← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 84

Sashe 61

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

bayan sun koma gida sunyi wanka gajiya ta sauka wayar jidda tana ta ring tak'i d'agawa jannat ta kalleta ta girgixa kai,
"wai anty jidda meyasa baxaki d'aga ba ?
ya mutsa fuska jiddan tayi had'e da kashewa wayan,
"mtssww anty jannat ko na d'aga takaici kamani xaiyi kun d'auki abun k'arami sam bakusan girman shiba"
gaba d'ayansu kallonta suke,
zahra tace,
"anty jidda ke kika mai dashi babban abu tun farko kin maidashi mai girma "
jannat tace,
"anty jidda mai zai hana ki had'ashi da sarkin iya tsari ?
gaba d'ayansu suka kalli jannat
sulthana tace
"waye kuma sarkin tsari ?
sai da jannat tayi dariya tace,
"mahboob mana"
dariya dukansu sukayi Rubayya tace,
"la la laa anty jannat kin kawo shawara danjuma kam tabbas daya mahboob ya dace kun san shine da tsara mgn musamman in yaga mace"
dukansu dariya suke har jiddan,
"wllh kam hakane anty jannat zan had'asu nasan mahboob bashi da wata matsala"
hjy murja ce ta shigo tana mgn;
"nifa narasa wacece anty a cikinku dukkanku kowa sai naji kuna kiranshi da anty wacece antyn ta gsky ?
jannat da sulthana suka nuna jidda,
jidda da zahra da Rubayya suka nuna jannat,
dariya dukansu sukayi,
hjy murja ta ware ido
"tsakanin jannat da jidda waye anty ?
jidda tace,
"jannat ce anty dan tana auren babban yayanmu kinga umma dole itace anty"
sulthana tace,
"umma kinga itace babbarmu tun farko kinga dole muce mata anty "
rik'e hab'a hjy murja tayi,
"kowa yana da gsky dole ku dink'a kiran junanku da anty " ta kalli hindu datake akwance tana kallonsu bata mgn,
"hindu ga hafiz cen yadamu sai ya ganki nace masa a'ah kin gaji kuma dare tayi sai gobe baku san shi ba ko ?
kai suka d'aga mata suna kallonta,
"k'anina ne uwa da uba duka d'aya lokacin da suka mutu rik'onshi ya dawo hannuna dan shine autanmu da aka bani ke tun kina jinjira kullum kina hannunsa yana sonki yana ji dake yana fad'awa kowa kece matarsa in ya girma"
ya b'una fuska hindu tayi had'e da yak'e,
"bayan an sace ku kullum sai yayi kuka akan yana son ganin hishmar sa da kyar akeyi masa dabara ace an kaiki makarantar jarirai"
tak'ara sa mgnr kamar zatayi kuka,
sulthana tace,
"dole ya damu yana son ganinta ashe matar shi xai gani "tak'ara sa mgnr da dariya k'asa k'asa,
hjy murja mik'ewa tayi,
"sannu sulthana kedai kishi kike tun d'axu dan baice yana son ganinki ba"
ta fice daga d'akin
rubayya tace
"oh hindu da saurayi,
kwafa hindun tayi,
"ni konaje ma ban san me zance masa ba danni wllh ban san abinda ake fad'a awajan zance da namiji ba"
kwashewa sukayi da dariya,
sulthana tace,
"anty hindu dama fa ke ba abinda kika iya kada kidamu ga iyayen soyayya nan anty jannat zata koya miki abinda ake fad'a,
girgixa kai jannat tayi "ke kika sani"

suna xaune a falo dukansu hira suke sosai hirar walimar yau had'e da murnan angama lafiya ya khaleel sai raba ido yake yana kallon agogo ko xai ga fitowar ta shiru shiru har kusan 10;00 kasa jurewa yayi ya mik'e xaije b'angaren su hjy murja ta kalli Abba ta nuna masa da ido ya kalli khaleel dayake gaf da xaifara hawan stairs,
dady ya kalleshi da mmk yace,
"khaleel ina xaka haka dare yayi ?
sosan kanshi ya keyi yana in ina,
"dama...dama.. ina ..son zan duba.. jannat ne..
zaro ido dady yayi,
"kabari sai gobe dare yayi,
Abba yace
"ah 'ah yaje ya ganta jeka khaleel"
juyawa yayi cike da jin kunya ya hau saman momy tace
"oh yaran yanxu sai dai abarsu"
bayan sun gama tattaunawa suka tashi kowanne ya tafi b'angarensa

bayan sati biyu
suna xaune a babban falo wanda suke xama idan xasuyi magana dukansu dady yace,
"alhamdulillah yanxu dai hnkl ya kwanta ina so zanyi mgn akan hidimar khaleel da jidda tunda anyi auren kwara ayi bikin su tare a huta dama abinda yasa ba a yi bikinba tuntuni sbd ina son bincike ne akan sanin iyayensu kuma Allah cikin ikonsa yasa akadace"
Abba yace,
"hakane inaga tunda bikine kawai nan da sati biyu yayi ko ?
ya fad'a yana kallon su dady da Abbu,
dady yace "yayi
tunda suka fara mgnr ya khaleel yake jin dad'i sosai dan dama ya matsu yarasa yadda xaiyi ne,
ya haisam ne yace,
"dady "
dady ya kalleshi,
"ya dai haisam ?
ya sunkuyar dakai cikin in ina
"am...ah.. dama.. naji baka ce nida sulthana ba"
dariya dady yayi,
sulthana kam b'oye fuskarta tayi jikin hjy murja, momy tace
"oh ni firdausi yaran yanxu ba kunya bare karah zamani kenan"
hajiyarmu tace "zamani fa kam in yaxo sai a zamance ai nan duk iyayensa ne idan yaji kunyar mu suwa xai fad'awa damuwar sa ? girgixa kai momy tayi,
dady yace,
"ina zan manta da mgnr aurenka da sulthana ? bayan nasan aranar ne ustaz khaleel xai cashe da rawa?
dariya sukayi suna kallonshi cike da rashin fahimta,
dady ya cigaba da mgn,
"in dai sulthana tana sonka haisam zanfi kowa farin ciki"
ware ido haisam yayi,
"dady kasanfa tana sona"
hajiyarmu tace,
"haba haisam meye na tsorata ?idan batayi ni inayi dan kyakkyawa kamarka ah ina so,
suna dariya hjy murja tace,
"ah'ah kin masa tsufa hajiyarmu shi sulthana yakeso itama tana sonshi"
Abbu ne yai mgn
"toh in dai hakane nasa ranar su ranar tarewar khaleel ayi gaba d'aya "
dad'ine sosai ya kama haisam itakam sulthana sai k'unshe fuska take ajikin hjy murja ammy tace,
" ikon Allah yau Allah ya nunamin ranar da sulthana take jin kunyar had'a ido dani"
yusuf ya xaro ido
"wai basabamba yaya mukarram ka manta? kace anty sulthana baxa ta rigaka aure ba gashi ita xatayi ta barka"
ajiyar xuciya mukarram yayi
"kada kadamu yusuf kajira nan da sati biyun ka gani ina nan akan mgn ta banjan ye ba"
Abbu yace,
"kai dai mukarram akwai kishi"
ammy tace
"yak'ara ta cen da kishin sa ita dai nan da 2 weeks shi kuma ko budurwar ma bashi da ita "
cike da birgewa suke kallonsu,
hajiya Nabila tace,
"kada amatsawa d'ana xai baku mmk ko mukarram?
"yawwa ummey barina dawo kusa dake na samu mai tare min kullum sulthana suke tarewa yau nima ga ummina nan ta shigar min"
suna dariya suna tsokanar junansu, nan dai suka tsaida mgn har bikin haisam da sulthana nan da 2 weeks masu xuwa
[2/28, 6:44 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

*Ummee Garkuwa*
99&100
Chapter 61 · 0% Book details