← Book details Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 84

Sashe 72

Jennifer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan cikin G.R.A CHED'E CRESCENT aka kaisu unguwa guda Abba ya ware akayi wa kowa gini gidajen nasu iri d'aya

jannat na xaune gefen gadonta tana xubar hawaye tana tuna rayuwarta da y'an'uwanta da irin budirin da sukeyi d'akin kowacce daban amma kullum suna tare da ita wataran ma ad'akin nata suke kwana sbd shak'uwa yau gashi sun rabu wannan rayuwar ta wuce taxama tarihi tana son y'an'uwanta sosai gashi yanxu sun rabu kowacce ai kaita gidan mijinta kuka sosai takeyi

ayimin afuwa gobe na cigaba☹
[2/28, 6:44 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

111&112
*Ummee Garkuwa*
satin su 2 a dubai suka wuce Singapore sun sha amarcinsu sosai sun nunawa junansu soyayya satinsu 2 acen Abba ya kirasu awaya akan su xo hjy murja bata da lafiya sosai ba shiri suka dawo batare da sunyi adadin kwana kin dasuke son yi ba tun acikin jirgi jannat take kuka sosai sbd basu san yadda jikin hjy murjan yake ba gaba d'ayansu hnklin su atashe yake har suka dawo 9ja kai tsaye gidan su suka wuce suka tadda shi empty ba kowa duk suna asibiti megadin su ne ya fad'a musu asibitin da suke nan cikin G.R.A lameedo crescent kai tsaye asibitin suka xarce a babban d'aki suke wanda d'akin an wareshi ne sbd kwantar da manyan mutane tunda suka shiga hnklin y'an'uwansu ya dawo kansu kowa na mmkin dawowar tasu dan basuyi tsammanin su yanxu yanxu ba hjy murja na kwance kan gadon marasa lfy ta rame kana ganinta kasan tasha jinya da sauri ta tashi daga kwanciyar datayi tana kallonsu fuskar ta d'auke da murmushi hannu ta nik'owa jannat
"Alhamdulillah jannat kin dawo xo na rik'eki naji ko kece ba gixo kikai min ba"
hawaye fal idon jannat ta k'arasa kusa da ita ta rik'e hannunta k'am tamkar wacce xa'a kwace ta.

hannu ta mik'owa khaleel dayake a tsaye yana kallonsu fuskarshi d'auke da tausayinsu.
"matso khaleel ngd wa Allah daya dawo min da ku lfy ban mutu ba"
hjy Nabila tadake gefenta a xaune tayi tagumi muryar ta asanyaye tace,
"haba murja tun yaushe zan fad'a miki ki daina wannan zancen ? cuta fa ba mutuwa bace kin damu bakiga jannat ita da khaleel damuwar hakan har ciwonki ya tashi gasu nan sun dawo kusa dake ki saki ranki,
ki daina sa damuwa aranki Allah xai kiyaye miki su"
tak'arasa idonta fal hawaye.

tunda ta fara mgn falon yai tsit suna kallonta har tagama

wani irin murmushi hjy murja tayi cikin muryar mara sa lfy dasuka fara warwarewa tayi mgn

"bana ji na dai dai idan har bana jin nimfashin su kusa dani babban burina duk na waiwaya naga idanun y'ay'ana "
momy tasa baki,
"yanxu ga sunan sun dawo kusa dake ki cire damuwa murja y'ay'anki sun dawo"

dady da Abba ne basu ce komai ba sai binsu da ido,
jannat da hawaye suka cika mata ido tuni suka b'alle hawaye ke xuba kamar an bud'e fanfo

zaro ido sulthana tayi tana kallon jannat dake tsiyauar kwallah
"anty jannat hawayen me kike ? kun tafi kun barmu da kewa kina cen kina hutawa kinyi k'iba da kyau kin xama k'atuwa kin bar umma da kewa gashi nan har ciwonta sai da ya tashi,
kukan me zaki ai mun gama kuka tunda ta warke fatanmu Allah ya bata lfy ke kuma Allah ya sauke ki lfy "

idonta fal hawaye hakan bai hana ta jefi sulthana da uban harara kamar idanuwanta zasu fad'o

hjy Nabila sunkuyar da kai tayi fuskarta k'unshe da murmushin jin dad'i dan taga y'arta ta ta canza alamun akwai motsi a cikinta dan ga alamu nan b'aro b'aro sun bayyana

momy kam hamdala tayi axuciyarta najin dad'in samun jikanta na farko a duniya itama yau taxama kaka.

k'ara rik'e hannunta hjy murja tayi tana hararar sulthana kad'an
"karki matsa mata yanxu lallashi take buk'ata Allah ya sauki jikana lfy"
dukansu suka amsa da amin

hajiyarmu tace
"banda muna asibiti dana yi gud'a Alhamdulillah ! ina kallonki nasan jikata akwai kyakkyawan motsi a jikinta"

tuni ya khaleel ya manta a inda yake
"hajiyar mu da gaske kikeyi jannat tana da ciki ?"

hararar wasa tai masa cikin wasa tace
"ah 'ah bata dashi sai k'aton toilet"

dady da Abba ficewa sukayi fuskokinsu k'unshe da murmushin wannan lbrn na samun k'aruwar da sukayi..

khaleel ne yai hmdl mai cike da xak'uwa da murna matuk'a dan bai tab'a tunanin ajiyar tashi ta xaunu ba

"Alhmdulillah na zama baba nima Allah na gode maka da wannan ni'ima jannat! Allah ya biyaki "

sulthana kwashe wa tayi da dariya da sauri ta kame baki tana kallon hjy murja

ta waiwayo kan ya khaleel daya xubawa jannat ido yana jin kamar ya had'iye ta,

"majnun kalli umma da hajiyarmu da momy kada kayi sub'ul da baka"

waiwayo wa yayi fuskarshi kamar ammasa albishir ko kad'an baxai iya k'iyasta abinda yakeji na game da farin ciki

"suma suna cike da murna sun sami jikan su na farko,
kada kidamu k'anwata yau babu wannan
abune na farin ciki bazan iya k'iyasta miki yanda nakeji ba zan xama uba ga d'an da jannat xata haifa mana"
da sauri jannat ta kwatse shi da shagwab'a
"habaaa ya khaleel ! kabarii manaaa kana kallonsu momyyy faa"

kama bakinsa yayi yana kallonta
"sorry sorry beautyna kada ki yi fushi kin san ba ke kad'ai bace "
murmushi hjy murja tayi

"ya khaleel angon k'arni kwantar da hnklinka baxatayi fushi ba,
ina ita ina yin fushi bayan tasan ba ita kad'ai bace ?
jannat yi shiru saki fuskarki "

salati momy tayi hjy Nabila ta tayata.

" oh ! zamani Nabila kalli ikon Allah uwa da y'ay'anta tana tayasu sakarci?"

hjy Nabila tace
"hmm kasa mgn nayi uwar da y'ay'an sai a hnkl"

hajiyarmu tai dariya tana kallonsu

"kunga kada mu matsawa jikokina kuma ba'a hanaku yi ba ku kyalesu su warwasa"

hindu da ta zabga tagumi tana mmkin surutun su da rashin kunya ta ya mutsa fuska

"wai kun manta a asibiti muke ?"

hajiya murja ta kalli hindu.
"hindu na warke ni kam babu wata sauran cuta kuma yanxu babban fatanmu Allah ya sauki y'ata lafiya"
ta k'arasa mgnr tana kallon jannat fuskarta k'unshe da murmushi.

kwanan su 2 da dawowa aka sallami hjy murja daga asibiti sbd ta warke.

hankalin dangi biyu na kan cikin jannat dan sai da suka sa akai nata test anan asibitin aka tabbatar da tana da shigar ciki wata 2 da sati uku farin ciki kam ba'a mgn kaf dangi sai da suka san da zaman cikin dan ched'e family har d'an k'aramin biki sukayi shi kam Alhaji Adam ched'e kallon dangin nasa kawai yake amma xuciyar sa na k'in amincewa dasu sbd cike yake da xargin su.

tana kwance jikin ya khaleel tana cin magarya dan bata laulayi ko kad'an sai d'an karan kwad'ayi kusan komai ta gani birgeta yake suna kallon tashar libarty tv bayan sun gama news suka fara na farashin kasuwa suna nuna hotunan kayayyakin abinci karaf idonta ya kai kan gwarin kwaki tuni taji tana sha'awar shi musamman jik'ak'k'e me siga da gyada mai gishiri irin had'in dasukeyi lokacin da tana gidan maman david abinka ga renon yare
tuno had'in tayi

ta had'iyi yawo da sauri ta kalli ya khaleel daya ke k'ok'orin canza wata channel d'in

"ya khaleel ina son garin kwaki plx yanxu"

ajjiye remote d'in yayi da sauri yana kallonta

"ok beautyna duk abinda kikeso cikin sauri zan kawo miki sbd bana son ajiyata ta wahala"

ta xame daga jikinsa ya mik'e ya sunkuyo dai dai cikinta ya shafa shi kamar yanda yake kullum.

" babyna zanje na siyowa mamanka garin kwaki yanxu zan dawo bana son na dink'a nesa da kai amma zan bar amanarka a hannun mamanka ta kula min da kai,"
ya k'ara shafa cikin
"me zan siyo maka?"

kwab'e baki jannat tayi.
ya tashi yana kallon fuskarta ya mannata mata kyawawan kiss a fuskarta ya fice.
bai jima da fita ba ya dawo da sauri .
"beautyna banyi mantuwa ba ?"
ta kalleshi da mmk

"ya khaleel baka manta komai ba "

ya d'an xaro ido
"any'a kuwa ?"

turo baki tayi

"plx katafi kaje na matsu insha garin nan"
yarfe hannuwansa yayi

"sorry sorry jannah ta ina tunanin kamar nayi mantuwa? oh ! "
da sauri yai wajanta ya d'age mata riga
ya mannawa cikin ta kiss

" zan dawo yanxun nan ban yadda da motsi mai k'arfi ba kada ki bige min ajiya sannan ki kulamin da ita da kuma kanki yanxu zan dawo "

kallonshi take cike da xak'uwa na ya tafi ya kawo mata dan ta matsu ta sha marmarinsa ya isheta

ya fice yana dariya yana fita tasaki ajiyar xuciya kafin ta k'ara motsawa ya shigo yana dariya k'asa k'asa tana k'ok'arin mgn ya katseta

"sorry sorry nayi mantuwa zanyi missing d'inka nawasu y'an lokuta kafin na dawo ki kular min da kanki"

ya fice daga falon tana jin motsin tashin motar sa sannan ta saki numfashi tana girgixa kai fuskarta d'auke da dariya mara sauti

"ya khaleel kenan"
ta furta a hnkl kamar mai rad'a
ta ki shingid'a akan kujerar bata dad'e da kwanciya ba bacci yai a won gaba da ita

bata farka ba sai da ta kwashe 4 hours da sauri ta tashi ta yi sallah Dan lokacinta har ya k'ure ta kalli agogo 5:12 na yamma tayi ajiyar xuciya tana mmkin me ya hana ya khaleel da wowa ga sha'awar garin kwakin ya isheta dan ko baccin datayi mafarkin sa tayi janyo wayarta tayi ta kirashi wayar akashe d'an k'aramin tsaki taja ta mik'e da sauri ta fita harabar gidan mai aikinsu ta kira tace taje ta siyo mata garin kwakin ta koma falo ta kunna tv tana kallo bata jima ba mai aikin nasu tadawo tace ta had'a mata shi yanxun nan

bata dad'e ba ta kawo mata ta kalli had'in yawunta ya tsinke dan had'in yayi tuni ta fara sha sai da takusa shanyewa sannan ta ajjiye badan bataso ba sai dai cikin ya cika hnklinta ya kwanta tunda tasha garin

wayar ta d'auko datake kusa da ita takira wayar shi still akashe dai dai time d'in da aka kira sallah magrub ta mik'e tana mmkin wannan abun
Chapter 72 · 0% Book details