← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 167

Sashe 117

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Khaleesat na zaune gaban Coal pot wajen karfe sha biyun rana tana ta fifita gawayin da ta hura zata dora girkin rana at the same time tana gyara waken farantin dake cinyanta, Ummanta ce zata dora girkin don Aunty Farida ta fita kasuwa shi ne ta amshi girkin tace zata yi, shinkafa da wake da mai da yaji ne za su yi da rana, babu kowa a gidan sai ita da Umma don su Mama Zubaida da Mama Shatu sun tafi gidan biki ko girkin siyarwa basu yi ba ranan, Umma ma gidan Nenne take shirin zata je ta kai mata kubewan da ta tambayeta ranan friday,
aga kai Khaleesat tayi jin sallaman Safiyyah a compound din su, ta dinga kallonta bata ko kiftawa don bata ce mata zata dawo yau ba, Safiyyah tayi murmushi ta karasa har inda take sannan ta dau kujeran tsugunno da ta gani a tsakar gidan ta zauna tana kallon Khaleesat tace "Sannu da aiki" Khaleesat ta
an bude ido tana murmushi tace "You didn't tell me you were coming today Safiyyah" Safiyyah tace "Eh nima ban zata zan zo yau ba, dama ranan Monday ko Tuesday nace maki zan dawo ai" Umma ce ta fito daga dakinta, Safiyyah ta gaisheta da ladabi, Umma ta amsa da fara'a tace "Ya su maman ku?" Safiyyah tace "Sun ce in gaishe ku Umma" Umma tace "Allah sarki, to ina amsawa, bari in je gidan Nenne in dawo yanxu" Safiyyah tace "To sai kin dawo Umma" A haka Umma ta fita daga gidan, Khaleesat ta dora ruwan girkin ta ajiye waken da ta gyara sannan suka shiga dakin Umma da Safiyyah, Safiyyah na kallonta tace "Don Allah ki daure ki dinga cin abinci Khaleesat, kin ga yanda kika rame kamar ba ke ba kuwa" Murmushi kawai Khaleesat tayi tace "To ni dama kiba gareni Sophie?" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Even though, yanxu raman tayi yawa wallahi, ji fa sai idanuwa da dogon hanci kawai" Dariya kawai Khaleesat tayi bata ce mata komai ba, Safiyyah na kallonta tace "Ba dadewa zan yi yau ba Khaleesat, aikoni aka yi wajen ki" Da mamaki Khaleesat ta dinga kallonta, sai kuma tace "Wajena kuma?

Wa ya aiko ki" a hankali Safiyyah tace "Ur Housemate" Sosai gaban Khaleesat ya fadi ta dinga kallon Safiyyah babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace "Sai dai kiyi hakuri, ni dai na gaya masa abinda ya faru, And...." Sai kuma Safiyyah tayi shiru, Ita dai Khaleesat kallonta kawai take don ta kasa cewa komai tana jin hawaye na taruwa gradually a idonta, a hankali Safiyyah tace "He sent me money for ur flight ticket back to America, and you tuition fee for this semester, ya ce zai samar maki wani apartment din for the one year that is remaining for us...." Hawayen dake makale idon Khaleesat ya zubo, ta kasa ce ma Safiyyah komai, bata san sanda ta fashe da kuka ba sosai, ita dai Safiyyah tayi shiru tana kallonta cause she wasn't expecting less, sai da Khaleesat tayi kukanta me isarta sannan tana girgiza kai muryarta na rawa tace "I don't think za a bari in koma in ci gaba da karatu Sophie" Safiyyah tace "Ban gane ba?

Saboda me baza a bar ki ba?" Khaleesat na goge idonta da kyar tace "Saboda Abdul ma da aka bari ya kai ni karatu babu yanda za mu yi ne hakan ta faru, we had no choice then, dalilin haka har sai da Ummata ta samu hawan jini, kin ga yanxu kuwa ai babu wani hujjan da zai sa a sake barin wani ya ci gaba da sponsoring dina a wata kasar" Safiyyah tace "I don't understand Khaleesat, yanxu me kike nufi?

So kike kiyi asaran shekarun da kika yi a makarantar kenan?" Hawaye na zuba idon Khaleesat ta girgiza mata kai tace "A'a Sophie, but iyayena za su ji tsoron sake yarda wani ya dau dawainiyata try to understand me" Safiyyah tace "Zan jira har Umma ta dawo daga gidan Nenne in mata magana, ke kam bani da sauran magana dake, cause haushi zaki ci gaba da bani idan na biyeki, banda haka ta yaya ga dama ta samu amma kina neman misusing opportunity din, did you even know what you are saying?shekara daya kacal fa ya rage maki Khaleesat?

Dropout kike son ki zama ko me?

Ai wani abun mutum ba shi yake bargaining ma kansa hakan ba, you never bargained for all this Khaleesat, situation ne kawai, kina tunanin har a tashi duniya akwai ranan da Yaya Jawwad zai bude baki yace ai ya dau nauyinki a makaranta?

Kina ganin Jawwad yayi kama da mutumin da zai maki gori wataran?

Ai wallahi daga shi har Cousin dinsa sun girmi hakan, they are too classy for that, Kin zata kowa mahaukaci ne mara aikin yi kamar Abdul?

Haba wallahi har kin bata min rai, ban ta
a tunanin zaki nemi kiyi turning down din offer dinsa ba, shi fa taimako kawai yayi saboda yana da halin yin hakan, duba da kin kusa gamawa kuma yasan duk abinda ya sameki, amma sbda rashin tunani irin naki kina neman gwalesa, i was thinking zaman da kika yi da Abdul zai sa ki
an canza wasu tunaninki marasu ma'ana, ko kuma in ce Childish tunani" Ita dai Khaleesat hawaye kawai take sosai ta kasa ce ma Safiyyah komai, tasan duk bayanin da zata mata bazata ta
a fahimtar ta ba, Safiyyah ta ciro wayarta ta fara dannawa bata sake ce ma Khaleesat komai ba don da gaske ta
ata mata rai, after a while Khaleesat ta mike zata je ta wanke wake ta zuba a ruwan da to dora kan wuta, bayan ta gama wanke waken ta zuba ta rufe tukunyar tayi tagumi tana zaune gaban Coal pot din, a haka Umma ta shigo gidan ta sameta, Khaleesat ta sauke hannunta daga tagumin da tayi tana kallon Umma da ta nufota, tace "Umma kin dawo" Umma tace "Na dawo, ina Safiyyar?" Khaleesat tace "Tana ciki" Umma tace "Shi ne kika bar ta ita kadai" Khaleesat tace "Yanxu na fito in zuba wake ne" Aunty Farida ce ta shigo gidan da abubuwan da ta siyo a kasuwa, Umma tayi welcoming dinta sannan ta karasa dakinta ta shiga ciki da sallama, Safiyyah ta amsa tana mata sannu da zuwa, Umma ta cire Nikab da hijab dinta ta linke tace "Bata baki ko ruwa ba?" Safiyyah tayi murmushi tace "Umma ni ke nake jira ma tafiya zan yi" Umma ta zauna tana kallonta tace "To gani Safiyyah, lafiya dai ko?" Safiyyah tace "Lafiya lau Umma" Kafin Safiyyah ta ce komai Aunty Farida ta shigo dakin, Safiyyah ta gaisheta tana murmushi, Aunty Farida ta ajiye kayan hannunta tana amsa gaisuwan Safiyyah da fara'a, Umma dai kallon Safiyyah take tana jiran jin abinda zata ce, Babu bata lokaci Safiyyah ta fara yi ma Umma bayanin duk yanda suka yi da Housemate din Khaleesat, ita dai Aunty Farida na tsaye ita ma tana sauraron bayanin Safiyyah, Umma ta
an yi murmushi bayan Safiyyah tayi shiru tace "Allah sarki, mun gode sosai da kulawan sa, amma dai ki maida masa kudinsa Safiyyah, don ko babanta ma bana jin zai yarda, Abdul ma da ya kai ta karatun ba mu da yanda muka iya ne Safiyyah, Allah ya amfana abinda ta samu" Safiyyah was speechless, Aunty Farida ta dinga kallon Umma jin abinda tace, can tace "Allah ya amfana abinda aka samu kuma Umma?

Shikenan fa tayi asaran karatun gaba daya idan bata karasa ba, kamar ka fara gini ne fa ya ruguje har kasa ya rage Foundation, ai kin ga kuwa baza kace Allah amfana abinda aka samu ba" Umma ta kalli Aunty Farida tace "Farida kin fi kowa sanin ban ta
a goyon bayan fitar Khaleesat karatu waje ba tun asali, daga ni har mahaifinta babu yanda muka iya ne, don haka Khaleesat bazata koma Amurka da sunan karasa karatu ba, ashe ma bamu dau darasin abinda ya faru a baya ba kenan" Aunty Farida bata sake ce ma Umma komai ba ta hau fiddo abubuwan da ta siyo a kasuwa, Ita ma Safiyyah tayi shiru don bata ma san me zata ce ba, Umma na kallon Safiyyah tace "Ki masa godiya kawai ki mayar masa da kudinsa Safiyyah, Allah ya dubi niyyarsa na alkhairi ya saka masa, ba wai ni kadai ba, hatta Mahaifinta ma ba yarda zai yi ba Safiyyah, cutar da ita da muka yi da farko ma da muna da wani dubaran da baza ayi haka ba, kin ga in mu iyayen arziki ne ai baza mu yarda ayi na biyu ba" Aunty Farida ta mike tace "To shi Umma ce maki yayi da wata manufa zai biya mata kudin karatun har kike tunanin za ayi na biyu?
Chapter 117 · 0% Book details