunga sallayar sa ! idan na kalleta ina jin kamar zan ganshi ..."

kuka hindu tasa ita da hjy murja
"jannat kiyi hkr dan Allah kina jefa mu cikin axabar bak'in ciki" ta mik'a mata carbi "karb'i kiyi ta salati xuciyar ki ta sanyaya"
karb'ar carbin tayi
ta kece da kuka
"ya khaleel ne ya bani carbin nan da hannunsa yace na dinka xikiri gashi kin mik'omin shi sbd rashinsa,
ku tai makamin ku nemo minshi wllh idan ban ganshi ba sai na kashe kaina ! ..... wayyo ! innalillahi Allah kadawo min da khaleel ! mama meyasa xasu rabani da shi ? ki basu hkr kice nace su kyaleshi ni su kashe ni ! nasan sbd dani xasu axabtar min dashi .... momy ki dawo min da khaleel rubayya kinsan me nakeji ? ki daina kuka ki dawo min da khaleel zahra ! kin san gobarar xuciya ? xuciyat tayi gofara idan ba khaleel bani da sauran numfashi mutuwa xanyi ! hindu ki d'auko bindigar ki ki kashe ni! idan baku kashe ni ba zan haukace baxan iya yin shiru ba bansan hakana ke ba ! ku daina kuka ! kashe ni kawai xakuyi shine gatan da xakuyi min wayyyyo innalillahi wa inna ilaihi raji'unnn haka axabar xuciya yake wllh baxa ku gane me nakeji ba !""......

kuka dukansu sukeyi mai had'e da gunji
ta girgixa kai axababben hawaye na sauka
"sulthana ina muka b'oye bindigar hindu ? d'auko ta plx ! "....

cikin kuka sulthana tace
"anty jannat surutun nan naki yana axabtar da xuciyar mu kiyi hkr ki bari surutun ki yana mana illah axuciya ki bari bansan inda take ba !" ta k'arasa da wani irin kuka..
da kukan axaba jannat tace
"k'arya kike sulthana kin san inda bindigar hindu take mu muka b'oye ta,
momy bindigar tana gida a d'auko ta na harbi kaina ....."

ta shi tayi tsaye da sauri hjy murja ta rik'eta tayi wani mummunan murmushi
"mama kada ki rik'eni ki bari na fita na nemo ya khaleel idan ba haka ba zan mutu da axaban rashin ganinsa,
na tsani kaina bani da amfani "...... kanta na juyawa bibbiyu take kallon kowa
"sbd jin dad'i kun koma bibbiyu kowa ya xama iri biyu amma sbd bakwa son farin cikina sai kuka mai dashi d'aya ni ko shi d'ayan ne kubani shi ahaka mu rayu ...."""" kuka me cusa axaba takeyi tana k'ok'arin kwace kanta daga hannun hjy murja bayan ta fincike tayi luuuu ta k'ume da center table ta gangara wajan kujera kanta ya k'ara k'umuwa.
gaba d'aynsu suka sa kuka sukayo kanta tana k'ok'arin tashi ta sume a hannun hjy murja jini na fita akanta wulli hajiyarmu tayi da sandar ta tararu mosu ita da hjy murjan tana wani irin kuka
"jannat na shiga uku ni zainab naga axabar rayuwa ! "
suna k'ok'arin fita da ita suna rusa kuka mahboob ya shigo arikice yana mgn yana fidda uban haki
" ga khaleel can an yasar mana dashi a k'ofar gida ko ina na jikinsa sarane ! "
da gudu suka fice suna wani irin kuka sam ! sun manta sun tab'a rayuwar farin ciki.
a sume khaleel d'in yake su dady suna k'ok'arin sa shi amota suka hango matan sun nufu so suna kuka jannat rumgume jikin hjy murja kamar matacciya da kuka suka basu lbrn abinda ya faru suka sata amota suka nufi asibiti

asibitin su wanda suke xuwa sama da shekara 20 suka tafi babban likitan daya ke dubasu ya fito da sauri ya nufi inda aka kai khaleel emergency d'akin k'asa ita kuma jannat tana sama b'angaren mata
hjy murja ta biyo bayan Dr fahat tana kuka tana fad'in
"Dr fahat kai sauri muna buk'atar khaleel ka ceto mana rayuwarsa"...
"kiyi hkr madan xamuyi iya k'ok'arin mu"
ya shiga d'akin ya umarci kowa ya fita
suna fita ya xuge labule bayan ya rufe k'ofa ya d'auko kwalbar allurai guda biyu d'aya mai murfi ja d'aya kuma fara ya dad'e yana naxari ya ajjiye me farin murfi ya bud'e mai jan murfin yasa allura ya xuk'ota ya kalli khaleel dayake asume ya tsikara masa allurar ya mayar da ita aljihunsa yai ajiyar xuciya ya bud'e k'ofar d'akin ya fito ya samesu sunyi jigum jigum cikin kasalalliyar murya me cike da tausayi yace
"nan da 20 mints xaku iya shiga amma bai farfad'o daga suman ba" ya wuce office d'insa

bayan 15 mints suka shiga d'akin yana kwance babu alamun motsi dady yana kallonshi gabansa ya fad'i ya kara kunnansa yaji babu alamun numfshi ya d'aga hannunsa asake gumi me d'umi ya karyo masa yace
"innalillahi wa inna ilaihi raji'unnn khaleel ai yarasu ! "
salati me k'arfi suka saki da gudu hjy murja tai office d'in Dr fahat tana sambatu baya office d'in giftawar shi ta hango a sama d'akin da jannat take ta haw saman tana ihu

jannat ta farfad'o idonta akan dr tana k'ok'arin mgn hjy murja ta shigo tana sambatu
" Dr fahat khaleel ya rasu ! "
da sauri matan suka mik'e arikice cikin mugun yanayi kafin su ankara jannat tayi kukan kura ta bangaje su ta fice a guje suka dafa mata baya sam bata ganin komai ta gangaro daga benan tundaga na farko har na k'arshe tuni ta sume jini mai yawa ya b'alle yana fita ta gabanta cikin mugun yanayi suka kinkimeta dr yace su kaita d'akin da khaleel yake kuka sosai mahboob da haisam suke shi kanshi Abba kukan yake yana surutan baxai yadda ba sai ya d'au mataki su ka kwantar da ita kusa da gadon khaleel Dr fahat yace su fita xai dubata

suna fita ya ciro allurar da yaiwa khaleel itama ya tsira mata ya maida aljihu ya bud'e d'akin ya fito ya samesu duk sun rud'e suna kuka me tsuma xuciya babu me rarrashin wani dr Fahat ya goge gumin fuskarsa ya girgixa kai bakin shi na rawa yace
"kuyi hkr itama ta rasu !"

kuka suka kece dashi kowa na sambatu sulthana muryarta tafi ta kowa d'agawa
"ya xakuyi mana haka anty jannat muna sonku ! nima kashe kaina xanyi wayyyyo ! jannat ki tashi ku rayu "........!!!!!!!!!
Chapter 76 · 0% Book details