← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 167

Sashe 158

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

I am only admiring the ring, it look soo cute in your finger" Taki daga kai ta kallesa, ita kanta ta rasa gane wannan sabon kunyan nasa da take yi, ya jinginar da kansa da kujeran motar yana kallonta babu ko kiftawa, tunda taji yayi shiru tasan kallonta yake hakan yasa ko da wasa bata yarda ta dago kanta ba balle su hada ido, murya can kasa taji yace "Me yasa ni baki gaya min Ex dinki yaje wajenki a schl ba sai Ajay?" Shiru tayi jin tambayar da yayi mata, can ta dan kallesa, still speaking slowly yace "Why?" Tace "Ae ko an kira ka baka picking call dinka..." Yayi shiru yana kallonta kafin yace "Yaushe kika kira ban yi picking ba?" Ta langwabar da kai tace "Anytime i call, you don't pick" Jay ya sauke idonsa kasa, after some seconds yayi kasa da murya yace "I promise i won't do that again, i will prioritize ur call from henceforth yanda nake prioritizing na Mami da me martaba" Khaleesat ta daga kai suka hada ido, tayi saurin dauke idonta daga nasa, yace "Me yace maki da ya sameki a school din?" Khaleesat tace "Safiyyah ce ta kulasa suka yi exchanging words" calmly Jay yace "Do not worry Halysaah, i will bring an end to ur fright about ur Ex Husband very soon in sha Allah, i promise you this, zaki samu kwanciyar hankali fiye da yanda kike tsammani" Khaleesat ta kallesa, cikin sanyin murya tace "But i don't want you to confront him pls, he can be cunning" Jay ya
an yi murmushi yace "I am not confronting him Halysaah, kawai dai zan yi abinda zai yi cutting duk wani Intention din da yasa ya dawo yake bibiyan ki, i will put a total stop to that, kuma babu yanda ya iya haka nan zai hakura ko ba don Allah ba...." Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, After some seconds tace "Amma yanxu i will prefer inyi ma brother din Safiyyah magana to let me stay in their home har sanda zan gama exams, don bazan iya zama a apartment dina ni kadai ba kuma, i am very afraid" Jay yace "Kar kiyi inconveniencing dinsu Housemate, and I don't want you to be a burden to them considering the high cost of livelihood in this state.... ki zauna a apartment dinki kawai, i will be there also, i will be there to protect you...." Khaleesat tace "Zaka dinga zuwa kamar sanda muke former apartment dina?" Yayi murmushi yana kallon kwayar idanuwanta yace "Sure, anything for you Halysaah" Sosai taji hankalinta ya kwanta, cikin sanyin murya tace "To Nagode" Yace "Lokacin sallah ya kusa, can we go home now" Tace "Let me get my handbag" Gyada mata kai yayi, ta bude motar ta sauka, ya bi ta da kallo har ta shiga apartment din, after some minutes sai ga ta ta fito daga gidan da handbag dinta da waya, ta shiga motar ta rufe tana kallonsa taga kallonta yake....

Khaleesat na zaune dakinta wajen karfe takwas da rabi na dare suna WhatsApp call da Aunty Farida, gaba daya jikinta a sanyaye yake ga faduwar da gabanta yake ta yi jin abinda Aunty Farida ke gaya mata, labarin biyota da Abdul yayi har sabon Apartment dinta da kuma cikin makaranta take ba Aunty Farida, a nan ne Aunty Farida ke sanar mata ai yaje Mariri ma yafi a kirga few weeks ago kawai gaya mata ne bata yi ba don bata son daga mata hankali, Cikin sanyin murya Khaleesat tace "To Aunty ya aka yi yasan ina America ne?" Aunty Farida tace "In kin tambayeni in tambayi wa Khaleesat?

Kilan ko bincike yayi a unguwan aka gaya masa, kinsan babu abinda yan unguwan nan baza su yi ba akan kudi, dama kuma ga tsegumi ya masu yawa, in kuma ba a unguwan ya bincika ba kilan shi ma yaga hotonki da wannan mutumin da ya dora ki a Instagram" Khaleesat kamar zata yi kuka tace "Toh me yake so kuma a guna Aunty da yake bibiyana ne?" Aunty Farida tace "Mutumin da yana zuwa cewa yayi ya maida auren ku, Allah ya so Nenne ta zo ranan sai abinda ta manta ne bata gaya masa ba ta kusa tara masa yan unguwa, kuma tace ai kin gama iddansa tun wani shekara in ma yau ya farka bacci tun sanda ya sake ki to yaje ya duba calendar yaga yau shekara nawa da yayi sakin, Nenne ta sille sa tas, ni ai shi yasa hankalina bai wani tashi ba, da dai baki idar da iddansa bane shine babban tashin hankalinmu gaba daya, amma da baki da hakkinsa ai kinga Allah ya kada hankalinsa sai bayan da kika gama ya waiwayo ki, yana sake zuwa inda kike ki kira masa hukuman kasar kawai su ja maki layi da shi...." Khaleesat dai ta kasa cewa komai, Aunty Farida tace "Dama in kika ga ya hakura da bibiyanki ai sai in wani auren kika yi tunda babu tsoron Allah a ransa, ban ta
a ganin mara kunya ma irin sa ba, babu kunya babu tsoron Allah fa ya zo ya marairaice ma Babanki wai ya maida ke, ya zo gidan nan yafi sau goma wallahi, to Allah na tuba ko da ace baki gama iddansa ba da ba sai dai mu makasa a kotu ba akan ki koma gidansa, shi
an iska, danginsa matsiyata marasu mutunci" Khaleesat taji hawaye ya cika idonta tace "Toh Aunty ni tsoro nake kar ya sake cewa zai daukeni kema kinsan halinsa fa" Aunty Farida tace "A American zai dauke ki saboda ba shi da seti?" Khaleesat dai tayi shiru gabanta na faduwa don har yanzu bata mance yanda aka dauketa aka kai masa ita ba, tunanin hakan yasa hawaye ya fara zuba idonta, Aunty Farida tace "Yanxu dai ki kwantar da hankalin ki tunda kin ce Jarabawa za ku fara, su Junaid ma baza su bari ya cutar dake ba in sha Allahu, kiyi ta addu'a kina neman tsari daga sharrinsa, in sha Allahu Allah zai kare ki" Khaleesat ta gyada mata kai cikin sanyin murya tace "To Aunty" a haka suka yi sallama da Aunty Farida tana goge hawayen da yaki tsaya mata, kiran Safiyyah ne ya shigo wayarta tayi picking ta kai kunne, Safiyyah tace "Khaleesat kin san wa yayi ring din bell daxu kuwa?" Sosai gaban Khaleesat ya fadi tun kan Safiyyah ta gaya mata, Safiyyah tayi wani dariya har da kyakyatawa tace "Wallahi shi ne in gaya maki, Abdul ne ba wani ba, gashi nan an duba Camera na gansa, to da na bude kofar uwar me zai min ne?

Wato ban ta
a ganin
an iska mara aikin yi kamar sa ba, ki ji har yayi locating inda nake saboda rashin aikin yi, to me zai min da Allah bai min ba?" Cikin rawan murya Khaleesat tace "Kin dai ga abinda nake gudu ko, wallahi da baki kulasa ba Safiyyah, ba kowa ake musayar yawu da ba" Safiyyah tace "Wallahi ba abinda ya isa yayi min da izinin Allah, shi kuma yaya Musty idan ya gama bambamin fadan da yake yana cewa ina dauko masa magana a kasar nan sai ya daukeni mu tafi mu kai ma Cops report, sai an gano Abdul duk inda yake ya fadi abinda ya zo yi a apartment dinmu wallahi..." Tana kai wa nan ta katse wayarta, knocking din kofar dakin Khaleesat taji ana yi, ta juya ta kalli kofar har sannan zuciyarta na bugawa ta mike ta dau hijab dinta ta saka ta tafi ta bude kofar, sauke idonta tayi bayan sun hada ido, yana kallonta da damuwa ganin hawaye idonta yace "Are you crying Halysaah?

Me ya faru?" Kamar jira take ta jingina da kofar dakin ta fashe masa da kuka dama ta kwana biyu bata yi ba, nan da nan ta rikitasa a wajen.....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
*Ur evidence 07087865788*
https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM
Juyawa Jay yayi ya sauka downstairs don bai son yayi abinda zuciyarsa ke tunzura sa yayi a wannan moment din, yasan in ya ci gaba da tsayuwa yana sauraron kukanta a wajen the case will be totally different, sai da Khaleesat taga ya sauka kasa sannan ta dena kukan da take har lokacin tana jingine da kofar tana goge idonta a hankali, juyawa tayi ta koma dakinta ta dau laptop dinta ta zauna kan gado zata yi karatun wani course dinsu amma ta kasa karatun, sai kuma tayi tagumi tana kallon screen din laptop din babu ko kiftawa, after a while ta maida Laptop din gefe ta sauka daga kan gadon ta nufi kofa ta fita daga dakin, walking slowly ta fara sauka downstairs tana kallonsa, zaune yake kan kujera idonsa a wayar hannunsa, ya juya yana kallonta jin foot step dinta, har ta karaso karshen staircase din, ta sunkuyar da kai ganin kallon da yake mata, mikewa yayi ya nufeta yayi kasa da murya yace "Halysaah...
Chapter 158 · 0% Book details