← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 84

Sashe 23

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

***********
Malan suka kebe shida dady daya khaleel malan ya jinjina kai Dr bashir ! Yakira sunan dadi, akwai matsala gagaruma makarin sammun jikin yarinyar nan shine ta auri musulmi, gaban dady ya fadi shi kanshi khaleel wani mugun shock yaji girgixa kai malan yayi wani shedanin aljinine ajikin yarinyar nan baxai barta ta karfi shahada ba muddin ta auri musulmi xai kyaleta dan shi baya son aure asalima hana wa yake shiwa ? Dady ya tmby shi aljanin malan ya bashi amsa, dady yace toh malan yarinyar nan ba yata bace shari'ah bata amince da haka ba, a a Dr bashir malan ya katseshi a ina iyayenta suke ? Ba Wanda yasani, sannan lalura ce ta taso muhimmiya da kuma uxiri, xa ajira ne har sai anga iyayenta sannan xa a fiddata daga cikin duhu ?, in dai yarinya ta amince magana tayi sannan su marinka ba musulmai bane amma dole xa a fada musu ajiyar xuciya dady yayi, yana jinjina lamarin khaleel kuwa tuni gumi ya jikeshi sharkaf, malan yace muddin kana da Wanda ka yadda dashi da kuma addiminsa da tarbiyyarsa a daura mata aure dashi, hakane malan ina dasu dan naga tasu taxo daya da mahboob Dana ba matsala na hadata dashi danna San baxata kiba hamdala malan yayi Allah yaska da alkairi Dr bashir kayi jihadi Allah ya biyaka murmushi dady yayi bakomai da na kowa ne shikam khaleel suman xaune yayi wani abu yaji me dafi da xafin gaske ya sokeshi da karfi jin an ambaci mahboob xa a. Bawa jennyn Sa 😭😭😭😭

By
*Ummee Garkuwa*
F[truncated by WhatsApp]
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

49&50

Girjin shi yaji yana xafin gaske tamkar ana babba ka masa wuta numfashinshi da kyar ya ke iya saita shi,
Malan ya cigaba da cewa, Dr bashir na jijina maka irinku mu keso Ku yawaita aduniya masu taimako dan Allah, masu jajircewa akan d'a koba nasu bane Allah ne kawai xai biyaka da mafificin alkairi bakomai malan shi d'a na kowane baxaka ki mutum ba koda yaka sance ba addininku daya ba, sbd bakasan gaba, malan ya mike xan wuce Dr duk yadda ake ciki muyi waya, amma maganar auren nan in son samune kada ya wuce satin nan, murmushi dady yayi cikin gwarin gwiwa bakomai malan ko gobene ashirye muke,
Shima malan murmushin yayi hakane Dr Allah yasanya alkairi, ka tamvy ta bakin yarinyar ko tana da abinda xatace, insha Allah xanyi haka nagd sosai, malan ya tafi yana zabgawa dady addu'a ta samun rahama,
Saukar da numfashi dady yayi ya kalli khaleel,
khaleel ? Yakira sunanshi, khaleel ya kuma maimaitawa a tsorace yata bashi hade da girgixashi khaleel ! Da kyar ya iya bude ido ya kalli dady, cikin raxana dady yace meya sameka ? Kirjina dady yana min xafi ina jin xuciyata kamar xata fito, subhanallah khaleel ! Sbd me ? Yanxu yanxu fa lfyr ka kalau, mikewa khaleel din yayi tamkar xai fadi dady natafi daki zansha mgn da kyar ya iya mgnr,
Dady binshi yayi da ido yana mmkin ciwon nashi yanxu yanxu ace ana tunanin xuciya kamar xata fito ya salam ! Meya sami yaron nan farat daya haka ?? Haka ya cigaba da tunane tunane ko xai danko dalilin cutar babban nasa daya keso tamkr namaa tsoka daya a miya

*************
Kai tsaye dakinshi ya wuce shi kadai yasan yadda ykeji aransa abude ya tadda dakin ya shiga ciki a wahalce ya xauna kan 3 siter dinshi sai da ya xauna sosai sannan ya kula da sagir daye xaune yana kallonshi,
Sagir ! Yakira sunanshi, ya cije lebenshi xan rasa jenny ta,
Xaro ido sagir yayi, cike da mmk yace ban fahimta ba khaleel, da kyar khaleel ya bude baki cikin wani mugun yanayi na bakin ciki da bacin rai,
Dady xai bawa mahboob auren ta,
Subhanallah ! Sagir yace sbd me ? Ya tmby khaleel din daya runtse ido yanajin kansa kamar ana cakamasa kibiya, sbd yace tasu tafi xuwa daya,
Da mmk sagir yace to khaleel yanxu meye abinyi hnklina yatashi nikaina bana so karsa jenny, tsaki sagir yayi duk kai ka janyo wannan tashin hnklin taurin kanka ne yajamaka,
Kwfa khaleel yayi bana son fda plx kabarni naji da abinda nakeji shi kadai ya isheni, idan narasa jenny narasa dukkan farin ciki na rayuwata bana jin xanyi aure, dan konayi wacce na aura baxata taba jin dadin xama dani ba, kallonshi kawai sagir yakeyi dan ya kasa mgn, ina son jenny naso na aureta na reneta na bata ilimi ta goge da rayuwa har xuwa lokacin daxata mallaki hnklin kanta yanda xata iya rayuwar aure dani, da inaji ajikina jenny ta wace, yanxu tana so tafi karfina tayaya dady xai gane jenny itace mahadi na farin cikin rayuwata ? Dafe kansa yayi cikin mayuwancin hali har abada bazan daina son jenny ba,itace macen dana kalleta yanayi na sauya ita kadaice macen dana fara so har nake tunanin rayuwar aure da ita sagir kasan ya akayi jasan Jennifer?
Girgixa kai sagir din yayi,
Kwanciya khaleel yayi hade da tsirawa cillin din dakinsa ido

Ranar lahadi ne da yamma Momy ta ce ya kai wata abu Yar aikinsu kasuwa xatai mata siyayya bayan sunje yai parking dai dai bakin kasuwa wajan kofar gidansu inda mamansu take sai da abinci yana xaune cikin mota ya hango baban avokinsa da ya rasu xaune cikin rumfan murmushi khaleel yayi dan mutumin yana da matukar kirki tun suna yara abokin nasu ya rasu amma khaleel bai manta da shi ba dan yana xuwa gaishe ahi lokaci xuwa lokaci futawa yai daga cikin motar yana sanye da wando 3 quarter da riga maroon ta dan kamashi kadan hannun shi rike da mukullin mota yayo rumfar wajan Baban abokinsa ganinshi yasa mutumin yin dariya hade da fadin sunanshi, khaleel d'ana kana duniya ? Dariya shima khaleel din yayi hade da sunkuyawa baba barka da yammaci,
Yawwa khaleel tashi ga benci nan xauna ya gida ya aiki ya iyayen naka? Mikewa yayi ya xaune hade da fadin suna nan lafiya baba,
Mashaa Allah khaleel har yanxu dai ba iyali ko ?
Kai khaleel ya sunkuyar hade da murmushi ankusa baba,
Af kullum amsar kenan ankusa ba, to ubangiji Allah yasa,
Khaleel ya amsa da amin
Shiru Baban yayi, duk lokacin Dana kalleka sai na tuna da khamis, Ubangiji Allah yaji kanshi da rahma,
Amin baba,
Karasowa tayi tai musu sallama suka amsa kan khaleel akasa bai kalleta ba ta mikawa baba plate na abincin daya siya ta juya xata tafi baba ya kirata, Jennifer xo ki tambayi khaleel me yakeso? Dago kansa khaleel yayi suka hada ido gabanshi yaji ya fadi da karfi wani abu yaji yam tundaga kansa har dan yatsan kafansa da sauri ya sunkuyar da kanshi muryarta yaji me matukar dadi, me xa'a kawo maka ? Girgixa mata kai yayi hade da kara kallonta mmk sosai abin yabashi ganinta yayi adire kyakkyawa Sam batayi kala da sunanta ba aslima shi yafi ganin kamarta da Hausa fulani a hnkl a hnkl gaban nashi ya rage faduwa mmkin kansa yake baba na cin abinci yana mishi hira shi kam hnklinshi nakan sabon sauyin daya samu kansa ciki bai taba kallon mace duk kyanta da tsarinta yaji wannan yanayin yanayi wa mutane kwarjini yau shi akaiwa kwarjini yarinya karama hnkl ya kallo bangaren da take xaune akan benci cikin runfar nesa dasu kadan karantar yanayin da ta ke ciki yayi sbd ya karanci sanin yanayin halayyan dan adam tana da nutsuwa sannan tana cikin damuwa haka kawai yaji tausayinta ya kamashi, kwala kiran sallah akayi, araxane yaga ta kalli inda kiran sallar yake fitowa gaba daya ta bada nutsuwanta akan sauraren kiran sallar mmk sosai ya kama khaleel bai tsure da mmkinta ba sai da suka debi ruwa arumfar tasu shida baba suka fara alwala kura musu ido tayi tana kallon alwalar kana gani kasan alwalar birgeta tayi jinjina kai khaleel yayi ya mike Abu ya hango ta nufosu tagama siyayyar yace ta shiga mota ta jirasu xasuyi sallah xuciyar cike da mmkin yarinyar da kuma tunanin son taimakonta suka shiga masallaci

Bayan sun idar da sallah sun fito shida baba ya kira Jennifer xai biya kudin abincin daya ci da sauri khaleel ya xaro kudi ya tambayeta nawane kudin tace 500 ne ya bata 1k ta tafi kawo masa changy yace ta barshi baba yai gdy shikuma khaleel din ya shiga mota dai dai lokacin da Maman david takara so wajan baba Jennifer tace wai a bar changy? Gyda kai baba yayi bani na biya ba khaleel ne dan gidan Dr bashir na g.r.a xaro ido Maman David tayi, hee ! Baba meyasa baka kirani nayi gaisuwa ba ? A kamfanin babansu fa Baban David yake gadi kamfinsu na takalma ai mutanen kirkine baba, Allah ya saka angode ta wuce tana mmkin ganinshi ana sbd tasan dan manyan mutane ne
Chapter 23 · 0% Book details