← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 84

Sashe 45

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana sauka ya hadu da drivern Alhaji nasir ya kaishi gidansa suka tattauna Dan amininsa ne tare sukayi kuruciya bayan sungama suka tafi wajan President sbd yasan da xuwansu kai tsaye gidanshi suka wuce suka sameshi a falonsa na musamman da yake saukar baki way'anda suke da muhimmanci,
Yana ganinsu ya saki murmushi, Dr bashir rabona dakai shekara shida kenan kullum kana nan a yanda kake, dariya dady yayi yabashi hannu suka gaisa bayan sungama gaisuwa, President ya kuma kallon dady,
Dr bashir meyasa kaki yadda da shawarata? Siyasa ta dace dakai danshi mulki yana neman mutane irinka masu adalci ina fata xuwan nan dakayi kaxone dan ka fada min ka yanke ahawara xaka shiga siyasa Dan ka kwatowa talakawa yancinsu ?
Girgixa kai dady yayi dan sam bai son xancen ya kalli President ba wannan bane ya kawoni ina son wani taimakone,
Da mmk President yake kallonshi yanxu bashir dan kana son abu awajena sai ka kirashi da taimako? Murmushi dady yayi, ina son kai min hanyar da xanga Adamu ched'e
Ajiyar xuciya President yayi yana jinjina kai yai murmushi yana kallon dady,
Ni kaina rabon dana Sa ched'e a idona na manta shima irinkane ba ruwanshi da yan siyasa tsakanin mu dashi idan muntashi kanfen mu kirashi awaya mu tambayeshi kudi ya bamu muyi canfen dashi waya kwai xamuyi yasa aturo mana wani xubin ma ko ka kira wayan yaransa ke d'agawa ganin ched'e ba karamin babban aiki bane yanxu xakaji cen gobe ka jishi acen,

By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

77&78

zaro ido umman jidda tayi cike da kad'uwa da mgnr da dady yayi, da rarrashi dady yace, ajjiye wukar danjuma,
jikin danjuma a sanyaye ya ajjiye har yanxu hawaye na xuba daga idonshi danji yake xai iya yin komai akan soyayyar jidda, dady ya kallesu ranshi ab'ace
gaba d'aya kowa yaje yai sallah xuwa gobe xamu tattauna,bana son naji kowa yakara wannan mgnr
ya wuce, jikin kowa asanyaye suka bar wajan, daren ranar kam kad'an ne na gidan suka iya cin abinci sauran kam xuciyoyinsu kamar wuta jidda kuka take sosai,tana jin wani irin tuk'ik'i a xuciyarta,

washegari tun da sassafe baban jidda yaxo gidan dady dan tun jiya dadyn ya kirashi akan yana son ganinsa da gaggawa, haka ya taso hajja mahaifiyarsu wacce bata da lfy tana fama da hawan jini ba kowacce mgn ake fad'a mata ba,
dady ya tara mutanen gidan kaf a babban falon k'asa, kowa ka kalla yana cikin mmk, jidda har lokacin kuka take musamman dataga mahaifinta ita kanta umman jiddan arikice take ganin mijinta yasa ta shiga wani sabon tashin hnkln, danjuma yana xaune agefe ya takure cikin xuciyar shi yana jin takaicin yadda ya tsinci kanshi a wannan halin, cikin takaici mara misaltuwa dady ya fara mgn,
Alhaji musa nasan kayi mmkin kiran gaggawar da nai maka sbd jibi ne ranar da ta kama daurin auren Ibrahim da jidda,
kuka danjuma yasaka Alhaji kataima kamin,
dady ya xuba mishi ido cike da tausayawa, ya kalli umman jidda da harara,
sai kiyiwa mutane bayanin abinda kikayi,
sunkuyar da kanta k'asa tayi hawaye na xuba kunya sosai takamata tarasa ta ina xatai bayanin wannan abin kunyar,
ya daka mata tsawa a firgice ta d'ago kai jikinta na karkarwa wani b'akin ciki mai xafi ya tokare mata kirji,
sam takasa bud'ar baki tayi mgn,
cikin kuka hjy Aisha yayarta ta fara mgn xuciyarta akarye, kayi hkr yaya bashir kuskure ne da kuma kad'dara, shekaranjiya ne mukaje wajan wani malami akan ana so jidda ta mallake Ibrahim, tayi jim cike da danasani muryarta k'asa k'asa had'e da kuka ta cigaba,
shine yai aiki mai karfi ya bamu yace ta xuba masa a abinci ko a lemo in dai yasha to sai yadda tayi dashi dan ko uwarshi tace kada ya kara gaisheta baxai k'ara ba xata maidashi kamar d'anta sai abinda tace,
salati Alhaji musa yayi ya cire hula yana girgixa kai gumi yaji ta ko ina,
momy ma salatin tayi hawayen farin ciki ya sauko mata na Allah ya mayar musu da mummunan k'udirinsu,
jannat ma hamdala tayi ta godewa Allah xuciyarta cike da tsoron Allah, hajja kuka tasaka tana yiwa yarta mugun kallo,
hadiza ina bak'in cikin mugun halinki yanxu ko makiyinki xaki masa haka ? balle Ibrahim daya ke d'anki ? innalillahi wa inna ilaihi raji'unn kin cuceni hadiza kin gama da rayuwarki,ya khaleel daya ke kusa da ita ya riko mata hannu plx hajja yi hkr ki yi shiru, ta rik'e hannunshi sosai sannu khaleel kayi hkr kaji nasan kana da tausayi da imani da taimako shiyasa Allah yake tare da kai, d'aga mata kai yayi, ki daina kuka hajja,
tabe baki dady yayi yana yiwa hjy hadixa mugun kallo cike da tsanarta,
kinga yadda Allah ya nuna ikonsa ko ? Allah baya barin xalunci, Ibrahim d'ankine hadiza idan kin maidani d'an'uwanki kaf d'inku kun tsani firdausi mahaifiyar shi wai ta shanyeni, yar bin bokaye ce da malamai yanxu tsakaninku waye mai bin bokan ? tunda yaran nan suke xaune cikin gidan nan kuke xaginsu kuna aibatasu kuna ce musu yan asiri sbd kawai sun rab'eni,
sam bakwason kowa ya rab'u da jikina,
wannan shine babbar sakayya daga ubangiji yanxu sai ku gane abu d'aya duk wanda yake xaune dakai da kyakkyawar xuciya ubangiji baxai baka sa'ar ka cutar dashi ba,
Alhaji musa ya kalli dady,
Dr bashir yau yaxama dole na fadi abinda ke raina akan hadixa da y'ata hauwa'u ka gansu nan babu wanda na isa dashi hauwa'u ita kadaice mace tilo da Allah ya bani amma sai na shafe wata ko shekara ban sata a idona ba danayi mgn uwarta tace min tana gidanka bawai zan hanata xuwa gidanka ba amma amatsayina na ubanta yadace ace duk inda xataje a fad'amin, amma sbd ammai dani buje dantofi ya jinjina kai ban isa ba sai dai na xuba musu ido, hadixa ta rabani da yan'uwana tace duk mak'iya nane
Dr bashir na fad'a maka hakane dan kagane wannan kad'an daga cikin mugun hali irin na hadiza ta xamemin masifa bala'i a ratuwata narasa yadda xanyi da ita,

innalillahi wa inna ilaihi raji'un lokaci daya dady da hajja sukayi hajja ta k'ara rushewa da kuka , da kyar khaleel ya rarrasheta tayi shiru,
sai a yanxu dady ya tabbatar da hadiza ba k'aramar makira bace gdy yaiwa Allah daya tsare d'ansa daga makircinsu,
cike da jimami dady ya cigaba da mgn,
aikin gama ya gama khaleel Allah ya tsareshi daga wahala baici abincin ba cikin tsautsayi ya bawa danjuma ya nuna danjuman daya ke arab'e yaci abincin sai akayi dacen shima sunanshi Ibrahim,
dalilin haka ya shiga wani mayuwancin hali na kaunar jidda har yana ikirarin muddin aka hanashi xai iya kashe kanshi ya kasheta,
xaro ido hajja tayi hade da murmushin yake tace alhamdulillah Allah nagode maka,
Alhaji musa shima murmushin takaici yayi ya kalli danjuma, kwantar da hnklinka d'ana na baka auren ta kuma yau yau dinnan xa a d'aura maka aure da ita, wani ihu jidda ta kurma hajja ta kai mata rankwashi,rufewa mutane vaki makira ba uban da ya isa ya hana wannan d'aurin auren haka ba wanda ya isa yace baxa d'aurashi ayau ba, ngd maka musa nagd mk musa, haka akewa mutane masu mummunan xuciya ta fashe da kuka, wllh ban wa hadiza wannan tarbiyyar ba cen y'an bariki suka b'atamin ita Allah ya shiryar min dake, kuka hadizan take sosai dana sani na xiyartar ta ta ko'ina,
Alhaji musa ya kalli danjuma fuskarshi na nuna tausayinsa,
kana da sadaki a hannunka ?
asanyaye danjuma ya shafo aljihunsa dan bashi da kudi sai wasu yan canji, da sauri ya khaleel yace xan biya mishi sadakin,
dan shi ya fi kowa farin cikin wannan hadin waskewa kawai yake yana nuna ya damu amma xuciyarsa cike take da farinciki,
danjuma
ya kalle shi ngd oga khaleel
Alhaji musa yace ka katuro wakilinka
kana da mata ?
kanshi a k'asa yace mahaifina ya rasu sai mahaifiyata datake xaune da matata acan garinmu gexawa,
nan garin bani da kowa idan kuma xa'a jira wakilan nawa zan kirasu awaya, dady yace in dai wakiline zan zame maka Allah ya baku xaman lfy,
nagode dady,
kada kadamu danjuma kaima kazama namu tunda xaka auri yarmu,
Alhaji musa yace kana da inda xaka ajjiyeta ?
girgixa kai yayi jikinshi asanyaye sai dai gidanmu na gado na cen gexawa d'aki biyu ne anan matata da mahaifiyata suke xaune,
Alhaji musa yace nabaka gidane da yake rijiyar xaki nan kano ku xauna aciki,
idon danjuma fal hawaye yake gdy,
dady yace zan canxa maka aiki kadawo companynmu Allah ya baku xaman lfy,
fashewa yayi da kuka lokaci daya Allah ya axurtashi ta dalilin wannan auren yai gdy sosai, hajja tace saura waccen ja'irar ta nuna zahra, dady ya gallawa xahran harara itama cikin satin nan zan aurar da ita ga duk wanda na ga dama sbd itama na fuskanci wani irin hali gareta, da sauri hajja tace bakin hali kai,
kai dai baka dashi uwarta ma bata dashi xama da wannan ta nuna hadixa yasa tana k'ok'arin komawa ita sak Allah ya shirye ku addu'ar da xan muku kenan, zahra ta fashe da kuka hajja tabige mata baki yi mana shiru munafuka,
Alhaji musa ya kalli agogon hannunsa inshaa Allah yau ana idar da sallar axahar za'a daura auren ya mik'e tsaye dady yayi addu'a suka tashi ya khaleel ya mik'e shima had'e da kiran danjuman yabi bayansa dakinsa yaje kayan shi da dady ya dinko masa sbd bikin shi da jidda set 30 ya d'auko ya had'a masa da hula da takalma harda agogonsa wannan dady ya siyo masa ya bashi, danjuma gashi nan aje ayi hidimar biki dasu, gdy sosai danjuman yakeyi, shikam ya khaleel farin ciki fal ranshi shiyasa ya had'a kayan da aka siyo masa dan d'aurin auren ya bada su dan ko kallonsu bai son yi tunda Allah ya rabashi da alak'a k'ai
Chapter 45 · 0% Book details