← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 84

Sashe 33

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

******
Ya kalli agogan hannunsa 11:30 ya furxar da huci me yarinyar nan take nufi ? Kodan taga yana hada jikinshi da nata ? Tun kafin magrub yace ta kawo masa coffee har yanxu bai ganta ba ? Dalilin daya Sa baison yarinya kenan dafe kanshi yayi idanfa yayi sake rainashi xatai shi mutun ne da baya son raini shiyasa ko k'annan sa baya wasa dasu xabura yai ya mike ya fice daga dakinshi kai tsaye bangarensu yayi yashiga dakinta tana kwance ta na bacci ya kalli beauty face dinta tayi kyau da baccin, tsura mata idanuwansa yayi yana kallonta, a hnkl ya xame bargon jikinta ya kalli hannunta dayasha lallai mai kyau yashafa hannun sbd yana matukar son lalle motsi tayi ya cire hannunsa ta juya daga kwanciyar ya kalli gashin kanta cikin sha'awa yakai hannu ya shfa kan, xabura tayi ta mike idonta taf cike da bacci ta galla masa harara menene haka ? Hada rai yayi ban sani ba ya mike tsaye, daxu nace ki kawomin coffee meyasa baki kawo ba ? Ya b'una fuska tayi "mantawa nayi ta fada tana gyara kwanciya, jannah ! Ya kira sunanta da tsawa har sai da ta tsorata,me kike nufi ne amarairaice tace kayi hkr plx bacci nakeji,
Mantawa nayi,
" kinga bana son musu ko gardama kina jina ya fada hade da xare ido, na kyaleki sbd yau kika fara kada ki kuskura ki kara maimaitawa, ya fice daga dakin ajiyar xuciya tayi hade da hararan bayansa, idan baxaka canxa ba ya khaleel nima yanxu na fara ta juya ta cigaba da baccinta,

Da safe bayan sunyi breakfast suna hira ga al'adarsu, muryar Jidda taji tayi sallama suka shigo ita da mamanta da gudu zahra ta rungumesu gaban jannat ya fadi tasan wannan xuwan ba alherine ya kawosu ba

By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:42 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

63&64

tabe baki yayi yana jin dadin fitar tata tana ganin ta fice ranta ab'ace taji dadi sosai dama tayi hakanne dan ta bata mata rai ta dago kai suka hda ido ita da shi ta b'ata rai ta sauke kanta a hnkl ta xame kanta daga cinyarsa ta mike ta dauki hijab dinta ta fice kallonta kawai yayi hade da lumshe ido yau kam tabashi mmk yanda ta nuna ta damu dashi

cikin jin dadi ta kai flast din kitcean ta nubo bangaren su afalo ta sameta, ganinta yasa jida ta mike taxo gaf da ita xata wuce ta fisgo hijab dinta, fisge hijab din jannat tayi tana kallonta, hararta tayi mara asali wacce aka watsar da ita a bola, kina gadarar cewa khaleel mijinki ne ? auren na kaddara har aurene baya sonki ba kuma xai taba sonki ba dan ya khaleel yafi karfin ki yar matsiyata mara
asali waya sanima ko shegiya ce, tafiyar ta tayi ta kyaleta tana jifan ta da maganganu na cin xarafi daki ta shige xama tayi akan gado xuciyar ta na kunan maganganun da jidda ta yaba mata hawaye masu daci suka xubo mata cikin kuka take magana, dan kawai Allah ya jarabcemu shine muka xama abin gori ,meyasa mutane basa gane kaddara? sun manta Allah shiyake tsarawa bawa rayuwa ba ba bawane yake tsarawa kansa ba ?? hannu ta daga ya Allah ya ubangiji ka kawo mana agaji Allah kanuna mana iyayenmu kuka sosai takeyi, nagaji da wannan cin mutuncin jidda dole na dau mataki baxan iya jurewa ba ko ada ina kyalekune saboda aiki nake muku yanxu kam yayanki nake aure bazan iya ba dole na dau mataki

*********
washegari da safe ta fito daga wanka hindu ta shigo da breakfast dinsu sulthana na biye a bayanta, ta kallesu anan zakuyi breakfast din ? kai sulthana ta daga mata waccen masifaffiyar matar ta hakimce a dining area tana ta muxurai shine momy ta kawo min tace muje sama muyi breakfast din,zama jannat tayi hade da tagumi,sulthana ta kwashe da dariya anty jannat ki kwantar da hnklinki wllh duk da tana takamar ita kanwar dadyce gidan dan'uwanta ne idan ta kuskura tace zata kara takamu nima sai na takata dan bata da girma a idona bazan iya jure cin mutunci ba dan ma nayi sauki sai na nuna mata kuskurenta, hindu ta katseta, haba sulthana matar nan fa ba sa'arki bace kodan darajar dady ki kyaleta plx dan Allah muna xaune lfy kada kija mana tashin hnkl duk masifarta nasan ba dadewa xatai a gidan nan ba, hararar hindu tayi idan xaki iya jurewa ki jure nikan wllh bazan iya ba ita tasan ba sa'ata bace take janmu da masifa ta xubar da mutuncinta nasa kafa na take, jannat ta kalli sulthana any'a kuwa kina shan mgninki sulthana ? ina sha sosai naga canji bakuyi mmkin jiya ban rama abinda matar nan tai mana ba ?? plx anty jannat sauko miyi breakfast a hnkl ta sauko tana tausayawa kansu na rashin sanin iyayensu,
bayan sun gama breakfast hindu tace jannat dama jidda budurwa ya khaleel ce ? kai jannat ta daga mata,sulthana tace jiya ruby take bamu lbr wai har ansa musu rana,tsaki tayi hanji dadi ba ko kadan, anty jannat naso ace ke kadaice matar khaleel banso kiyi kishi da tsohuwar guxuma irin jidda, murmushi jannat tayi dole ne sulthana sbd an dade da sa musu rana,addu'a xaki mana Allah ya bamu zaman lfy,test ya shigo wayarta tana dubawa taga ya khaleel ne...... ki kawo min breakfast..... ajjiye wayar tayi ta kyaleshi
Chapter 33 · 0% Book details