← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 167

Sashe 137

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bai ma dau matarsa da muhimmanci ba in dai haka ne, who does that?" Safiyyah tace "Atoh, nima dai haka naji aka ce yana da mata amma ban sani ba ban kuma tabbatar ba" Khaleesat ta kalleta baki bude, Safiyyah tace "Wallahi kuwa, haka naji ana cewa, kuma wai yana da ciwon zuciya, ni dai bai min kama da me ciwon zuciya ba kuma ban ma yarda da wnn labari ba, kinsan yan mata na jin haushinsa saboda sai wanda ya ga dama yake kulawa shi yasa aka masa wannan sharrin, amma ki kalli mutum lafiyayye kamar sa a wani ce ciwon zuciya, gashi da son zuwa club" Khaleesat ta ma rasa abinda zata ce ma Safiyyah, kawai ta kauda kai don lamarin Sophie ya fara bata tsoro, the way she is saying it kamar bakinta da bakinsa suka yi magana ya gaya mata yana da ciwon zuciya kuma yana da mata, Safiyyah tace "Ni dai tashi mu je mu ci abinci yunwa nake ji, kilan ma haushin an sa shi ya cire hoton ne ya sa yayi banza da ni ta WhatsApp kuma na kirasa yaki picking, dama an masa shaidan girman kai and he is way too pompous of himself, bazai wuce Housemate dinki ya san sa ba shine yayi masa magana ya sauke hoton, dama ni fa sam gayen bai min ba ga wani jijji da kai da yake wai shi
an gidan Deputy sai kace
an vice president, deputy governors da ba a ma san da zamansu ba a Nigeria, gani yake yafi kowa a haka fa, kina kallon idonsa kinsan bazai rasa shan drugs ba" Khaleesat tace "Amma dai yanxu idan Abdul yaga hoton nan me kike tunani Safiyyah?" Safiyyah ta mike tace "Waye kuma Abdul?

Pls mu je mu ga abinda za mu siya mu ci yunwa nake ji wallahi" Har Khaleesat ta bar school ranan bata ga Ajay ya zo amsar wayarsa ba, hakan kuma yasa taji a ranta he is sick.

Mamaki abun ya ba Khaleesat ganin har ta dawo school Housemate dinta bai kirata ba ko kuma yayi mata magana ta WhatsApp, wayar Ajay ma bai sake kira ba, sai dad dinsa da ta ga ya kira wayar har sau biyu, da daddare taji zuciyarta ya kasa daurewa kawai tayi ma Housemate din nata magana via WhatsApp, ta gaishesa sannan ta tambayesa ya jikin cousin dinsa, after almost 15 minutes yayi mata reply da Alhamdulillah, daga nan kuma bai sake cewa komai ba, she was taken aback, haka nan ta ajiye wayarta kawai ta kwanta tana jin wani iri a zuciyarta.

Bayan kwana biyu Khaleesat da Safiyyah suna zaune a wajen department dinsu, Khaleesat na yi mata explaining wani course dinsu da tace bata gane ba, Murya can kasa taji Safiyyah na cewa "Ji gantalallen Aymaan din can, he is coming toward us, kar ki dago kanki" Khaleesat bata dago kai ba, ta ci gaba da bayanin da take ma Safiyyah, har ya iso inda suke zaune, calmly yace "Good evening Safiyyah and Khaleesat" Safiyyah ta washe baki tace "Hi Aymaan, how are you doing ya kwana biyu?" Yace "Lafiya lau, ya karatu?" Safiyyah na washe hakora tace "Alhamdulillah, tun ranan bamu sake haduwa ba sai yau" Yana kallon Khaleesat yace "Good evening Khaleesat" Ba tare da Khaleesat ta kallesa ba fuskarta babu fara'a tace "Ohk" Ya kalli Safiyyah yace "Naga kamar kawar taki a fusace take" Safiyyah tayi dariya da iyakarsa fuskarta tace "Ai bata ji dadin abinda kayi mata bane, duk da na fahimtar da ita ba da wata manufa kayi hakan ba, kuma ta fahimta, ita tsoronta ma kar matarka ta ga hoton" Yana kallon Safiyyah yace "Ke kika min auren?" Safiyyah tayi dariya tace "To ai kaga za a sa maku ido kuma shi yasa ta damu" Yace "Ohk in nasan haka ne ai da bazan sauke hoton ba, don wani guy that is full of himself i think saurayinta ne ya sameni yayi min magana about it, yasan ni, na sansa a kasar nan amma ba mu ta
a ma juna magana ba, had i know ban cire hoton ba in ga abinda zai yi" Safiyyah ta kwantar da murya tace "Kaga Aymaan Khaleesat fa matar aure ce babu wani boye boye...." Aymaan yayi wani murmushi without letting Safiyyah to go further yace "Ban yarda ba, shi wanda ya min magana in cire hoton zan nuna masa ba aurenta yayi ba ai...." Khaleesat ta daga kai fuska daure tace "Pls delete my pictures off your phone Mr man, don ban san ka ba, ban hada komai da kai ba ban kuma ga dalilin da yasa zaka yi posting dina ba, no sane person will do such, plss take my pictures off ur phone matar aure ce ni" Tana kai wa nan ta tura ma Safiyyah Laptop dinta ta mike ta figi handbag dinta ta bar wajen ko waigawa bata yi ba, Aymaan ya bi ta da kallo yana
an murmushi, Safiyyah tayi tagumi don har ta gaji da ce ma Khaleesat ta koyi siyasa da iya zaman duniya, da faram faram ya kamata ta samu ta rabu lafiya da Aymaan amma ga abinda tayi, Aymaan ya gyada kai yace "We shall see then" Safiyyah ta kallesa tace "Kasan tana da aljanu ne fa Aymaan kuma abun har ya ta
a brain dinta, da sauki ma basu tashi a nan ba, don wallahi duka take kuma in ta fara famfala gudu da kyar ake kamota, shi sa kullum zaka ganta babu fara'a ni kadai nake iya zama da ita wallahi, wanda kuma yasa ka cire hoton ba saurayinta bane believe me..." Aymaan yayi wani murmushi yace "Nima su gareni, kin ga dai dai kenan" Daga haka ya juya ya bar wajen, Safiyyah ta kara rafka wani tagumi.

Khaleesat na isa gida wajen karfe biyar zata bude kofa taji kofar a bude, ta kalli parking space taga babu mota a nan, tura kofar tayi a hankali ta shiga parlon, zaune ta gansa ya kunna TV yana kallon kwallo, ko juyowa bai yi ba har ta karasa cikin parlon tana kallonsa, ya mike without looking at her yace "Bani wayata" Tace "Ya jikin?" Sai a sannan ya kalleta yace "Nace maki bani da lafiya ne?" Tace "A'a kawai na gane idan baka da lafiya surutu that is not comprehensible kake yi a bacci....." Tana murmushi ta kare maganar tana kallonsa.
[7/11, 8:44 PM] khaleesat Haiydar
: Khaleesat ta bi sa da kallon gefen ido ganin ya nufi kofa, sai kuma ta juya tana kallonsa, fita ta ga zai yi daga parlon, da sauri tace "Ka jira in dauko maka wayar yana sama" Tuni ya fice daga parlon without looking at her, tafi minti biyu tsaye tana kallon kofar da mamaki, does this min yaji haushin abinda ta fada kenan?

To ai ita ba da wata manufa ta fadi hakan ba, tana ta tsaye parlorn with surprise, can dai ta ta
e baki ta karasa ta zauna kan kujera ta bude handbag dinta ta ciro wayarta tana duba pdf da aka mata sending a school na wani course dinsu, after a while ta mike ta tafi sama don yin sallah ta canza kayan jikinta sannan ta dawo downstairs ta girka abinda zata ci, Khaleesat bata sauko downstairs din ba sai kusan karfe biyar da rabi na yamma don tana sallah bacci ya dauketa saboda sanyin garin, tana gyara hulan kanta bayan ta sauko kasa zata shiga kitchen taji anyi knocking kofar parlor at the same time aka murda kofar, juyawa tayi da sauri after realizing ashe a bude ta bar kofar bayan Ajay ya fita daxu, kallonsa ta dinga yi babu ko kiftawa kuma ko kwakkwaran motsi bata yi a inda take tsaye tsabar yanda ta tsorata, ya kullo kofar yana tsaye daga nan bakin kofar yana kallonta yana murmushi with calm yace "Good evening Khaleesat" Khaleesat ta sauke idonta gabanta na wani mugun faduwa, her common sense didn't give her the go Ahead to be rude or anything of such to him, can dai ta kallesa with calm in her voice tace "Why will you badge into my House just like this?" Ya
an yi murmushi yana sauke hulan jacket din jikinsa yace "That was because u left the door open..." Cikin kwantar da murya tace "But that doesn't warrant you to badge in" Ya daga hannu sama yace "My bad, sorry about that beautiful Khaleesat" Zaunawa tayi kan kujera bata sake cewa komai ba faduwar gabanta ya tsananta, yana bin apartment din da kallo keenly yace "Such a nice apartment, Communal living kike, ko ke kadai ce a duk apartment din nan?" Ba tare da ta kallesa ba calmly tace "Co-living" Ya karaso cikin parlon tayi masa kallon gefen ido gabanta na faduwa sosai, zaunawa yayi gefenta yana kallonta yace "Sorry i came unannounced, banyi tunanin kina da fahimta haka ba, na zo gidanki ba tare da izinin ki ba and u are not mad at me, i even badged in but u are still calm...." Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace "It's fine...
Chapter 137 · 0% Book details