← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 84

Sashe 40

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da kyar ta iya shiga falo ga mmkinta ba kowa kamar mai sanda ta lallava ta hau sama ta shiga dakinta ta kwanta tayi lamo momy ce ta shigo dakin itada su sulthana da hindu, "jannat xamu fita dasu hindu ki kula da gidan Dan duk sauran suma basa nan, da kyar ta ce to Momy adawo lfy Dan kunyar ta takeji murmushi Momy tayi ta fice
Ajiyar xuciya tayi ta sakko kasa farfajiyar gidan ta xauna tana xama ta hango wata tsuhuwa suna mgn da danjuma ya bude mata get ta shigo tunda jannat ta kalli tsohuwar taji batai mata ba kusa da jannat taxo tai mata sallama ta amsa "Yar nan ina hajiyar take ? Bata nan sunfita
"Fitsari nakeji zan wuce nace bari naxo nan gidan nayi kuma hjyn bata nan
Jannat tace eh ta fita,
Nuna min inda bandakin yake jannat ta nuna mata na tsakar gidan Wanda anan driver da danjuma suke amfani dashi kwata kwata jitayi hnklinta bai kwanta da matar ba, ta ajjiye jakarta jannat ta kalli agogon tsohuwar na gwal ta xaro ido sosai ta bi tsohuwar da kallo har tashiga toilet din bata jima ba ta fito ita kam jannat jikinta tuni ya fara rawa Dan tsoro damma ta hango danjuma yana sallah nesa dasu kadan, takara so kusa da jannat," Yar nan nace Ku yan biyu ne agidan nan ? Da sauri jannat ta girgixa kai a'a ni kadaice tana ganin lokacin da tsohuwar tai ajiyar xuciya da alama taji dadin amsar da ta bata, "to ngd na tafi
Da kyar jannat tace mata to ! Gaba daya ta rude

By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

71&72

a tsorace take kallon matar xuciyarta na cikin firgici har matar ta fice daga gidan kasa komawa cikin gidan tayi sbd firgicin da ta ke ciki meyasa wannan tsohuwar ta tambayeta su yan biyu ne ? tunda take bata tab'aganin wannan tsohuwar ba,gabanta yai mummunan fad'uwa da ta tuno gargad'in sadik osasa akan su kiyaye yawo barkatai sbd har yanxu ba'a daina bibiyar rayuwar su, xumbur ta mike xuciyar ta cike da firgici safa da marwa da farayi a cikin harabar gidan tana jin takaicin kyale matar da tayi da bata cakumeta ba, bacin rai mai tsanani ta tsinci kanta da shi, da sauri ta nufi danjuma axaune ta sameshi yana laxumi tak'arasa muryarta na rawa ta gaishe shi ya amsa yana kallonta dan yaga hnklinta atashe,
danjuma kasan wannan tsohuwar ?
arud'e ya amsamata, a a madan wllh ban santa ba me ya faru ??
a tsorace ta kalleshi hnklinta ya kuma tashi,
meyasa kabarta ta shigo ?
mikewa tsaye yayi yana xare ido,
cemin tayi wajan hjy taxo nace sunfita shine ta ce min waccen ba Jennifer bace nace eh shine tace bari ta baki sako wajan hjyr intaxo a fada mata,
girgixa kai kawai tayi dan bacin rai ya hanata mgn cikin gidan ta wuce ta dafe kai hade da xama akan tyles na harabar gidan cikin wani mugun yanayi ? bataraba dayan biyu tabbas matar nan taxo bincikarsu aikota akayi , su kuwa wanne irin laifi sukayi ake bibiyar rayuwarsa ?
wani axababban hawaye ya sauko mata haka ta dinka jin xubar hawayen kamar fanfo sam takasa tsaida hawayen, daga kanta tayi ta kalli sama cikin xuciyar ta tana addu'a akan Allah ya kawo musu sauki, ya Allah ka tsare bayinka ya Allah ka karemu daga sharrin makiyan mu wayanda muka sani da wanda ba mu sani ba gareka na dogara kuma gareka nake neman taimako ya Allah ka kara tsaremu daga dukkan abinki Allah kada kabawa makiya nasara ya Allah ka rushe mummunan nufinsu akanmu, haka ta dinka jero addu'o'i kala kala tanayi tana xubar da hawaye sam tarasa gane laifin da sukai da ba'ason haduwarsu da iyayensu, tanayi tana girgixa kai sbd abun ya matukar dauri mata kai, haka su momy suka dawo suka tadda ita cikin wannan yanayin, arud'e suke tambayarta, ta kwashe labari ta fad'a musu xama sukai awajan suna mmk da ta ujjibi kansu gaba daya ya daure, kowacce tagumi tayi tana mmkin yadda alamarin yake tafiya arikice da kyar momy tace wai ni way'an nan mutanen way'anne irin axxalumai ne ? dole musa matakan tsaro sosai a gidan nan salati kawai take nanatawa da kanta tashi taje wajan danjuma tai masa gargadi kada ya kuma barin wata tashigo gidannan sannan duk wanda ya tambayeshi jannat yan biyune yace ita kadaice agidan a tsorace ya amsa mata dan shi gani yake kamar ya tafka wani babban kuskure na barin matar ta shigo yai wa momy rantsuwar baxai kuma barin wani ko wata tashigo sai da ixininsa balle ya basu lbrn jannat su ukune, ta dawo ta samesu suna kuka sun rungume juna tausayinsu ya kamata ta dade akansu ba su san taxoba surutai sukeyi na jimamin halin da suke ciki da kyar ta lallashesu sukayi shiru suka koma falo babu wanda ya iya yin lunch aranar duk a tsorace suke, sai yamma dady ya dawo ganinsu cikin jimami yasa ko d'akin shi baije ba ya xauna ya na naxarinsu yasan akwai bak'on al'amarin daya shigo cikin gidan, da kyar momy tace,
alhaji narasa gane laifin daya rannan sukai akeson wulakanta su akeson tarwatsa rayuwarsu,hawaye ya xubo mata koma waye Allah ya isa,
ta kwashe lbr ta fad'a masa xura mata ido yayi cikin mmkin xancen nata,
ya girgixa kai, wannan abin yana matuk'ar bani mmk wannan somin tab'in tonuwar asirin koma waye tabbas asirinsu ya kusa tonuwa, karfin addu'a ne yake fito da wayannan misalan, firdausi makiya basai ka musu komai ba wasu ma basu da dalili xasu ji kawai sun tsaneka bakuma xasu barka haka ba har sai sundinka jifan ka da sharurruka iri iri dana baki dana karkashin kasa kai dai babban burinka Allah yai maka tsari daga sharrinsu, kuyi hkr yayana jarabawa ce bakusan irin baiwar da Allah yai muku ba nan gaba, Allah baya jarabtar mutanen banxa sai na arxiki koma wanda Allah xaiwa wata gagarumar baiwa duk wani k'usa kowani shahararre baya xama haka banxa sai Allah ya jarabceshi ya gwada imaninka gwargwadon imaninka gwargwadon jarabawarka da kuma shahararka,
kuyi hkr kuxuba wa sarautar Allah ido shiru sukayi suna jinshi suka d'ai suka san irin bakin cikin dake cikin rayuwarsu da kyar ya rarrashesu da nasiha suci abinci, cin abincin suke tamkar suna xuba wa cikinsu mgn kowacce ta kagu tasan kanta takuma san wanne irin abu taiwa mutanen nan da suka jefa rayuwarsu a wahala suka hanasu jin dadin duniya,

************
da daddare tana kwance bayan ta idar da sallah shafa'i da wutr tayi lamo kan gadonta xuciyar tana jinta wata iri tmk mad'aci sam bata san shigowarshi ba sbd dogon tunanin da ta tsinci kanta aciki jitayi an rungumota asanyaye ta kalleshi yai mata murmushi kad'an ta kauda kanta hade da ajiyar xuciya da ita kadai tasan tayi ta kwantar da kanta yayi ajikinsa, cikin muryar lallashi yake mata nasiha had'e da lallashi tayi lamo ajikinsa dan dai dai kunnanta yake mata mgnr tana jinshi kuma nasihar tana ratsata sun kai kusan 11:00 na dare yana lallasarta har sai da yaga ta gamsu da nasiharsa dan jikinta yai matuk'ar sanyi haka ya kwantar da ita ajikinsa tamkar yar baby a hnkl a hnkl bacci mai nauyi ya fusgeta,

***********
ganinta tayi cikin wani rami ita dasu sulthana da hindu suna gudu xasu fita daga ramin kag da xasu fita suka ga wannan matar da tagani a mota ta taho da gudu itama daga wani gefe na jikin ramin tana ce musu koxo yayana kuxo na ganku kada a rabani daku saura kiris taxo kusa dasu wasu mutane suka xo wajan fuskokinsu a daure basa iya ganinsu suka biyo su, suka rirrik'esu wasu suka rik'e matar wasu suka rik'e su tana ihu ga mutane birjik amma sunki suxo su cetosu firgit ta farka da sauri ya rungumeta gam ajikinsa tuni gumi ya jiketa fincike jikinta tayi daga nasa tana nishi da ajiyar xuciya wani irin kallo yake mata, beautyna menene? kallonshi tayi idonta cike da hawaye ta girgixa masa kai muryarta na rawa tace, nayi mummunan mafarki, mik'ar da ita yayi shima ya mik'e ya nuna mata agogo 3:59 muje muyi alwala mu fad'awa Allah bukatarmu kiyi addu'a sosai dan haka annabinmu ya koya mana duk lokacin dakayi mummunan mafarkin anfison katashi kayi sallah raka'a biyu kayi addu'a sosai akan Allah yai maka tsari da abin ki na cikin mafarkin ya kuma sadaka da alherinsa dan shi mafarki bushara ce babba, alwala suka d'auro sukayi nafilfili har asuba sannan yabar d'akin nata,
Chapter 40 · 0% Book details