← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 84

Sashe 25

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da yamma suna xaune a falo bayan sun gama cin abinci hindu tace dady ina son mgn dakai ya kallete yana naxarin fuskarta ya fuskance ta tunda suka xo gidan nan Sam bata da nutsuwa ko da yaushe a cikin damuwa take, ina jinki hindu,
Dady narasa ta inda xan fara bin ciken inda iyayenmu suke,
Jinjina kai dady yayi ni kaina narasa ta ina xan fara, abinda yakamata muyi shine mu dogara da Allah mu mike tsaye mudage da ambatonsa da naiman daukinsa sbd Allah da kansa yace mu rokeshi xai amsa mana,
Jenny tace dady ko xamuje gidajen radio da jaridu,ko xa'a dace ?
Shiru yayi yana naxarin xancen,
Momy tace ganina wannan ba mafita bace, tayaya xa'a fara cigiyar ? Ace wacce ta yadda yayanta har 3 shekaru goma sha takwas? Ta ina xa'a sameta ? Hakan ma kamar jawo wata masifar ne sannan ga tonon asiri muddin yan jarida suka San da haka sun dinka yayata zancen kenan Ku xama abin nuni a gari kunya ma ta ishe ku,
Addu'a itace mafita ko ba'aga iyayen Ku ba ni Ku daukeni matsayin uwa dan ni tuntuni na maidaku yayana,
Sunthana ta fashe da kuka ta daga hannayenta sama dukansu suka kalleta da tausaya wa, ya Allah ya ubangijina gareka na dogara gareka na ke naiman taimako ya Allah kasa kafin na koma gareka Allah kahadani da fuskar mahaifiyata na ganta ta ganni, tana kuka sosai
hindu ta runtse ido hade da mikewa ta bar wajan,
Jenny ma kukan takeyi batason lokacin da ta fara fadin inaji ajikina xan hadu iyayena amma narasa ta ina ta wacce hanya ? Mikewa itama tayi ta bar sulthana anan tana kuka,
Dady ne yai karfin halin rarrashinta dan duk tausayinsu ya kamasu kiyi shiru sulthana ko mai tsanani yana tare da sauki duk jarabawa tana tare da falala nan gaba wannan jarabawa ce kuma babu mahlukin da xai guje mata Allah ya fada a alkur'ani, inna kulla shai'in kalaq nahu bi kadar wama amruna illah wahidatan kalam hin bil basr, komai da Allah ya halicceshi sai da ya halicci kaddararsa, idan Allah yaga dama cikin kankanin lokaci sai Allah ya hadaku da iyayen naku, kuyi kokari Ku cinye jarabawar nan taku Allah yana tare daku sannan ubangiji yana amsar addu'ar Wanda aka xalunta da gaggawa, anxalunce ku duk Wanda yai muku wannan danyan aikin ya xalunceku, ya jinjina kai kowaye kubarshi da rabbil ixxati, mudage da addu'a dan ubangiji mai jine mai ganine yana kallon kowa, masani ne akan komai Allah ya kawo mana mafita Allah ya baiyana su,
Cikin kuka ta amsa da Amin ta mike xata hau Sama, da sauri ya dakatar da ita. Sulthana ! Banda fada plx kuxauna lfy kai ta daga ta wuce sama
Jidda ta ya mutsa fuska ita tun xuwan gidan Sam tsarin bai mata ba ta gwammace ta koma gidansu, tunda burinta ya cika an Sa ranar aurenta da ya khaleel,
Ashagwabe tace dady ina son komawa kd naga ummana kallonta yayi, yace ba damuwa duk lokacin da kika shirya sai akaiki, tamike xahara tabi bayanta suka hau sama,
Jingina yai da kujerar dayake xaune yana jinjina al'amrin yaran nan mai sarkakiya yaran suna matukar bashi tausayi lallai xaiyi aiki da jikinsa da dukiyarsa wajan taimakonsu dan ya cika musu burinsu,
Itama Momy abinda take sakawa kenan aranta da tana da yadda xatayi da tayi dan ganin yaran nan sun hadu da iyayensu tunda taji lbrnsu kullum sai tai musu kuka tana matukar tausaya musu sbd halin da suke ciki tana jinsu tamkar yayenta na cikinta

*******************
Da daddare dady ya sameta a daki tayi xugum tarasa me ke damunta, Jennifer ! Ya kira sunanta ta dago kai ta kalleshi da sauri ta sunkuya ta gaishe shi cikin girmamawa,
Ya amsa da tausayinta fal aranshi,
Kina da Wanda kikeso acikin masu sonki ?
Cikin matukar karfin hali ta masa da ah ah dady, kallonta yayi naya naxarin ta,
babu Wanda kikeso?
Eh dady, bavaka xabi ka xabi duk Wanda yai maka in dai ka yadda da ingancin addininsa,
Gyada kai yayi Allah yai miki albarka Jennifer,
Ta amsa da amin yace jibi juma'a nake so da an idar da sallar juma'ar a daur auren ubangiji Allah yasa albarka a rayuwar aurenku,
Ta kyar ta iya amsawa da amin,
Ya fice yana jin dadin biyayyar yarinyar yana kuma tausaya wa halin da suke ciki,

Tunda ya fita ta fashe da kuka shikenan yanxu tarasa ya khaleel dinta ? Tarasa farincikinta tarasa Wanda take matukar so ? Baxata iya fadawa dady shi take so ba baxata iya ba ! Cikin kuka take maganganunta,
Rayuwa tana xuwar min abaibai abinda nake tunanin yiyuwarsa baya yiyuwa yaushe zan fara rayuwar farin ciki ? Yaushe burina xai fara cika ? Yaushe xan fara son abu na samu ? Meyasa duk abinda nakeso ban fiya samuba ? Kuka take sosai tana sambatu

***************
Washegari ranar alhamis gaba daya ranta acunkushe take jinshi tana xaune adaki sulthana ta shigo,
Amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida, kallonta kawai jenny tayi hinduma ta shigo dakin,
Gobe muna da shagali a gidan nan,
Bata rai jenny tayi,
Hindu tace wai plx jenny waye mijin naki nifa ban San Wanda xaki aura ba,
Hawaye ya saukowa jenny tace nabawa dady xabi nasan baxai xabamin mutumin banxa ba,
Da sauri hindu tace dama abaki wannan dan xafin kan dan kun dace da shi,
Wani irin kallo jenny tai mata hade da sauke numfashi tasan ba xa ataba bata shiba hawaye ya sauko mata shine burinta shi takeso amma ina yai mata nisa,
Sulthana tace wannan dan xafin kan yanda ya keji da kansa tunaninshi xai iya bashi ya wuce da ajinta dan dai kawai jenny mai Kyau ce, karar bude kofa sukaji kan jenny akasa tana tunanin wanne irin miji xa a bata ?,wa xa'a aura mata ? Muryarshi taji kubani waje xanyi mgn da ita ! Da sauri ta dago kai ta akalleshi fuskarshi a daure
Mikewa sukai har xasu fita sulthana ta kalleshi
Plx xan baka shawara, kallonta yayi
Da sauri tace shikenan ma ba komai, ta fice
Murmushi Jennifer tayi tace lallai sulthana rijiya ba wajan wasan makaho bane,
Ya jima yana kallonta baiyi magana ba kanta akasa jikinta na karkarwa jira kawai take taji da me yaxo,
Muryarshi a sanyaye yace Jennifer! Naam ta amsa, tana sauraronsa,
Kin fadawa dady xabinki ? Wanda kikeso ?
Ah ah ni babu wanda nakeso nabashi xabin ya xabamin wanda yaga yadace dani,
Kwaba yayi cikin facin rai haka kikeso ?
Meyasa kikeson cutar kanki ? Kin gwanmace ki auri wani da soyayyar wani ?
Mikewa tayi a dake dan tafara gajiya da titsiyen daya ke mata, ta kalleshi idonta cikin nashi,
Nifa ya khaleeel ba wanda nakeso
Karya kike ! Ya katseta kina dashi ya xuba mata ido wani abu yaji ya na bin jikinsa,
Ya matso gab da ita numfashinsu na karo kowanne najin fitar na kowa, gabanta ya fadi da karfi ta sunkuyar da kanta yasa hannu ya dao fuskar suka kalli juna,
Muryar shi adashe kin San xuciyarki kinsan abinda takeso kada ki kuntata kanki har yanxu kina da lokaci kije ki fadwa dady kina da xabin ki shiru tayi dan tarasa me xatace,
Kura mata ido yayi yana kallon lip dinta ya runtse ido bayason rasata bayason rasa komai nata bai son rasa dan karamin lip dinta me matukar taushi da xaki, gabanta na faduwa tarasa yadda xatai ya tsura mata kyawawan idanuwansa a hnkl ya sauke faskarta daga hannunshi ya matsa nesa da ita kada ki kuntatawa rayuwarki ki faranta mata da samun wanda kikeso sbd shine nutsuwarki ya fice daga dakin [truncated by WhatsApp]
[2/28, 6:42 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

53&54
Chapter 25 · 0% Book details