← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 167

Sashe 89

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina son sanin zaman me ku ke har yanxu a garin nan baku karasa gida ba?" Duk suka yi shiru babu wanda yace komai kansu a kasa, Calmy Abba yace "Ohk take ur time, amma kuyi kokari ku je gida kafin hutun ku ya kare, Secondly.... maganar da nayi da ku a Maryland naji babu wanda yace min komai a kai har yanxu, ga lokacin da na baku ya cika, nayi maku uxurin mantuwa shi yasa nake tunatar da ku yanxu..." Nan ma duk suka yi shiru babu wanda yace komai, shi ma Abban yayi shiru yana kallonsu yana jiran amsa a duk sanda suka shirya, sun san shirun da Mai martaba yayi amsarsu yake kira ko da zai dau 10min ko fin haka ma kafin su basa amsan he won't mind zai jira su patiently, sanin halin Abban nasa yasa Ajay ya daga kai, Softly yace "Ayi hakuri ranka shi dade ba mantawa muka yi ba, in sha Allah we are working on that very soon" Mai martaba yace "Is that so?" Ajay ya sauke kansa don kalman Abba na nufin bai gamsu da abinda yace ba kenan, Shi dai Jay yaki dago kai, a hankali Ajay yace "A gafarce mu a
an kara mana lokaci Abba..." Aunty da har ta fahimci maganar da ake ta
an yi gyaran murya ta nemi permission din magana gun Mai martaba, ya gyada mata kai alamar ta fadi abinda zata fada, cikin nutsuwa tace "In na fahimci maganar da ake ranka shi dade, magana ce akan su fito da matan aure duba da yanda shekarunsu ke gaba ba baya ba, wannan magana kuma ba sabuwar magana bace don an fi shekara 3 ana yin ta amma babu wani progress, a takaice basa daukar maganar da muhimmanci, to amma dai ina ga ka
an sha'afa ne ur Highness, don shi Jawwad ai akwai maganar sa da Hadeeyah a kasa duk da ba wai maganar tayi karfi bane kuma wannan hadi, hadi ne me kyau da zai kara karfafa zumunci don mahaifiyar Hadeeyah jininka ce kuma ita ta kawo wannan shawara duk da Fulani wato mahaifiyar Jawwad uwar dakinta ce tun asali, shi kuma Junaid a yanda na lura da shi zai fi maraba da zabin ka garesa duba da nature dinsa da rashin choice dinsa, don haka shi Jawwad a tsaida maganar sa da Hadeeyah kawai ina ga hakan zai fi, shi kuma Yarima i think we should get him a princess from neighbouring states, ko ni zan iya jagorantar hakan don arranged marriage zai fi suiting dinsa duba da nature dinsa, kuma ina son a bar komai a hannuna ranka shi dade..." Ajay ya daga kai ya kalleta zai yi magana mai martaba ya dakatar da shi, Ajay ya sauke kansa, Speaking Calmly Mai martaba dake kallon Ajay da Jay yace "Za ku iya tafiya, Allah yayi maku albarka" Sai a sannan Jawwad ya dago kai ya kalli Aunty dake
an murmushi ganin Mai martaba yayi na'am da shawaranta, tuni Ajay har yayi disappearing daga parlorn fuska a murtuke, Jay ya mike shi ma ya bi bayan Ajay yana tafiya a hankali, bai ta
a sanin baya son Hadeeyah da aure ba sai yau da Aunty ke bada shawaran a tsaida ranan aurensu da ita, yasan kuma duk abinda Aunty tace kamar Abba ya aikata hakan ya gama ne, kawai yaji hankalinsa yayi mugun tashi yaji wani zufa na keto masa, dakinsa ya shige ya kulle da makulli ya jingina da kofar ya lumshe ido zuciyarsa na bugawa, Ajay na shiga dakinsa shi ma ya kulle da makulli ya zauna gefen gado ya dafe kansa da hannu biyu, this is not the first time da Aunty ke kasalanda akan duk abinda ya shafesa gashi Abbansa baya basa listening ears ko me Aunty tace masa kawai haka za ayi abun nan komin munin abun, at this point he felt he is of no importance to his father, he felt dejected, and it's been like this for so many years, he have no one to stand for him, a hankali ya juya yana kallon wayarsa dake vibrate, Number Aunty Farida ya gani a gaban screen din wayar, ya kalli agogo yaga karfe shidda da minti biyar na safe, request din Khaleesat na jiya da ta kirasa ya tuna, hakan yasa har kiran ya katse bai daga ba knowing she might be the one calling, kiran ya sake shigowa ya kalli screen din nan ma bai daga ba har ya katse, sau hudu kiran na shigowa continuously, hakan yasa ya maida attention dinsa kan wayar ya
an yi jim with different thought running his mind, ganin kiran ya katse an sake kira making it the 5th time of calling yasa ya dau wayar ya daga ya kai kunne yayi shiru waiting to hear who is on the line, a hankali ya mike jin abinda Aunty Farida ke ce masa ta wayar, bai san sanda ya zame wayar daga kunnensa ba rate din heartbeat dinsa na karuwa, da sauri ya nufi kofarsa ya bude ya fice daga dakin ya murda kofar dakin Jay yaji a kulle, knocking ya dinga yi non stop kafin Jay ya bude kofar da mamaki yana kallonsa yace "What is it?" Ajay ya shiga dakin yana shafa gashin kansa da wani expression yace "He tracked her to Lagos" Still Jay yayi a inda yake tsaye ko kwakkwaran motsi baya yi yana kallon Ajay, Ajay ya ja numfashi sannan ya zauna kan kujeran dakin ya lumshe idanuwansa ya jinginar da kansa jikin kujeran trying to calm himself, Jay was speechless and shock at the same time, da kyar ya ja kafa ya zauna gefen gadonsa ya dafe kansa da yaji yayi masa nauyi, kamar an tsikare Ajay ya mike yace "Book us ticket to Lagos" Daga haka ya fice daga dakin.
[6/12, 8:02 PM] khaleesat Haiydar
: Aunty Farida ta share hawayen da yaki tsaya mata tana kallonsu Ajay da kyar tace "Wallahi ban san ko har su nawa bane a motar, ban ma san ya motar take ba tunda ina cikin gida sanda abun ya faru, yaran makota dake diban ruwa a bakin rijiyar tare da ita ne suke cewa kawai suna diban ruwa sai ga motar ta shigo street din, wasu mutane suka sauka a motar suka ja ta zuwa cikin motar suka tafi da ita, a sannan an idar da sallahn subahi kenan kun ga gari bai waye ba ai" Ajay was speechless, bai ta
a zama confuse haka a rayuwar sa ba don ya ma rasa abun cewa, likewise Jay dake jingine jikin mota tun da suka iso unguwan dama shi bai ce komai ba, Ajay ya daga kai after some seconds ya kalli Aunty Farida a hankali yace "Amma yana da number ki ne Aunty?" Aunty Farida tace "Ba shi da wannan number tawa gaskiya sai tsohon layi na, kwanaki Maman Khaleesat tayi rashin lafiya sai na tafi kano dubata to a hanya na yar da wayata, da na zo kano sai na siya sabon layi kafin inyi welcome back din tsohon layin, to har yanxu ban yi welcome back din ba" Ajay yayi shiru yana nazari, Aunty Farida na hawaye tace "Tsautsayi yasa ta fita deban ruwan yau, amma tunda ta xo wallahi ni ke diban ruwana bana barin ta dibar min tunda har yanxu gata nan ne dai bata dawo dai dai ba, wani lkcn ma da daddare idan na dawo kasuwa nake yi tunda ana wahalar ruwa a season din nan don yawanci rijiyoyi kafewa suke yi sai ana bari ruwan na taruwa sannan a diba, gashi ba a samun wuta balle a samu ruwan pampo, a jiyan nayi girki me yawa ne na wani biki duk sai na gaji ban deba ruwan da daddare ba, da na tashi kuma sai nake jin zazzabi, kun ji dalilin fitarta ta debo mana ruwa kenan" Ajay ya jingina da motarsa ya lumshe ido ya bude, gaba daya
ansa ya gama kullewa, bai yi zaton Abdul ya wuce yanda yayi zatonsa ba, the guy is really something else ko wani salon tactics na mugunta ya san sa gashi har yau yaki kunna wayarsa balle a san inda yake, ko by mistake baya kunna layin, shi dai Jay dama bai ta
a underrating Abdul ba dai dai da rana daya duba da irin actions din da ya dinga portraying, kawai dai tracing din Halysaah har zuwa Lagos is the least thing da yayi zaton Abdul zai yi, tunda bashi da access da Aunt dinta, but like seriously how did he even find his way, bayan bashi da active line din Aunty Farida sannan bai san unguwan da take ba, ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yana tunanin ta inda za su fara billo ma wannan lamari, tunda dai babu ta yanda za su ce yayi kidnapping Halysaah da ke a matsayin matarsa ta sunna.
Chapter 89 · 0% Book details