← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 167

Sashe 95

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dama ance duk abinda babba ya hango yaro ko uban me zai hau bazai ta
a hangowa ba wallahi, ba ya kwana da ita ba dole ki ga abinda yafi haka ai, babu yanda banyi in lalata batun auren nan ya hakura ba amma sam Meemah kika ki bani hadin kai ki ka koma bayan Abdallah, har da bin wasu malamanki da basu taka kara sun karya ba duk don yarinyar ta shigo hannunsa, to ai ta shigo kuma kin ga abinda ya biyo baya daga shigowarta, to wallahi zai kai ya kawo wataran Abdallah yace bai san mu ba akan yarinyar nan, ni na haifesa ba wani ya haifar min shi ba sarai nasan abinda zai iya aikatawa" Meemah ta dinga kallon Momy babu ko kiftawa don ita sai yanxu ta kara fahimtar dalilin Abdul nayi mata irin wannan mugun tijara kan yarinyar da yake ta ikirarin zai koya ma lesson idan ta shigo hannunsa, sarai kuwa ya kwana da ita dole ya birkice haka ya haukace kanta, dama buzaye da aka sani da mugayen asiri, Meemah tayi wani murmushin takaici tace "To kuwa yanda nayi ruwa nayi tsaki har sai da yarinyar nan ta shiga hannunsa to haka zan yi har sai ya rabu da ita a kwanan kuwa ba da jimawa ba" Momy ta kwado ma sabuwar me aikinta kira, matar ta taho a guje har sai da tsantsin tiles ya kwasheta sbda ruwan dake kafarta sai ga ta a kasa timmm, A fusace Momy tace "Wallahi tallahi kika kuskura kika illata min tiles sai na cire cikin kudin albashinki, yau naga er iskar mata kawai, kullum na kiraki sai kin azabtar min da tiles saboda kauyanci?

Wannan wace irin mata Adama ta kawo min haka da sunan me aiki?" Har kasa mai aikin ta zube tana ba Momy hakuri, cikin tsawa Momy tace "Miko min wayata dallah ki fita ki bamu waje, er kauyen banza" Mai aikin ta kalli wayar dake kan center table dab da inda Momy ke zaune, ta karasa da sauri ta dau wayar ta mika ma Momy, Momy ta warce, mai aikin ta bar parlon, Momy ta mika ma Meemah wayar tace "Dubo min lambar Godiya, glasses dina yana daki" Meemah ta amshi wayar ta dubo number aminiyar Momy sannan tayi dialing ta mika mata, a kashe suka ji wayar, Momy tace "Tayi tafiya me muhimmanci kenan, bari zuwa anjima in sake kiranta" Meemah da kanta ya gama kullewa tace "Tabddi jam, lallai nayi babban kuskuren da ban ta
a yin irinsa ba Momy, sai ma fa kinga kayan dake jikinta da naje gidan, tana kitchen tana soye soye" Momy dai tayi shiru tana girgiza kafa don bakin ciki da takaici, can tace "Dauko min gyale da jaka a daki, ina zaman zamana kin janyo min kashe kudin da banyi budgeting ba Meemah, duk ke kika ja min wannan masifa da kika ki jin maganata wallahi, in hada iri da matsiyata akan wani dalili?

A farko dai na hakura na zuba masa ido da yaki jin maganata, amma yanxu kuwa wallahi sae ya rabu da yarinyar nan, babu dalilin da zai sa in hada zuri'a da ita, ga kuma rashin adalcin da aka yi ma Alhaji ga asara ga biyan tara" Tashi Meemah tayi ta tafi dauko ma Momy gyalenta da handbag, all this while dama ita ke ta shiga malamai don Khaleesat ta shiga hannun Abdul Momy ko bin ta kanta bata yi tunda dama ba son auren take ba, Momy na ficewa daga gidan da driver dinta Meemah ta tafi dakinta da wayarta tayi dialing number Malamin da tasa yayi mata aiki.

Runtse ido Khaleesat tayi bayan taji duk maganganun da Abdul yayi, yana rungume da ita saman gadonsa kamar zai maidata jikinsa, it's past 8pm na dare, jin taki cewa komai s hankali yace "Khaleesat" Bude idonta tayi wasu hawaye masu zafi suka silalo fuskarta tace "Um" Yace "Say something" Still tayi shiru hawaye na zuba idonta don bata ma san me zata ce masa ba at this point, ya dago kanta yana kallonta yayi kasa da murya yace "Say something pls" Da kyar muryarta na rawa tace "Ban san me zan ce ba" Yace "Say anything" Shesshekan kuka ta fara yi masa tana jin zafi a zuciyarta, me kuma yake son ta ce masa, tunda yace bazai ta
a rabuwa da ita ba ko me zai faru, meaning dole ko tana so ko bata so haka zata ci gaba da rayuwa da shi a matsayin mijinta, so me yake son ta ce, ta dai dake da kyar har sannan muryarta na rawa tace "Kawai alfarma daya zan nema wajenka" Murya can kasa yace "Say it Khaleesat" Tayi karfin halin cewa "I don't want you to hurt anyone because of me...." Kasa ci gaba tayi tana kuka a hankali, ya dinga kallonta don sarai yasan su wa take nufi, Calmly yace "Ohk u mean ur Body Guards that sue me?" Ita dai kuka kawai take, Ya
an yi wani murmushi yace "I don't think i will leave dem cause they started everything first, they intruded in what wasn't der business, basu baki labarin harbin da aka yi ma wani dake da alaka da su ba, I mean Salem..." Khaleesat ta daga kai da sauri ta kallesa hawaye na sauka idonta gabanta na faduwa, lkci daya ta tuna sanda Aunty Farida ke sanar mata Ajay yace mata an harbi wani abokinsu a kano, yana wani murmushi yace "To su ma ana nan ana targeting din su, amma in kince in kyalesu i will do that under 2 condition..." Khaleesat dai kallonsa kawai take ta kasa cewa komai duk jikinta yayi sanyi, yace "The first condition is that.... zaki yi magana ta waya da su ki gaya masu ke za ki zauna da mijin ki they should back off, sannan ki gaya masu su janye karan da suka kai kotu..." Bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba, ya dinga kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Baza ki yi ba kenan?" Muryarta na rawa tace "Ban ce bazan yi ba" Wayarsa ya dauko ya mika mata yana kallonta, da kyar tace "Bani da number ai" Yace "Amma aunt dinki na da shi ai...

Call her and ask her to send you the number" Ta girgiza masa kai tana jin kamar numfashinta zai dauke sbda rikicewan da tayi bayan ya fadi conditions dinsa, cikin kuka tace "Bani da numberta offhand" Yace "Ni ina da shi, i will call her now sai ki gaya mata ta turo maki number daya daga cikinsu, and mind you kada ki kuskura ki ce mata komai, number kawai zaki yi requesting ta turo maki" Ta fashe masa da kuka sosai tace "Why are you doing this plss Ya Abdul" Yace "Ohk, i will revenge and nothing is gonna stop me, i promise you this, shi abokinsu da aka harba ai yayi surviving, i hope they survive too....." Tana kuka sosai tace "No plsss..." Wayar ya dauka yayi dialing number din Aunty Farida yana fara ringing ya mika mata yana kallonta.
[6/17, 7:43 PM] khaleesat Haiydar
: Har Aunty Farida ta
aga kiran Khaleesat bata amshi wayar da Abdul ke mika mata ba hawaye na zuba idonta, lkci daya ya hade rai yana mata wani irin kallo, babu shiri ta amshi wayar hannunta na rawa, a sanyaye tace "Aunty" Cikin rikicewa Aunty Farida tace "Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta tayi shiru, hankali tashe Aunty Farida tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Khaleesat kina ji na?

Don Allah kiyi magana, Hello Khaleesat" Khaleesat ta kasa ce mata komai hawaye masu zafi na sauka idonta, kiris ya rage ta fashe mata da matsanancin kuka a wannan lokacin, Abdul ya fixge wayar yayi a hannunta ya katse yana mata wani mugun kallon da ya tsorata ta sosai yace "Are you daring me?" ta fashe masa da kukan da take dannewa tana girgiza masa kai, a fusace yace "Ohk then, since abinda kika zabar masu kenan to ina me tabbatar maki zan aikata hakan nan ba da jimawa ba kuwa, sannan bayan nayi zan sanar maki, don bani da imanin kyale duk wani mahalukin da yace zai shiga hurumina, i don't mind sending that person to his early grave, and mind you.... i will so deal with them yanda in their next life baza su kara shisshigi akan abinda bai shafesu ba, if you think i am bragging watch and see, bani da conscience...." Khaleesat ta girgiza masa kai cikin karfin hali tace "Duk ba sai ka masu komai ba, zan yi abinda kace" Wayar ta amsa a hannunsa ta cire a Flight mode din da ya saka sannan ta sake dialing number Aunty Farida, yana fara ringing Aunty Farida ta daga da sauri tace "Khaleesat, kina ji na Khaleesat??

Hello" Khaleesat ta dake ta hadiye sauran kukanta cike da karfin hali tace "Na'am Aunty" Cikin tashin hankali Aunty Farida tace "Kina ina Khaleesat?" A hankali Khaleesat ta daga kai ta kalli Abdul taga ya wani murtuke fuska yana kallonta kamar bai ta
a fara'a ba a rayuwarsa, ta sunkuyar da kanta wasu sabbin hawayen na zubo mata cikin sanyin murya tace "Aunty Number Ahmad za ki turo min yanxu plss" Aunty Farida da duk ta rude tace "Ahmad kuma Khaleesat?

Wanene Ahmad?
Chapter 95 · 0% Book details