Sashe 125
Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
A gaban nawa ku ke wannan rashin hankalin?" Magana yake yi at the same time yana kai kawo yana dube duben makullin dakin Safiyyah a parlon, Ita dai Khaleesat na rakube jikin kujera taji kanta har ya fara mata wani azababben ciwo, banda rashin option me zai kawota gidan nan ita kam, tunanin hakan yasa ta ji hawaye ya cika idonta, Safiyyah sai girgiza kafa take tana hararan Surayyah da ta koma ta zauna tana cin Popcorn dinta tana gyara daurin ture kaga tsiyan dake kanta tana kara cokarosa gaba, Mustapha ya karasa inda Aslam ke kwance yana bacci a parlon ya fara tashinsa yana tambayarsa makullin dakin Safiyyah, yaron da ko shekara biyu bai karasa ba, a fusace Surayya tace "Wallahi kar ka tada min yarona Mustapha, shi yasan maka wani makulli da zaka tashesa yana bacci" Mustapha ya juya ya kalleta yace "Surayya in ke kika dauke makullin nan ki fito da shi bana son rainin hankali" Surayya ta wani hararesa tace "Kar ka bata min rai this early morning, in dau makulli inyi uwar me da shi?
Plss do not provoke me Mustapha" Tana kai wa nan ta mike ta figi yaronta dake bacci ta nufi dakin ta da shi, Mustapha ya kasa cewa komai ya bi ta da kallo yana rike da waist dinsa, can ya juya ya kalli Safiyyah dake masa wani mugun harara kamar zata kwadesa, karasawa yayi kusa da ita yace "Look Safiyyah...." Katse sa tayi a fusace tace "Babu abinda zaka gaya min Yaya, Don't tell me anything, dama don matarka ta min wannan walakancin ya sa ka dage sai na dawo an koma makaranta, wallahi ni dai Daddy zan kira a samar min wani gidan da zan zauna in karasa final year dina kawai in peace, don bazan iya zama da wannan devil wife dinka a gida daya ba" Kamar zata yi kuka ta kare maganar, Mustapha bai iya yace mata komai ba, can dai ya nufi hanyar dakinsa don daki uku ne a gidan, yana shiga dakin ya dau duk abinda zai bukata ya fito da shi parlor ya ajiye yana kallon Safiyyah yace "Ga bedroom dina can ku shiga" Safiyyah na jin haka ta figi hannun Khaleesat zuwa dakin nasa, da sauri Surayya ta fito daga dakinta don bata kulle kofar dakin ba saboda ta dinga jin abinda za ace a parlon, tana kallonsa da wani irin mamaki tace "Ban gane ga Bedroom dinka can su shiga ba Mustapha, turakar namu za su shiga kake nufi ko me?" Safiyyah ta kwashe da wani dariya har da kyakyatawa ta ja Khaleesat suka shiga dakin sannan tayi banging kofar ta kulle, Surayyah zata yi magana Mustapha ya
aga mata hannu fuska a murtuke alamar baya son jin komai sannan ya fice daga parlon zai shigo da sauran akwatunan su Safiyyah, Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi ta dinga kallon Safiyyah tace "Haba Sophie, this isn't proper mana, why not mu zauna a parlor har san da za a ga makullin dakin naki, dakinsu ne wannan fa" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Ai ba kowa ne
an iska mara zuciya kamar ki ba Khaleesat, kuma wallahi ina dakin nan babu inda zan je har sai ranan da ta fito min da makullin dakina...." Khaleesat ta kasa cewa komai don da gaske she is shock, sai ga Mustapha yayi knocking kofar dakin sannan ya ajiye masu hand luggage dinsu yace "Me za ku ci yanxu?" Safiyyah na zaune gefen gadonsa fuskarta babu walwala irin ita an bata mata din nan tace "Kawai shayi da cookies kafin gari ya waye" Yace "Ohk" Juyawa yayi ya fita daga dakin ya kullo masu kofa, har sannan Surayyah na tsaye inda take a parlor ta kasa motsin kirki, ta bi sa da kallo har ya shiga kitchen zai hado masu shayin, bata san sanda ta fashe da kuka ba tana rufe bakinta ta nufi dakinta da sauri, Mustapha ya dawo dakin nasa da Cup din shayi biyu da cookies ya ajiye masu ya fita....
Khaleesat na idar da sallan Asuba ta kwanta kasan carpet din dakin Mustapha don dakin da dumi saboda room heater dake kunne, amma hakan bai hanata dinga jin sanyi ba saboda wankan da tayi, babu yanda Safiyyah bata yi da ita ta kwanta saman gado ba amma Khaleesat taki tace kasan carpet din ya isheta, wayar Safiyyah ya fara ring, ta mike ta dauko handbag dinta ta ciro wayar, kallon Khaleesat tayi tace "Housemate dinki ne ke kira" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah ta zauna gefen gado sannan tayi picking call din tayi masa sallama tare da gaishesa, daga daya bangaren yace "How are you, naga baki yi replying message da na maki ba tun jiya" Safiyyah tace "Kawai bana son inyi stressing dinka ne probably kace zaka zo picking din mu a airport" Yace "Kuna ina yanxu?" Safiyyah tace "Muna gidan yayana, ga Housemate din ka nan, let me give her the phone...." Calmly yace "Ohk..." Safiyyah ta mike ta tafi inda Khaleesat ke kwance ta durkusa tana mika mata wayar, Khaleesat ta kasa amsan wayar, har sai da Safiyyah ta kai mata wayar kunne, daga daya bangaren Khaleesat taji yace "Halysaah...." Kasa ce masa komai tayi, lokaci daya taji hawaye masu zafi sun fara sauka idonta, a hankali yace "Can you hear me?" Muryarta na rawa da kyar tace "Uhm" Shiru yayi, after some seconds yace "I will come over later in sha Allah" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, kashe wayarsa yayi, ta ajiye wayar wasu hawayen na sauko mata, ita dai Safiyyah bata ce mata komai ba.