← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 167

Sashe 5

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Karfe goma saura na safe Khaleesat ta fito daga dakinta rike da wayarta don kar ma Abdul ya kira by mistake tayi missing call dinsa, tun jiya take makale da wayar duk don kar ya kira bata sani ba, kuma sau uku tana kiransa bayan da tayi sallan asuba bai daga ba still, yanzun ma da ta tashi sae da ta kirasa sau daya nan ma no answer, zaune taga new Housemate dinta a
an reading nook da aka tanadar a living Room din studying with a huge textbook dake gabansa, she had no idea ma ya shigo gidan, don bayan da tayi sallan asuba ta fito ta hada shayi ta sha da cookies a nan parlon sannan tayi karatu har zuwa bakwai na safe, daga nan ta shiga daki ta kwanta sai kuma yanzu da ta tashi feeling hungry, sau daya ya kalleta yana ci gaba da duba Textbook din gabansa yace "Good morning" Ta karaso cikin living room din a takaice tace "Ok" Ajiye wayarta tayi kan 1 sitter ta nufi kitchen, Ya daga kai yana kallon direction din da ta bi da harshen turanci yace "In baki yi breakfast ba, ga wani nan ki dauka....." Tsayawa tayi sai kuma ta juya ta kalli Centre table da yake nuna mata, ledan abinci ne kan table din duk da bata san wani kalan abinci bane a ledan, ta kallesa taga ya ci gaba da karatun da yake, girgiza kai tayi with no interest tace "No, tnx" Daga haka tayi wucewarta kitchen, ta fi minti uku tsaye kitchen din tana tunanin me zata yi, seeing her House mate sitted in the living room yasa ta zama uncomfortable to cook anything, hakan yasa kawai ta dauko kwalin cereals da bowl zata hada cornflakes, wayarta ta ji yana ring a parlor don tun jiya ta cire wayar a silent, bata san sanda ta saki both d bowl and the Cereal din hannunta ba ta fito daga kitchen din within few seconds, House mate dinta ya bi ta da kallo har ta nufi gun wayarta ta dauka da sauri, sai da gabanta ya fadi ganin Abdul ne ke kiranta, babu bata lokaci ta daga call din, zuciyarta na bugawa tayi masa sallama, jin shiru tace "Hello" kallon wayar tayi ta sake maidawa a kunnenta har sannan bata daina cewa Hello ba, House mate dinta dai ya ajiye Textbook dinsa gefe ganin yanda ta rude ya maida duk concentration dinsa akan ta, Khaleesat ta sake kallon Screen din wayar jin shiru Abdul ya ki ce mata komai kuma tana jin maganar mutane a background, marairaicewa tayi ta duka nan kasan living room din ta saka wayar a handsfree tace "I know u can hear me pls, don Allah kayi hakuri, i am making u this promise hakan bazai sake faruwa ba wallahi, don girman Allah kayi hakuri" Sai a sannan yayi magana da husky voice yace "Hold on to ur promise malama, sau biyar kenan kina missing call dina within a short period, are you out of ur senses or is anything wrong with ur brain?" Da sauri ta girgiza kai kamar zata yi kuka tace "Wallahi ina kitchen ina girki san da ka kira jiya, kuma...." Cutting dinta yayi yace "ke, bana bukatar jin komai daga gare ki, none of ur lies and excuses will convince me, naga kamar u are beginning to take me for granted this days....

Kinsan Allah kika sake missing call dina zaki sha mamakina wallahi cause it will take me nothing to be in America...." Hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Amma me yasa baka min uxuri?" Yace "Baza ayi uxurin ba, ni za ki gaya ma uxuri?

A kanki aka fara karatu?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Wato ke kin fi karfin ki bude baki ki bada hakuri ko" Kasa cewa komai Khaleesat tayi don tun da ta daga kiransa ta fara basa hakuri bata kuma san wani hakurin yake nufi ba, A takaice yace "Anyway, i called to warn you to stop disturbing me with unnecessary calls, na biyu kuma ki ja ma kawar
ki kunne she should never come into my DM and tell me nonsense again don zan dau mummunan mataki a kanta, ke kuma duk sanda yayi suiting dina i will call you, don't try calling my line again" Yana kai wa nan ya katse wayar, Khaleesat ta dinga kallon screen din wayar hawayen dake makale idonta ya gangaro, House mate dinta ya
an yi murmushi wanda iyakarsa lips after paying attention to their conversation, mikewa Khaleesat tayi tana share hawayen dake sauka idonta, sai a sannan ta lura da shi a parlon, dauke kai tayi da sauri bayan sun hada ido, gaba daya ta ma mance yana parlon, taji yace "Is that ur Father?" Wani kallo ta jefa masa tayi wucewarta dakinta wasu sabbin hawayen na zuba idonta, ruf da ciki tayi kan gadonta tana kuka har da shessheka, ta kusa minti arba'in kwance a yanda take, zuwa sannan ta dena kukan da take kawai ta lumshe ido, knocking din kofar dakinta da taji anyi at the same time aka bude ne yasa ta mike zaune da sauri don bata san bata kulle kofar ba, hada ido suka yi da new Housemate dinta, yayi dropping ledan hannunsa ya jingina jikin kofar dakin ya rungume hannu yana kallonta da kyau, calmly yace "Like seriously, Namiji kika kwanta kike yi ma kuka?" Ta wani hade rai ta kauda kanta zuwa wani direction din daban, how did he even know she understands Hausa?? yana juya counter din hannunsa as if counting his words yace "It's... funny" Ta juya ta kallesa har sannan fuskarta a daure tace "Excuse you, why will u barge into someone else's bedroom just like that?" Ya daga kafadarsa yace "Zan yi shisshigi in baki shawara ni dai, run for ur dear life cause u are dating a monster as a boyfriend" Yana kai wa nan ya juya ya fita daga dakin closing the door behind him, Khaleesat ta dafe kanta da yayi mata nauyi, daga karshe ta mike ta kulle dakinta da makulli sannan ta shiga bandaki, karfe sha biyu da yan mintuna ta gama shiryawa don wanka tayi, kallon ledan da ya ajiye mata tayi ta dauke kai sannan ta nufi kofa ta bude ta fita, satan kallon kofar bedroom dinsa tayi ta karasa living room, tana tafiya a hankali ta tafi kofar parlon ta murda taji a kulle an sa makulli, leka windon parlorn tayi taga babu motarsa a garage alamar ya fita, tana tafiya a hankali ta shiga kitchen, ta jingina da kofa tana kallon Cereal da bowl din da ta dauko daxu an ajiyesu kan cabinet din kitchen din, juyawa tayi ta fita daga kitchen din ta koma dakinta, ledan da ya ajiye mata ta dauka ta zauna kan kujeran dake dakin tana duba abinda ke cikin ledan, Breakfast Sandwiches ne sai fresh fruit smoothie a ledan.....
07087865788
[4/30, 5:36 PM] khaleesat Haiydar
: https://chat.whatsapp.com/KBwGIidDZY683SzzudJ0zc
HALYSAAH
By _Khaleesat Haiydar_
3.....

Bayan magrib Khaleesat ta fito living room saboda yunwan da take ji, har sannan bata ji alamar House mate din nata ya dawo gidan ba, gaba daya haka ta wuni ranan babu walwala, all of a sudden yau ta ji a zuciyarta ta fara gajiya da attitude din Abdul da abubuwan da yake mata, da ta tuna Housemate dinta overheard all her conversation with Abdul da kuma maganar da ya gaya mata sai taji wani bakin ciki da takaici ya tokareta at the same time tana wishing that never happened, zaunawa tayi kan kujera ta jinginar da kanta jikin kujeran ta afka duniyar tunanin rayuwarta, after a while ta sauke ajiyar zuciya ta mike tana tafiya a hankali ta shiga kitchen tana tunanin abinda zata dafa ta ci, absently ta fara wanke few utensils din da yayi amfani da shi ya bari a sink sannan ta kunna gas, stir fry pasta ta girka, bayan ta gama ta debi kadan da zata ci ta fita daga kitchen din, dai dai corridor din dakunan ta kusa cin karo da House mate din nata, a firgice tace "Innalillahi...." Sai kuma tayi shiru ta hade rai, ya koma gefe yana kallonta, har ranta taji tsoro don bata san yana gidan ba amma tayi pretending ta hanyar daure fuska, ya daga kafada ya bar wajen ta bi sa da kallon gefen ido.... reading nook dake cikin living room din ta ga ya nufa yana kwashe takardunsa dake kan table, ta dauke kanta ta shiga cikin dakinta ta kulle da makulli, karfe takwas da few minutes ta gama duk abinda zata yi ta dauro alwala sannan kwanta don gobe Monday tana da aji da safe, tana lumshe ido bacci ya dauketa.
Chapter 5 · 0% Book details