← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 84

Sashe 34

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*********
karfe 3:00 na rana suna xaune a falo jannat tana cikin daki haisam ya shigo, sulthana ta bata rai tai kamar bata ganshi ba xama yayi yana kallon tv da suke kallo, ya kalli sulthana ya ga ta bata rai, ya fuskanci kwana biyun nan ta daina kulashi, sulthana ba gaisuwa ? bata kalleshi ba tace ya kk ? murmushi yayi lafiya lau nake naga kin canza ko wani abun akai miki, murguda baki tayi wai kai ya kk so nayi in yi mgn kace bani da kunya sannan nayi shiru kana tmbyr me akaimin ina ruwanka da shiruna ? murmushi yayi ya mik'e bai ce mata komai ba ya fice, ta harari bayansa hade da yin kwafa, yana fita ya khaleel ya shigo dai dai lokacin da jidda take saukowa da ga upstairs ganinshi yasa ta karaso da sauri, gab dashi taxo sannu da xuwa ya khaleel, yawwa sannu, rubayya ki kawo min lunch dina daki, da sauri jidda tace ta bash shi zan kawo maka, ok yace ya fita kitcean ta wuce, sulthana ta tabe baki ta hau sama ta tadda jannat na karatun kur'ani, ta ajjiye kur'anin ta mike tana kallon sulthana, wani kallo takewa jannat din wai meya sameki ? ga shi cen waccen muciyar ta tafi kaiwa mijinki abinci tana matsayin budurwar shi idan kika tsaya sanya xata fiki daraja ni banga amfaninki ba keda mijinki ki xauna wata cen budurwar shi ta dinka yi masa hidima ? ki nemi dabara dan wannan ba ta dace da ke ba, ta fice daga dakin jannat tabita ta kallo hade dayin ajiyar xuciya, sulthana bakisan halin ya khaleel bane canza kaya tayi tai makeup ta fesa turarenta mai kamshi ta nufi kitcean ta hada masa coffee tai bangarensa sallama tayi ya amsa hade da galla mata harara, yarasa gane ina yarinyar nan ta dosa kusa dashi ta anjiye coffee din ta cire hijab dinta kamshin turarenta dayake so ya shaka ta xauna kusa da shi jidda na cen gefen ranta amatukar bace, ta gaishe da ya khaleel ya amsa yana danne dannen wayarshi miko masa coffee din tayi duk da yana fushi da ita haka ya amsa dan baya iya yin xuciya dashi, sannu ya khaleel ka gaji ko ? gama shan coffee din kaci abinci in maka tausa, araxane jidda ta kalleta shima mmk ne yasa ya kalleta yarinya sai kace mai aljanu kullum da salon daxata bullo dashi shi sam bai gane dan jidda takeyi ba,
ya harareta kadan dauko waccen ledar ya nuna mata leda nesa dasu da sauri ta mike tana tafiya a hnkl ya bi ta da kallo ya lumshe ido, jannat kina da tsari da xubi mai kyau hawaye ya saukowa jidda ganin irin kallon daya kewa jannat da sauri da goge hawayen, ledar ta dauko ta dawo kusa da shi ta ajjiye xama tayi ta bude ledar English wears ne masu kyau, da murna tace ngd sosai Allah yakara budi rufe mata baki yayi da hannunsa bana son gdy hannunta tasa ta riko hannunsa gam tana dariyar farin ciki Allah ya saka da alkairi ya tsareka da ga sharrin mutane da aljanuma, yaji dadin adduar ta hade da mmkin tulin yarintar ta, sakin hannunshi tayi, jidda ta mike tamkar xata fadi kasa da kyar ta fice daga dakin murmushin jin dadi jannat tayi aranta tace kadan kika gani idan baxaki daina shigowa dakin ya khaleel ba tana futa tafara tattare kayan ta xuba su a leda ta mike xata fita ya fisgota jikinshi, meyasa daxu baki kawo min breakfast ba ?hade rai tayi tace, sbd banyi niyya ba kara matseta yayi ajikinsa ni kike fadawa mgn son ranki matsar taji tayi yawa, a a ya hakuri plx dan Allah kasakeni, banza yai da ita yana jinta cikin jikinshi yana jin dadin kamshin turarenta dayake shak'a kuka tasaka sannan ya saketa ta dauki hijab dinta tasa dai dai bakin kofarshi ta tsaya bazan kara xuwa dakin kaba, yanayin yanda tai mgn cike da yarinta murmushi yayi har hkrnsa suka fito yanxu kam yarintar ta birgeshi takeyi tana kokarin fita ya riko ta kwabe fuska, "me kikace ? shiru tayi tana kallon gefen shi kamar xata fashe da kuka, baxaki kara xuwa dakina ba ko ? to babu inda xaki nan xakiyi ta zama, zaro ido tayi hade da kwabe fuska, kayi hkr ya khaleel, lip dinta ya kalla ganin yana kallonta yasa ta bata rai plx zan tafi daki ka cikani, kafin ta karasa taji bakin ta acikin nashi ya riketa gam yadda baxata iya motsawa daga rikon da yai mata ba sai da yagaji dan kansa ya saketa ta juya aguje ta fice ya bi bayanta dariya ta subuce masa cikin jin dadi ya xauna shi kam da baya son yarinta yamxu kam yarintar jannat birgesa take tana kuma sashi nishad'i

***********
da sauri ta nufo bangaren su jidda ta hango idonta sunyi jaa tana kara sowa hijab dinta ta kuma fincika, tsaki jannat tayi tana mata kallon sama da kasa, ganin irin kallon da jannat din take mata yasa tace iyye sannu yar matsiyata kinxo gidan arxiki kin bude kafa kina cin maiko har kin auri d'an masu gida, kinyi kuskure Jennifer sai kinyi danasani kina tak'ama da auren shi kike shiyasa kike min gadara to wllh sunan aurenki matacce, tab'e baki jannat tayi wannan ne kuma baki isaba sbd Allah shiyake da ikon komai ba wani ba, sannan niba sunana jennifer ba sunana jannat kada ki kara kira na da wannan sunan rufemin baki kona wanka miki mari jidda ta katseta,ba'a canxawa tuwo suna agurina har gobe sunanki Jennifer dashi zan kiraki, jannat ta galla mata harara ba mmk dan daga ganinki baki san ciwon jikinki ba idan kin saba hada jiki da ballagaxaxxu irinki nidai ba ballagaza bace kije kiyi da wanda kika sabayi dasu ta wuce afusace jidda ta kuma janyo hijab dinta, ki kare min kallo kinga nayi kala da ballagaza ?? wannan kuma ke xaki ba kanki amsa dan baki isa na kalleki ba, sakin hijab dinta tayi wllh baxan iya kishi da yarinya karama irinki ba akan ya khaleel babu abinda baxan iya ba banza yar tsintuwa mara asali, har jannat ta juya xata tafi ta dawo baya, meyasa kika bari mara asali ta rabaki da wanda kikeso ? alhmdllh ina gdw Allah da yayine a haka bani da asali amma ina tsoranshi kuma ina alfahari da jarabawarsa agareni dan nasan mumini na kwarai ake jarabta keda kike yar asali ni da bnda asali bamu da banbanci tunda dukkaninmu yan adam ne kuma mata, ta wuce ta barta anan tana mmkin ta batayi tunanin tana da baki haka ba da gudu ta karasa daki wajan ummanta tana xuwa ta fada jikinta ummana zan iya mutuwa,bakin ciki xai kasheni umma tunkina da ranki bakin ciki xai halakani araxane umma take jijjigata me ya faru jidda ? menene ? sai da ta gama kukanta hnklin umma atashe ta rarrasheta ta kwashe karya da gasky ta fadawa umman, ran umma ya baci sosai kwantar da hnklinki y'ata khaleel xai xama naki ki juyashi son ranki na miki alkawarin sai yadda kikayi dashi

by
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

65&66

Ngd ummana ina son ya khaleel yaji ni kad'ai yakeso arnsa bana son kishiya ummana araba auren khaleel da Jennifer,
Share mata hawaye ummanta tayi cikin kwarin gwiwa kada ki damu da wannan jidda ni kaina ban xauna da kishiya ba balle ke guda daya tal koxan tafi tsirara sai na cika miki burinki bani da farin cikin da ya wuce naki ki kwantar da hnklinki zanje wajan malamina na nan kano ya iya aiki kamar yankan wuk'a duk xasu Sani dukansu dariya jidda tayi cike da farin ciki Dan tasan ummanta ta akwai bin yan tsibbu babu abinda baxata iya ba, idan xata sama mata farin ciki,
Chapter 34 · 0% Book details