← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 167

Sashe 22

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Common WhatsApp kin dena min magana yanzu" Ta kasa kallonsa, tana wasa da gefen hijab dinta a hankali tace "To kwanan nan sai kayi ta min fada ta waya baka considering dina, ga kuma course dinmu da wahala ka sani" Ita kanta ta rasa dalilin da yasa hawaye ya cika idonta, He let out a sigh har a sannan yana kallonta, sai kuma ya dagota sitting her down by his side, gabanta ne ya fara faduwa, in da akwai abinda ta tsana kuma take fargaba a rayuwarta bai wuce Abdul ya zo America wajenta ba, duk da yawanci zuwan da yake it's either tare da Mom dinsa or his Dad, amma duk da haka a dar dar take da shi saboda wasu abubuwan da ya tsira wanda a baya baya mata haka, duk zuwansa kasar sai ta kirko wani abu da zai maidata unhealthy wani lkcn har sai an kai ta hospital, ita da tasan zai kamo hanya ya taho da bata fara ce ma Safiyyah tace masa bata da lafiya ba, yana caressing fingers dinta yayi kasa da murya yace "But you know i love you Khaleesah, ke ce kike jawowa nake maki fada a ko da yaushe" Ita dai bata ce komai ba hawayen dake makale idonta ya gangaro bisa kuncinta, ya kai hannu yana goge hawayen a hankali yace "Ohk, but you know i love you so much right?" ta gyada masa kai kawai, a hankali yace "Housemate dinki fa?

Is she around?" Sosai taji gabanta ya fadi, taki barin su hada ido tace "No ban sani ba, i saw she had a visitor daxu ya zo nemanta, probably her friend...." Yana kallonta yace "Friend?

Namiji kenan?" Khaleesat ta gyada masa kai, lkci daya ya hade girar sama da ta kasa yace "Yaushe ta fara kawo namiji gidan?

When did that start?" Khaleesat tayi karfin halin cewa "Dama tana kawowa time to time ai but not frequently, sai in kilan sun kawo mata reading materials ko bata da lafiya sun zo dubata" Yace "Kuma mazan na kwana a nan?" Khaleesat ta hadiye wani abu da kyar tace "Ni ban sani ba gaskiya, tunda ina dakina always a kulle ai" Kallonsa tayi to cu
t short the conversation tace "Na dafa noodles yanzu bari in kawo maka kar ya huce" Tana fadin haka ta mike da sauri zuciyarta na bugawa, dai dai nan Housemate dinta ya fito daga dakinsa, Khaleesat taji zuciyarta ya kusa shigewa cikinta tsabar kidimewa, tayi saurin dauke kai tayi hanyar kitchen, Abdul ya juya jin an bude kofar daki, hada ido suka yi da Housemate din nata da ya shigo parlon yana tafiya slowly waya kare a kunnensa duk da ba magana yake a wayar ba hannunsa daya rike da wani Textbook, idonsa kuma na kan Abdul, hannu ya daga masa calmly yace "Hello" Abdul ya bi sa da kallo babu ko kiftawa without replying to his Hello, shi dai Housemate din nata yana tafiya calmly ya nufi kofa ya fita daga parlon, tuni Khaleesat har ta shige kitchen hankalinta a tashe ta dafe kirjinta tace "Na shiga uku....." A haka dai ta fara zubo noodles din a plate, cike da karfin hali ta dawo parlon, Abdul dake ta kallonta yace "Who is he Baby?" Khaleesat ta
an yi fari da ido tace "Ni ban ma ta
a ganinsa ba sai yanxu, Nancy ya kawo ma littafi ina ga" Abdul ya mike yace "Ta yaya zaki dinga rayuwa under same roof da wani gardi Baby?

Yaushe Nancy din ta fara shigo da samari gidan nan?

All this while dama yana cikin gidan nan?" A hankali Khaleesat tace "Na fa ce maka ban ta
a ganinsa ba, i have never seen him before sai yanzu" Ajiye abincin hannunta tayi cike da karfin hali tace "In dafo maka black tea?" Komawa yayi ya zauna yaki cewa komai, kana ganinsa kasan he is boiling inside, ita dai ta juya tana tafiya kamar munafuka ta koma kitchen, mikewa yayi ya bi bayanta har zuwa kitchen din yace "Ta yaya wani banza can zai dinga shigowa yana kalle min ke anyhow Khaleesah?" A hankali Khaleesat tace "Ya Abdul kar ka manta communal living muke a gidan nan, this is America.... this isn't my apartment alone, bazan iya cewa ga wa enda za su shigo gidan ba tunda ba gidana ni kadai bace" Tsawa ya mata yace "And so what???

An gaya maki bazan iya kama maki hayar gidan ke kadai bane?

Banda kince kina tsoron zama ke daya a gida do you think u will be sharing an Apartment with anyone in America?

Do u think I can't afford a full apartment for you??" Har jikin Khaleesat ya fara rawa ganin how fiercely he was speaking to her yana huci, ga idanuwansa sun fara sauya launi, sosai take jin tsoron Abdul ita kam, hawaye ya fara gangarowa idonta muryarta na rawa tace "Ka fara kuma ko?" Kamo hannunta yayi fuskarsa a murtuke suka fito daga kitchen din, ta fashe masa da kuka a hankali har suka dawo cikin parlon, cike da fada yace "Ya bazan fara ba naga wani katon banza under same roof with you?

Me yasa tun tuni baki gaya min Housemate dinki na shigowa da gardawa cikin gidan nan ba in samar maki other alternative?

Me yasa baki da hankali baki da tunani ne ke a rayuwarki?" Zaunawa tayi ta fashe da kuka sosai ta hade kanta da kujera, ya zauna yana huci, ita dai kuka kawai take tana shessheka, after few minutes ya koma kusa da ita ya dagota drawing her closer to him kamshin turarensa ya cika mata hanci, nan da nan ta hadiye kukan da take tana zare ido, Gently yake caressing dinta murya can kasa yace "I am sorry Baby, amma da kin gaya min da na samar maki wani apartment din ai...." Ta fara kokarin komawa baya tana son kwace kanta daga hannunsa, kin saketa yayi a fusace yace "Why do u always act like a Bush gal Khaleesah?

Har yanzu rayuwar Ghetto bazai fita a kanki ba?

What is the meaning of this nonsense?" Ta ki barin su hada ido, da kyar tace "To ai...

This is a promise you made, amma kuma sai ka dinga..." Cikin tsawa yace "So f what if i break the promise?

Ko ance maki tsoronki nake ne?

Ko kuma wani ne zai aure min ke dama?" Ta marairaice masa kamar zata yi kuka tace "Ni dae bari in kawo maka black tea" zata mike ya fixgota har sae da fado kansa, ya fige hijab din jikinta yace "Naga alamar kin ma maida ni wani gara don kinga ina biye ki" Ta takure waje daya wasu hawayen na taruwa idonta taki yarda su hada ido tana kokarin kwatar kanta daga grip dinsa, skirt karami ne sosai jikinta sai half vest shi sa ma take ta yawo da hijab tun daxu da ta dawo schl, ya sake fixgota sosai jikinsa, kuka ta fara yi muryarta na rawa tace "Don Allah ka bari plss, this wasn't our deal, you are not keeping to ur promise" Kallonta ya dinga yi saboda yanda tayi provoking dinsa, duk da shi bai yi niyyar mata komai ba da ya wuce ya lallasheta amma tsabar yanda ta hasala shi sai ya fara kokarin kissing dinta,
in yarda tayi tana kiciniyar kwace kanta tana kuka, House mate dinta ne ya shigo parlon a lkcn, ya kalli yanayin da suke da kuma yanda take struggling din kwatar kanta daga jikinsa, direct ya nufi cikin parlorn har inda suke without a second thought ya cakumo Abdul yana kallonsa da kyau "Hey, this is America guy, what sort of molestation is this??" Mikewa Abdul yayi yana kallonsa da wani irin Expression na mamaki, bai yi wata wata ba kawai ya sauke masa fist dinsa a kirji har sau biyu, ya wani cakumosa yace "Are you insane?

How dare you??" Khaleesat ta zaro ido ta mike cikin tashin hankali ta riko Abdul tana zaro ido with shock, lkci daya ta kalli Housemate dinta da ya tsaya yana kallon Abdul baya ko kiftawa kuma bai yi attempting rama abinda yayi masa ba, da kyar tace "He is my boyfriend, I don't think u have any problem with this, who are you?

And where do you know us from?

You have no right to intrude!" Housemate dinta dake kallonta ya sauke idonsa kamar bazai ce komai ba, sai kuma calmly yace "My bad!

And i am sorry, i thought u were in danger, i am only here to drop some books, sorry about that plss" Khaleesat ta wani kallesa tace "Do i know u from anywhere that warrant u intruding?" Ya girgiza kai yace "Not at all...

I am sorry" Kallon Abdul yayi, bowing his head gently at the same time yace "I am sorry, dude" Daga haka ya ajiye book din hannunsa ya juya ya nufi kofar parlon ya fita waje, that was when Khaleesat realized she was half dressed all this while, dukawa tayi ta fara kuka a hankali ta hade kanta da kujera tana jin kanta na wani irin sara mata, wani kallo Abdul yayi mata yana huci, kawai ya dau wayarsa ya nufi kofa ya fice daga parlon kamar zae tashi sama, ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta, mikewa tayi da sauri ta nufi window tana duba waje taga babu motar Housemate dinta har ya tafi, sae Abdul da ta hango yana tafiya down the street, dawowa parlon tayi tana goge hawayen dake sauka idonta ta dau Hijab dinta ta wuce daki da sauri, har wajen karfe tara na dare Khaleesat ta kasa tashi daga saman darduman da take zaune ga wani ciwo da kanta yake mata, jawo wayarta tayi a hankali, tun daxu take son kiran Abdul amma ta kasa kiransa saboda tsoro, daga karshe tayi gathering courage tayi dialing numbersa har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma bai
aga ba, tasan ba lallai ya
aga ba dama, ajiye wayar tayi ta kwanta gefen gado wasu sabbin hawayen na zuba idonta.
Chapter 22 · 0% Book details