← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 167

Sashe 58

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

shi dai ya bi ta da kallo, Flight Attendance din da ta kawo mata Hot towel kafin tashin jirgin ne ta bi bayanta tana tambayar if she's okay, Khaleesat ta gyada mata kai kawai bayan ta fito daga Lavatory din, AJ ya bi ta da kallo har ta koma seat dinta ta zauna sannan ya tabe baki, Flight Attendance din ta duka kusa da ita tana tambayarta ko tana bukatar wani abu ne, Khaleesat ta girgiza kai tana murmushin karfin hali tace "Thank you, i am okay" Matar ta sake tafiya sai ga ta ta dawo da ruwa da orange drink, sai kuma wani drink daban duk a glass daban daban akan tray daya, ta duka tana mika ma Khaleesat ta dauki wanda take so, glass din ruwa kawai Khaleesat ta dauka ta mata godiya sannan ta sanar mata bazata ci abinci ba all throughout the flight don ma kar matar ta sake dawo mata, gani take tana cin abu zata yi aman da bata yi ba daxu, gyara kujeranta tayi ta kwanta ta lulluba da blanket din da jirgin yayi providing for business class passengers, nan da nan bacci ya dauketa, da za su sauka Turkey wajen karfe hudun asuba sai da wata Flight Attendance daban ta zo ta tasheta ta sanar mata jirgi zai sauka, Khaleesat ta mike zaune da kyar don ciwo kanta ke mata, tayi fastening seat belt dinta, bayan sun sauka Istanbul ta bi AJ da kallo har sai da ta daina hangosa sannan ta mike ta dau handbag dinta da waya ta bi bayansa tana tafiya da kyar leaving her Amenity kit behind, jiran awa biyu za su yi a Business Class waiting lounge na airport din kafin a canza masu jirgin da zai kai su Nigeria, ta riga AJ shigowa lounge din kilan masallaci ya tafi, ita ma tana ganin lokacin sallahn asuba yayi ta tafi tayi sannan ta dawo ta zauna a business lounge din, after like 15 mins sai gashi ya shigo, not far away from her ya zauna da ruwan gora a hannunsa, Ita dai ta jinginar da kanta jikin kujeran da take zaune ta daura handbag dinta a kafarta, she is having a terrible headache a lokacin, after almost 30 mins of sitting wani an Nigeria ya dawo kusa da ita ya zauna, wanda shi ma daga nan Turkey zai je Nigeria a Business class, kuma jirginsu daya kamar yanda ta ga ticket irin wanda ta amsa bayan sun sauka Istanbul din a hannunsa shima, yana kallonta yayi mata sallama cikin nutsuwa, ta an kallesa sannan ta amsa, yace "Guess you are coming from America right?" Tace "Uhm" Yana kallon Flight ticket dinta yace "Oops you are having the same name as my Mum, can i call you Jiddah instead of the real name?" Khaleesat dake sauraronsa without looking at him tace "Ohk" Yana murmushi yace "Alright, are you traveling alone Jiddah?" Ta girgiza kai tace "No" Ya buda ido yace "Ohk with who?" Ta kalli direction din AJ, shi ma mutumin ya kallesa suka hada ido don kallonsu kawai Ajayn yake yana jin conversation dinsu, mutumin na murmushi ya tashi yaje ya gaisa da AJ sannan ya koma ya zauna, shikenan Khaleesat ta samu lafiya, don bai sake ce mata komai ba kawai danna wayarsa yake tayi tunda shi dai bai san ko waye Ajayn a gunta ba, daga karshe ma ya tashi ya bar wajen, at last aka fara boarding din jirgin da zai kai su Lagos Nigeria daga Istanbul, Usman ya juya ya kalli Khaleesat da ta mike tana rike da handbag dinta, har AJ ya wucesu sai kuma ya tsaya amma bai juyo ba, ita dai tana tafiya a hankali har ta isa inda yake tsaye sannan ya ci gaba da tafiya tana biye da shi, har jirgi ya tashi Usman dake zaune not far from Khaleesat but close to AJ bai ce mata komai ba, this time around ma dai bacci kawai tayi har zuwa Nigeria.
Chapter 58 · 0% Book details