← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 167

Sashe 23

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da safe duk da yanda Khaleesat ke jin ta wani iri kamar zata yi rashin lafiya haka nan tayi shirin makaranta ta saka Facemask dinta sannan ta bar gidan, ta kusa awa daya a makarantar kafin Safiyyah ta shigo, Khaleesat ta zauna gefenta tana kallonta tace "Why are you sitted here Khalee?

Is the lecturer not around?" Khaleesat ta sauke idonta bata ce mata komai ba, Safiyyah ta sauke Facemask dinta ganin swollen eyes dinta cike da damuwa tace "Subhanallahi, what is wrong Khaleesat?

Kukan me kika yi?

Ko jikin Mama ne?" Khaleesat ta girgiza mata kai hawaye na taruwa idonta, hankalin Safiyyah ya tashi tace "Innalillahi, don Allah me ya faru?

Is everything ok?" Khaleesat ta girgiza mata kai tana goge idonta a hankali tace "Abdul ne ya zo" Safiyyah ta gwalo ido tace "Abdul kuma??

Yaushe?

Kuma me ya maki kike kuka?" Khaleesat tace "He came yesterday evening" Safiyyah tace "Ji jaraba, to me ya zo yi?

Kuma me ya faru da ya zo din?" Safiyyah na jefa mata wannan tambayar taji hankalinta ya tashi lkci daya, let it not be what just crossed her mind now, tunda tasan ko wanene Abdul, ta kamo hannun Khaleesat da sauri cikin tashin hankali tace "Ko ya maki wani abu ne?

A gidanki ya kwana???" Khaleesat ta girgiza mata kai a hankali tace "A'a" Safiyyah bata san sanda ta sauke wani ajiyar zuciya ba, can tace "Toh meye kuma na kuka don ya zo, ko rashin mutuncin da ya saba ya shuka maki?" Khaleesat na shessheka a hankali tace "He met my Housemate" Safiyyah ta bude baki tace "Kai don Allah, cikin gidan ya gansa?

To ke ma dai wallahi baza ki iya karyan kare kanki ba kice masa kawai ba
on Housemate dinki ne shi tunda bai san Nancy ta tashi a gidan ba, to sai kika ce masa me?" Khaleesat na gyada mata kai tana goge hawayen da yaki tsaya mata tace "Haka nace masa, amma ai kin sansa kinsan halinsa, he even fought with my Housemate" Safiyyah ta zaro ido tace "Fight?

To akan wani dalili?" Khaleesat tace "Kema kinsan yanda yake yi ai Sophie, kawai wai zai yi kissing dina ni kuma naki yarda sai ga Housemate dina ya shigo shine yayi approaching dinsa seeing what he was doing to me, hakan da yayi ne yasa Abdul yayi fada da shi, he hit him so hard" Safiyyah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to Housemate din ya rama ne?" Khaleesat ta girgiza kai a hankali tace "Bai rama ba, kawai hakuri ya basa" Safiyyah tace "Wallahi in ance min Abdul na shan giya ni bazan musa ba, cause his actions portray that, kawai daga ganin mutum ka fara fada da shi kamar wani
an daba, kuma in banda rainin wayo zai zo me yasa bazai ce maki zai zo ba kawai sai dai ki gansa kamar an jefosa a gidan?" Khaleesat tace "Wai fa ce masa da kika yi bani da lafiya shine yasa ya taso ya taho, da na sani da ban ce kice masa haka ba" Safiyyah ta bude baki tana kallon Khaleesat don ita ma sai a sannan taga da basu ce masa haka ba tunda ba isasshen hankali ke garesa ba, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "To yanzu Housemate din naki fa?

Hope he didn't hurt him?" Khaleesat ta fara goge wasu sabbin hawayen idonta tace "Kinsan menene ya dameni?" Safiyyah ta girgiza kai, a hankali Khaleesat tace "Maganganun da na gaya ma Housemate din nawa, meanwhile he was just trying to be protective ganin kamar Abdul molesting dina zai yi, ni kuma abinda yasa nayi masa haka don kar Abdul din ya zargi mun san juna da Housemate din nawa, cause i told him frnd din Nancy ne kuma ni ban taba ganinsa ba" Safiyyah da ta kasa rufe baki tace "Wasu irin maganganu ki ka gaya ma Housemate din naki?" A hankali Khaleesat ta gaya mata duk bakaken maganganun da ta gaya ma Housemate din nata, Safiyyah ta dinga mata wani kallo cike da takaici, can tace "To shi katon banzan da kika fadi bakaken maganganun a kansa hope yayi considering dinki at the end of everything?" Khaleesat ta girgiza kai tace "He walk out on me, na kirasa sau biyu jiya yaki dagawa, kuma har yanzu bai kirani ba" Safiyyah ta ja tsaki tace "In ma ya
aga shi babban
an iska ne, kada Allah yasa ya daga, kuma shi Housemate din naki kun sake haduwa bayan abinda ya faru jiya?" A hankali Khaleesat tace "Shi ma tunda ya bar gidan jiya har yanzu bai dawo ba" Safiyyah tace "To wallahi ki kirasa don mutumin nan yafi karfin walakanci a wajen ki" Khaleesat ta fara wani hawayen tace "I don't have his Number" Safiyyah tace "Ban gane baki da lambarsa ba?" Khaleesat tace "Wallahi, even when i was going to Nigeria kawai hadani yayi da wani mutum ya bani number mutumin amma bai bani lambarsa ba" Safiyyah tayi shiru, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Ki tashi kawai ki koma gida kilan Allah zai sa ya dawo sai ki basa hakuri, Abdul kuma kar ki kuskura ki sake kiransa in ba haka ba in tsine maki wallahi" Duk da bakin cikin da Khaleesat ke ciki sai da ta
an yi murmushi, a haka ta koma gida ta bar Safiyyah a school din bayan Safiyyah tace ta kirata duk abinda ake ciki, in ma Abdul din ne ya sake dawowa gidan ta kirata zata taho.....

Throughout ranan Khaleesat bata ga Housemate dinta ya dawo gidan ba har karfe takwas na dare, ta rasa me yasa ta kasa samun nutsuwa hankalinta yaki kwanciya, ko tunanin Abdul bata saka a ranta ba tun bayan barin ta school daxu da safe da Safiyyah tayi encouraging dinta kar ta sake kiransa, but she was so restless ganin Housemate dinta bai zo gidan ba, she wish she had his number ta kirasa, wajen karfe goma saura wayarta ya fara vibrate ta jawo a hankali tana duba screen din taga Safiyyah ce, Safiyyah ta kirata yayi sau 6 daga barinta school da safe har zuwa yanzu, Safiyyah tace "Is he back Khaleesat?" Khaleesat ta girgiza mata kai a hankali tace "A'a bai zo ba" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Kilan sai gobe zai zo gidan, ki kwantar da hankalin ki pls" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace "Plss kar ki wani damu kanki da yawa kawata, hope kin ci abinci?" Khaleesat tace "Na ci" Safiyyah tace "To kiyi kwanciyarki, good night" A haka suka rabu, Khaleesat ta ajiye wayarta ta lumshe ido duk da tasan ba baccin zata yi ba.......
*Continue making your payment before the end of free pages fanss, in ba haka ba aji shiruuu...*
07087865788
[5/8, 6:48 PM] khaleesat Haiydar
HALYSAAH
By _Khaleesat Haiydar_
11.....

Tun da gari ya waye Khaleesat ta kira Safiyyah tace mata bazata shigo school ba don tana son tayi bacci, Safiyyah tasan sarai bata yi baccin kirki ba kenan daren jiya, har mamakin yanda Khaleesat ta iya saka abu a rai ya dameta take, Safiyyah tace "Shikenan kawata, after our classes zan zo ko da yamma ne in sha Allah" a hankali Khaleesat tace "To Allah ya kai mu, Nagode" Daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar ta koma ta kwanta.
Chapter 23 · 0% Book details