Sashe 85
Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ku yan unguwan nan tsabar munafurci da gulma bakwa tashi shigowa sai iftila'i ya faru sannan ku bi ku cika ma mutane gida ko wacce da warin jikinta, farin cikin iftila'in ku ke ko menene haka?
Doo Allah duk ku fita ku ba mutane waje mu ji da daya, ai ba kanmu farau ba, en iska kawai magulmata" Rai bace ta nufi dakin Umma hannunta rike da jarkar manja daya hannun kuma rike da tocilan ta, ta tsaya daga bakin kofa tace "Zahra'u me suka dauka a dakin Alin da suka zo?" Umma da ta zauna gefen katifar ta tace "Shigowa ta kenan nima Nenne, na je gidan Baaba Gaje an sakota daxu da yamma" Nenne ta kalli kayan da su Islam ke shigarwa daki tace "Har dakin naki suka shiga ne?
To ni Usama ce min yayi iya dakin Ali suka shiga suka watso kayan ciki, ke kuma wa ya watso naki tsummokaran waje?" Mama Shatu tace "To shi da ya sulale ya gudu ya bar gidan ta yaya zai ce iya dakin Malam suka shiga?
Ai babu dakin da basu shiga ba a gidan nan yau, mu ma duk mayar da namu kayan mu ka yi, hatta babban jarkan mangyada da na siya jiya sun dauke, iya shi suka dauka a dakina, Ita kuwa Zubaida kwashin adashin da aka kawo mata suka dauke" Nenne ta fara matsar kwalla cikin rawan murya tace "Lallai na ga abinda ya isheni bai ishi Ubangijina ba, to yan fashi Awdul din ya aiko mana wannan karan?
Don dai duk mun san yafi karfin wani kudin adashin da bai taka kara ya karya ba balle wata jarkan mangyada, Allah mun gode maka da wannan rantsattsiyar jarabawan da mu ke ciki mun gode maka Allah, Alhamdulillahi ya Allah, Ina ga in ba tattarawa muka yi muka hakura da zaman birni mu koma kauye gaba daya ba muna cikin mummunan hatsari a Mariri gashi ba mu da gata, kar wataran cikin dare mun saki baki muna bacci su babbake mu, su babbake banza tunda babu me tsaya mana" Ita dai Umma tayi shiru bata ce komai ba, Nenne na kallonta tace "Su kuma samarin da suka sha uban fararen kaya suka zo mana nan suna kwambo dama yaudarar mu suka zo yi bamu sani ba, sun zo nan sun gama cika mana baki sai gashi tunda suka karkade wandonsu suka fita bamu sake ganin keyar su ba, to ina amfanin karya? har da ce min za a saki Ali kwanan nan ashe duk yan iskan gari ne makaryata bamu sani ba" Umma dai kallon Nenne kawai take, Nenne ta mika ma Islam jarkan manjan hannunta tace "Ba ruwana, wahalan da nake ta sha kan Ali ko shi ya halittoni duniya ai sai haka, kai kenan kullum ayi ta garkame ka kamar kasungumin barawo, sai kace wanda yayi ma Allah wani sa
on da bamu sani ba, saura kadan kwale kwalen da na hau jiya zan je nema masa taimako ya kife da mu banda Allah ya tsare, to ina dalili bayan ba shi kadai na haifa ba, in ya kasheni sauran su yi yaya? ke ungo amsa ki mika ma uwarki ta tsiyaya min manja, nawa ya kare" Islam tace "To ai an kwashe kayan abincin gaba daya Nenne" Nenne ta gwalo ido tana kallon direction din da aka ajiye kayan abincin taga wayam, bude baki tayi tana kallon Umma tace "Zahra'u ina kayan abincin?
Ko kasuwa ki ka kai kika siyar?
Fatarar taki ta kai haka Zahra'u?" Umma tace "Saboda me zan kai kayan abinci kasuwa in siyar Nenne, daga zuwa gidan Baaba Gaje in dawo nima na tarar an kwashe kayan abincin" Nenne ta ajiye jarkan hannunta a kidime ta saki salati tana tafe hannu tace "Baki kulle dakin bane Zahra'u?" Umma tace "In zan fita ai ina sa ma dakina kwado, to fasa kwadon aka yi, ga makullin ma a jakata" Nenne ta juya ta fita daga dakin dai dai shigowar Usama wani almajirin Malam Ali dake tare da shi tun yana da arzikinsa, kuma har yanxu dai yana tare da shi, Nenne na haska sa da tocila tace "Yauwa Usama kace iya wani daki mutanen suka shiga a gidan nan?" Usama yace "Iya dakin Alhaji kawai suka shiga" Nenne bata sake cewa komai ba ta nufi dakin Mama Zubaida don yafi kusa da ita, tana dage labulen dakin ta fara haske hasken tocila, sai kuma ta duka karkashin gadon karfen dake dakin ta hango carton din indomie biyu an tura su can ciki, ta kwalo ma Usama kira ya karaso da sauri tana haska masa karkashin gadon tace "shiga ka jawo min kwalayen taliyar yaran can" Ai ko ya shiga ya kwaso su ya fito da su, Nenne ta shiga cikin dakin tana duba bayan kyaure nan ma taga Babban jarkan man gyada ta sa Usama ya fiddo waje, ta gama duba dubenta a dakin bata ga wani kayan abincin ba sannan ta nufi dakin Mama Shatu, a bayan kyaure taga buhun shinkafa daya da quarter an lullube da zani, ta kwalo ma Usama kira shi ma ta saka ya kinkimo su ya fitar waje, a dakin Mama Shatu still taga kwalayen taliya da na maggi da jarkan manja duk ta sa Usama ya fiddo su waje, Nenne na kallonsa tace "Kwashe su ka mayar dakin Zahra'u Usama" Yace "To Nenne" Sai a sannan Nenne ta juya tana kallon su Mama Shatu da suka yi wuki wuki da ido ko wacce na kokarin diban ruwan alwala a buta, Nenne tace "An dai yi asara duniya da lahira, barayin banza barayin wofi, tirrr da halin ku, wato ga sabon jarin kayan abinci kun samu ko, tunda Zahra'un ta maida kanta er wahala warce bata san ciwon kanta ba, da ban ce a tsam min manja ba shiru zata yi maganar ta bi rariya ta bar ku da haram, ko zama da ku kadai ya isa ya dinga jefa Ali a masifa iri iri, ai ba kyau zama da jahilai shine kawai bai gane ba" Daga haka ta juya ta koma dakin Umma.
Khaleesat na bakin pampon dake compound din Aunty Farida tana wanke wanke, ita kadai ce a gidan gaba daya don duk sauran tenant dake gidan sun fita aiki, Aunty Farida kuma ta tafi kasuwa, juyawa Khaleesat tayi jin an bude gate, ta mike tsaye tana kallonsa, murmushi ya sakar mata ya rufe gate din ya karaso cikin compound din shi ma yana kallonta, ta sauke idonta a hankali tace "Sannu da zuwa" Yace "Good morning Halysaah"
an murmushi tayi ta sunkuyar da kai ta gaishesa sannan ta juya ta tafi ta bude masa kofar shiga parlon Aunty Farida tana kallonsa, yace "Aunty fa? ina ta kiran wayarta no response" Khaleesat tace "Eh ta bar wayar a gida ne ta tafi kasuwa" Ya kalli plastic chair dake veranda din Aunty Farida yace "Let me seat here ba sai na shiga ba, i just came to check on you" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "I really appreciate Housemate" Yace "To ki zauna mana" Ta kalli second chair din dake wajen sannan ta zauna, sake gaishesa tayi da ladabi tana kallonsa, yace "Lafiya lau Halysaah, how is ur body?" Tana wasa da gefen karamin veil din jikinta tace "Naji sauki" Yace "To amma naga kin rame, baki cin abinci ne?" Tayi shiru, yace "Baki ci ko?" Ta
an yi murmushi tace "Ina
an ci kadan" shiru ne ya biyo baya for almost 30 seconds, ta
an daga kai ta kallesa taga kansa a kasa, ajiyar zuciya ya sauke calmly yace "Everything will be alright soon in sha Allah Housemate" Nan da nan hawaye ya cika idonta, da kyar tace "But i don't know my mom's condition, i am really worried" Jay yace "Don't worry, Umma tasan kina nan, mun je can gidanku da Ajay, i assure you everything is fine back home do not worry ur self pls, yanxu dai we are working on clearing ur dad first before anything, soon in sha Allah he will be free from the debt" Hawaye na sauka idonta tace "To amma ni bazan iya zama da Abdul ba tsoron sa nake wallahi, kawai torturing dina zai yi yayi revenging abinda nayi masa, i am afraid" Jay yace "Do not be Housemate, we won't allow that happen in sha Allah, we will go to any extent na ganin hakan bai faru ba" Khaleesat dai tayi shiru tana share hawayen idonta, after some seconds yace "Baki tambayi Ajay ba?" Ta daga kai tace "Na zata tare ku ke yana waje" Jay yace "Not at all yana kano, bai ma san nayi tafiya ba, i took an early morning flight, zuwa 12 noon kuma zan koma kano in sha Allah, i just came to check on you" Khaleesat na kallonsa cikin sanyin murya tace "Nagode sosai, kuma naji dadi" Ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe sha daya saura yace "I will be leaving for the airport now kar inyi missing flight dina, kafin Ajay yayi noticing i am not home ya fara damuna da kira" Khaleesat tace "Ko ruwa baka sha ba, ko in kawo maka shayi?
Kilan ma baka yi breakfast ba ko?" Da damuwa tayi tambayar tana kallonsa, Yace "No i am okay Housemate" Wayarsa ne ya fara ring ya ciro yana kallon screen din yayi murmushi sannan ya nuna mata screen din taga Ajayn ne ke kiransa, mayar da wayar yayi aljihunsa sannan ya fiddo 100k ya mika mata yace "In case you need anything Halysaah" ta girgiza masa kai tace "A'a Nagode, bana bukatar komai wallahi" Mikewa yayi ya ajiye mata kudin a kafarta ya fita daga balcony din yace "Take care of ur self Housemate, idan na sake samun lkci ko zuwa nan da few days ne zan dawo in sha Allah, my regards to Aunty Farida" Khaleesat ta mike tana kallonsa ta kasa ce masa komai wasu sabbin hawayen suka cika idonta, ya daga mata hannu kawai ya nufi gate don bai ma son ganin hawayen nata, tana kallonsa har ya fita sannan ya rufo gate din, parlon Aunty Farida ta shiga ta zauna kan kujera ta rufe fuskarta tana rera kuka tana shessheka.....