← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 167

Sashe 116

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan Azahar Khaleesat na zaune kan darduma da qur'ani a gabanta tana karantawa a zuci, sai ga Safiyyah ta shigo dakin Umma da sallama, Khaleesat ta rufe Al-qur'anin ta daga kai tana kallonta tana murmushi, ji tayi kamar all her worries are gone ganin Safiyyah, Safiyyah ta ajiye handbag dinta ta zauna edge din katifar dakin tana kallon Khaleesat a sanyaye, gaba daya ta kasa ce mata komai, Khaleesat ta mayar da Al-qur'anin Aunty Farida gefe sannan ta mike ta koma kusa da Safiyyah ta zauna tana kallonta har sannan murmushin fuskarta bai
ace ba tace "I miss you so much" Hawaye ne ya zubo ma Safiyyah a ido don kawai ta kasa daure hakan, Khaleesat ta sauke idonta kasa, sai ga hawayen ita ma a idonta, rabonta da zubda hawaye tun jiya a gaban Abbanta, bayan kuma ta shigo ta kwanta bata sake yarda tayi kuka ba duk da kusan yanda taga rana haka taga daren ga zafin da zuciyarta ya dinga mata, Safiyyah ta rungumeta tace "It's fine Khaleesat, Allah ya saka maki abinda yayi maki" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Safiyyah ta goge idonta don taga alamar kukan da take ne yasa Khaleesat kuka, Safiyyah ta dago kanta tana kallonta tace "Su Umma fa?" Khaleesat tace "Sun je gaisuwa ne anyi rasuwa dazu a unguwan" Safiyyah tace "Allah sarki, Allah ya ji
an musulmi" Khaleesat tace "Ameen, ya su Mama fa?" Safiyyah tace "Duk suna lafiya lau, tace in gaisheki, bayan mun gama waya daxu tace in kira mata ke, na sake kiran wayar Aunty Farida naji a kashe" Khaleesat tace "Ehh babu caji ne, ta bada a kai mata wajen caji" Safiyyah tayi shiru, bata son yi ma Khaleesat maganar da zai kara sa taji ciwo a ranta, amma duk da haka calmly tace "Saki nawa yayi maki?" Khaleesat ta buda manyan idanuwanta tace "Kawai ce min yayi ya sakeni" Safiyyah taji bakin cikin ba saki uku yayi mata ba, don ita ba kukan bakin cikin sakin da yayi take ba, a'a bakin cikin mayar mata kawa bazawara da yayi ne babban bakin ciki da takaicinta shi ne yasa har ta zubda hawaye, a gida ma kukan da tayi kenan don taji ciwon abun sosai, Khaleesat ta kalli inda Aunty Farida ta ajiye Envelope din da Drivern gidan su Abdul ya kawo tace "Ga ma can takardan ya aiko" Safiyyah ta juya ta kalli Envelope din, mikewa tayi ta dauko ta dawo ta zauna ta ciro takardan ciki, ita dai Khaleesat kallonta kawai take don har sannan bata duba abinda ke jikin takardan ba, daga Aunty Farida har Umma babu wanda yace mata saki uku ne, jiya kuma da Nenne ke ta hayaniya a tsakar gida bayan an kawo takardan Khaleesat na kwance duk bata san abinda ake ba don abubuwan da suka dameta daban, Safiyyah ta kalli Khaleesat da sauri tace "Saki uku ne ai a takardan" Khaleesat ta amshi takardan a hankali tana dubawa, after some seconds ta kalli Safiyyah tace "Wannan ai ba rubutun sa bane" Safiyyah ta hade rai tace "Do we care??

Ba dai shi aka kawo mana ba, kinga ai da shi za mu yi aiki, don da kika ce saki daya ne sai da gabana yayi mummunan faduwa don matsiyacin zai iya dawowa yace ya maida ke mu shiga uku, amma tunda ga takarda an rubuta saki uku a jiki shikenan an wuce wajen, Alhamdulillah" Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take, Safiyyah ta ajiye takardan ita ma tana kallonta, can a hankali Safiyyah tace "I don't understand you Khaleesat, ko dai bakin ciki da sakin da Abdul yayi maki ki ke?

Kin yi give up kan cewa zaki zauna zaman har abada da shi ne?

Pls let me know first so that i will watch my words" Khaleesat tayi murmushin takaici tace "Dukan yau daban, na gobe daban, zagi, hantara cin mutunci, living with hunger...." Kasa ci gaba Khaleesat tayi ta fashe da matsanancin kuka tana girgiza kai, Safiyyah ta rungumeta tace "Allah ya saka maki, Allah ya saka maki cikin gaggawa, in sha Allahu sai yaga karshensa tun ba aje da nisa ba, in sha Allah sai hakkin ki yayi tormenting dinsa har karshen rayuwarsa, komin lalacewan gidanku baza a doke ki ba balle a zage ki ko a hantare ki, uwa uba a bar ki da yunwa, In anyi duniya don manzon Allah sai Allah ya nuna ma Abdul iyakansa, wato punching bag ya mayar dake a gidan, kalli yanda kika rame kalanki ya disashe kamar ba ke ba, dubi yanda duk kika fita hayyacin ki, wallahi hakkin ki bazai ta
a barin Abdul ba, ki kwantar da hankalinki ki cire ko wani damuwa a ranki ki dau hakan a kaddarar rayuwarki" Kai kawai Khaleesat ke gyada mata hawaye masu zafi na zuba idonta, Sosai Safiyyah ta dinga bata words of encouragement tana kwantar mata da hankali, har Khaleesat taji sanyi sosai a ranta, taji ta samu relieve din abubuwan da suka tunkushe mata a rai tun jiya, a haka Umma da Aunty Farida suka dawo suka samesu, Umma ta ajiye masu
anwaken da ta siyo a makota sanin Khaleesat na son
anwake, ba laifi Khaleesat ta ci
anwaken me yawa tare da Safiyyah, dama duk yau ta kasa cin komai, ko farfesun da Nenne ta kawo mata ka
an ta iya ci, amma sai ga shi ta ci
anwaken sosai, sai kusan karfe shidda na yamma Safiyyah ta bar gidan, with the relieve that tayi consoling kawarta tunda gashi har tana dariya ta baro ta, sallan magrib kawai Safiyyah tayi ta jawo wayarta tayi dialing number Housemate, wanda rabon su yi magana tun sanda ya gaya mata abinda Khaleesat tayi masu shi da Ajay.
[6/30, 11:27 AM] khaleesat Haiydar
: Jay na zaune dakinsa wajen karfe tara na dare yana rike da mug din coffee da yake ta stirring for almost 5 minutes now ya kasa sha, ya daga kai jin an bude kofar dakin, Ajay ne ya shigo ya nufi inda Laptop dinsa yake, shi dai Jay kawai bin sa yayi da ido har ya kunna laptop din ya duka yana dube dube a cikinsa, after almost 2 minute ba tare da Ajay ya kallesa ba yace "Resend me those files u sent yesterday via Email" Jay bai ce masa komai ba, hakan yasa Ajay ya juya yana kallonsa, mikewa yayi ya nufesa, ya cire masa head warmer din kansa ya saka a nasa kan yace "Hey is everything Okay?

Me yasa baka fito ka ci abinci ba?" Jay ya mike ya fixge Head warmer dinsa sannan ya koma ya zauna yace "Kai dai ba ka ci ba, cire min Jacket dina Ajay, I can't remember dashing you the Jacket...." Ajay na gyara Jacket din jikinsa ya koma ya ci gaba da abinda yake yi a laptop din Jay, after a while Jay ya ajiye Mug din hannunsa, speaking slowly yace "I spoke to Safiyyah not long ago" Ajay ya kallesa yace "Wacece haka?" Jay yace "My Housemate's friend" Banza Ajay yayi masa ya ci gaba da duba abinda yake yi a laptop, calmly Jay yace "And she...." Ajay ya dakatar da shi sounding pissed off yace "Plss Jay, i am not interested, do not provoke me this night, banda file da nake nema a laptop dinka baza ma ka gan ni a dakin ka da daddaren nan ba" Jay ya mike yace "Whether you are interested or not, Safiyyah ta gaya min gayen ya saki Halysaah" Ajay ya juya ya kalli Jay babu ko kiftawa, after some seconds ya maida idonsa kan laptop din gabansa sai dai bai ci gaba da operating laptop din ba, Jay ya karasa kusa da window din dakinsa ya bude drape din ya rungume hannunsa yana kallon tiny snow din dake zuba kasa, Ajay yace "What did you expect?

Were you expecting less?

He's satiated his craving, and that is all that he is after, yayi satisfying Lust dinsa" Yana kai wa nan ya rufe Laptop din kawai ya nufi kofa ya fice daga dakin, shi dai Jay da ido ya bi sa kawai, can ya sauke wani ajiyar zuciya ya karasa ya rufe kofarsa da Ajay ya bari a bude.
Chapter 116 · 0% Book details