Sashe 69
Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shekarun baya Malam Ali wanda shi ne mahaifin Khaleesat dreban babban mota ne, babu garin da baya zuwa da kaya a babban mota a fadin Nigeria, kuma motar tasa ce iyaka idan kana da lodi ya kai maka kayan ka har inda kake so sannan ka biyasa, har Nijar ya sha shiga da kaya daga nan Nigeria ta haka ma ya hadu da yayata Aunty Zahra'u warce ita ce mahaifiyar Khaleesat, don mu yan Nijar ne mahaifinmu har yanzu yana nan da ransa mahaifiyarmu ce dai Allah yayi ma rasuwa shekarun baya, to bayan ya auri yayata ya kawota Kano Nigeria ya ajiyeta cikin matansa biyu, bayan en watanni da auren shine na dawo wajen yayata tunda bata da kowa a Nigeria bata san kowa ba, nan rikona ya dawo hannunta a lkcn ina da shekara goma, tsangwama da kyara babu irin wanda ban sha ba a wajen kishiyoyin yayata, gashi bata iya ce masu komai tunda ita ma ba barin ta suka yi ba, mace ce me hakuri da kauda kai, in zanyi magana ma sai ta hanani, a haka ta samu makaranta ta saka ni tunda a can kasarmu ina karatu aka daukoni aka kawo mata, sai da tayi shekara biyar a gidan sannan Allah ya bata Khaleesat, Mahaifin Khaleesat na da rufin asirinsa sosai don haka bamu rasa komai a gidan ba sai zaman lafiya da kwanciyar hankali daga kishiyoyinta wani lokacin har da uwar mijin, jifa jifa mu kan kai ziyara Nijar gun iyayenmu da yan uwa da abokan arziki, bayan shekaru 12 da auro yayata a lkcn Khaleesat na da shekara bakwai sai abokan Mijin yayata da yan uwa suka dinga zugasa akan ya shiga siyasa ya nemi wani babban mukami zai samu tunda yana da jama'a sosai, kuma ba laifi yayi karatunsa, matansa ma suka dinga zugasa akan ya fito takara, yayata tayi kokarin ganin ta hanasa tunda bai rasa komai ba a sana'arsa ta dreban mota amma ya ki, haka nan ya daga babban motarsa ya siyar har da sabon gidan da ya fara ginawa a nan an Ladi na sidi, ya daga duk en kadarorinsa ya siyar ya shiga siyasa gadan gadan, duk matansa sai da ya biya masu Hajji suka tafi da mahaifiyarsa, ya kuma canza ma ko wacce kayan daki, ya ba kowa kudi a hannu, kusan mutane goma sha biyu ya biya ma Hajji a lkcn, banda matasan anguwa da ya dinga biya ma kudin makaranta, yayi ta facaka da kudi a karshe dai ya zo ya fadi zabe, duk wa enda suka dinga zugasa suka juya masa baya, Allah ya rufa masa asiri bai amshi bashin banki da wani abokinsa ke ta zugasa ya amsa ba kasancewar da zaben ya gabato bashi da kudi kuma a hannu, bayan faduwarsa zabe aka shiga yanayi na babu a gidan, cin yau da kyar na gobe da kyar ga yayata na da cikin yan biyu, dama gidan da yake haya me tsada tuni ya saki bayan kudin hayan sun kare muka dawo mariri gidan gadonsa da ya bari a walakance don saura kadan ya kyautar lokacin da yake campaign sai gashi gidan ya mana amfani ya rufa mana asiri, makaranta me tsada da yaran gidan ke zuwa duk ya ciresu suka dawo gida suka zauna babu karatu, iyayen basu yi dubaran mayar da su na gwamnati ba, duk muka shiga mawuyacin hali a gidan, sai sanda ya samu mota yake lodin kaya ya kai a biyasa, sanda babu mota kuma sai dai kowa ta ciyar da kanta a gidan, yana kuma fin wata da watanni bai samu ko da karamar mota ba, duk ka zo kofar gida zaka gansa a zaune babu abun yi shi ma duk ya fita hayyacinsa, tuni yayata ta siyar da kayan dakinta ta fara sana'a ina taimaka mata, ta kuma saka Khaleesat a makarantar da zata iya biya don Khaleesat ta taso da kwazo da hazaka ga ta yarinya ce me shiga rai ko don kalan fatarta, don a unguwan ma gidan buzaye ake kiran gidanmu, hatta Mahaifinta kiri kiri yake nuna yafi sonta a cikin sauran yaransa wanda hakan ya ja mata tsana da kyara a gun matansa da yan uwanta, ko sanda yake da mota a hannu tsaraba na musamman yake ma Khaleesat ko da bazai yi ma uwarta ba, ana haka yayata ashe duk cinikin da nake sai ta kwasa ta ba mijinta a boye ban sani ba, ga dai matansa duk da hali na babu da aka shiga a gidan basu bar yayata ba, kullum cikin hada mata tuggu da makirci ake wajen miji da uwarsa, cikin wannan yanayi yayata ta haifi yan biyunta wanda haihuwan da tayi na karshe kenan a gidan, a lkcn matsaloli har sun fi na da, jarin yayata ya karye kuma babu wani abu da zata siyar ta tada jarin, ga jegon yan biyu tana yi ga yunwa wani lkcn sai makota ke zubo abinci a kawo mata, iyayenmu a can Nijar ba masu karfi ba balle su taimaka mana, a haka na bi wata kawata zuwa nan garin Lagos tana siyar da abinci, kafin nan fa nayi aure har na fito, duka auren bai cika shekara daya ba, na auri wani abokin mahaifin Khaleesat, karayar arziki na samun Malam Ali na dinga fuskantar matsaloli gun mutumin da matansa uku wanda daga karshe ya sakeni dama ba saboda Allah yayi auren ba saboda kalan fata ta yayi, ina nan Lagos nake tallafa ma yayata da 'ya yanta uku, don bana son karatun Khaleesat ya tsaya duk da ta samu Foundation sosai sbda makarantar da ubanta ya sa ta ma a sanda yake da rufin asirinsa yafi na sauran yan uwanta tsada, na zo Lagos da yan shekaru yayata ta kirani wataran wai gashi an ba Baban Khaleesat babban mota har zai kai kaya kudu, matsaloli sun fara warwarewa tunda har an biyasa kudin kai kayan kuma kudade masu tsoka gashi har ya siya kayan abinci masu yawa ya ajiye a gida, tace in Maza in dawo gida kawai dama ita hankalinta ba a kwance yake da zamana a lagos ina sana'a ba, a haka ta takurani har sai da na dawo Kano, a sannan Khaleesat na da shekaru sha shidda tana kuma gab da gama secondary don da wuri aka sakata a makaranta, na dawo da wasu kwanaki ranan muna zaune tsakar gida da yamma sai ga mahaifin Khaleesat an shigo mana da shi ranga ranga ko motsin kirki bai yi, wanda duk gaba daya mun zata yana hanyar kudu har ya kusa Lagos, ga dai shi babu ko kwarzanen ciwo a jikinsa kuma wa enda suka kawosa suka ce ai daga asibiti ma aka taho da shi a can wajajen garin yarbawa, sannan kwanansa uku a asibiti aka sallamosa wasu mutane da suka shaidasa tunda dreba ne suka biya kudi aka sako sa a mota aka dawo da shi Kano, sosai hankalinmu yayi mugun tashi a wannan lokacin, sae da Malam Ali yayi kwana biyu a gida ana ta addu'a da neman taimako kafin ya farfado gaba daya har yana iya magana, nan fa yake sanar mana barayi ne suka kwace Trailer da kayan mutane a ciki bayan sun shaka masa wani farin abu, tashin hankalin da duk muka shiga bazai misaltu ba a lokacin, daga Trailern har kayan cikin trailern ya doshi miliyan dari da tamanin" Shiru Aunty Farida tayi tana goge hawayen dake zuba idonta, Jay that was shock ya kalli Ajay dake kallon Aunty Farida babu ko kiftawa jin zunzurutun amount din da ta kira, Aunty Farida na share idonta ta ci gaba tace "A ranan yan sanda sun kusa goma suka zo a motoci, a haka aka sa ma mahaifin Khaleesat ankwa ana jan sa kamar barawo aka fita da shi yaransa da matansa na kururuwa suna ihu, Khaleesat kadai ce bata motsa daga inda take zaune da littafi a hannunta ba sai hawaye kawai, duk aka cika kofar gidanmu babu masaka tsinke kai kace barawon gaske aka zo dauka, mun shiga tashin hankalin da baya faduwa a wannan rana, kuma duk mutanen da yayi ta biya ma Hajji a sanda yake da hali, da kuma mutanen da ya taimaka ma aka rasa wanda zai bi yaga inda ma aka kai sa, ashe daga kano Abuja aka nufa da shi, bayan dogon binkice aka gano trailern an yasar a wani gari an kuma juye duk kayan cikin trailern, dama me trailer daban, me kaya daban, adadin kayan cikin trailern kuma zai yi na miliyan dari, to ba kowa bane me kayan cikin trailern nan illa mahaifin Abdul, sam ba a yarda babu sa hannun Mahaifin Khaleesat a juye kayan cikin trailern ba, dama kuma yan unguwa na jin haushin ya samu lodi me yawa haka ya tafi kai kayan shi kadai ko yaron mota bai dauka ba, kuma ko wani dreba an san sa da yaron mota daya ko biyu, nan aka yi ta zuga baban Abdul akan kar ya yarda wai dama planning Baban Khaleesat yayi don ya ta a yi ma wani mutum haka da dadewa yace barayi sun kwace kaya a hanya sai yafewa mutumin yayi, kuma wai don yaga Alhaji Musa wato mahaifin Abdul me kudi ne sosai shi yasa zai cucesa yace an sace kaya tunda yanxu ta kare masa bai da komai, kuma wallahi sharri ne ba haka Baban Khaleesat yake ba, bai cin kayan wani baya ta a abu in ba nasa bane, beside bai ta a sanin Baban Abdul ke da kayan ba sai da iftila'in ya faru sannan yaga me kayan, shi dai kawai ance masa ga Lodi zai kai lagos ya kuma amince tunda sana'ar sa kenan kuma kullum fatan samun Lodi yake, ko da babu zugin yan anguwa baban Abdul bai yi kama da mutumin da zai iya yafe kudinsa ba don kana ganinsa kasan bashi da mutunci bashi da kirki, sai da Mahaifin Khaleesat yayi wata uku bamu sa shi a idonmu ba kafin aka dawo da shi kano duk ya rame yayi baki ya dawo kamar ba shi ba, da kyar aka bari muka gansa a fursin da aka ajiyesa na nan kano, ranan duk bamu yi bacci ba bayan mun dawo gida, yayata ta shiga tashin hankali mara