Sashe 16
Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washegari asabar Khaleesat na shanya kayan jikokin Baaba Gaje da ta wanke, Baaba Gaje kuma na shirin fita kasuwa Ummanta suka shigo gidan tare da Aunty Farida da Siblings dinta yan biyu Islam da Noor that are just 11 years old, da gudu suka tafi suka rungumeta suna mata oyoyo, sosai kannin nata ke kama da ita, Khaleesat was so happy seeing her twins Siblings wanda su uku kawai Ummansu ta haifa, Baaba Gaje tace "Basu tafi islamiyya bane?" Umma tayi kasa da murya tana kallon Gaje tace "Sun ma kwana biyu rabonsu da zuwa, ba a biya kudin wata ba" Baaba Gaje tace "Ikon Allah to Alin ca yayi bazai biya ba kenan?" Umma tace "Cewa yayi in dora masu talla kamar yanda yan uwansu ke yi tunda su ba 'ya yan Gwal bane, dama ba fa shi ke biya masu ba wannan karan ne bani da kudi duk jarin ya lalace shine nace su tambayesa" Baaba Gaje tace "To Allah ya kyauta, amma Ali dai ha
in 'ya ya da kyar ya bari ya jiyo kamshin aljanna balle yaje kusa da ita" Ita dai Khaleesat a sanyaye ta kama hannun kannin nata zuwa dakin Baaba Gaje, tana jin Baaba Gaje na cewa "Amma de suna zuwa bokon?" Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "Ina fa, islamiyya ma da ya zama dole ba aje ba sae wani boko" Aunty Farida ta girgiza kai cike da takaici tace "Allah de ya kyauta, shi fa bakin cikin bata dora ma yaran talla kamar yanda sauran matansa ke dora ma nasu 'ya yan talla ba yake" Sosai jikin Khaleesat yayi sanyi don duk sanda ta tambayi Ummanta ko kannen nata na zuwa boko da Islamiyya ta wayar Sha'awa sai tace mata eh suna zuwa, ashe basa zuwa, Umma dai bata ce komai ba suka shiga dakin gaba daya, Baaba Gaje tace "Kun ga bari inje kasuwa in dawo" Su Umma suka mata Allah ya kiyaye ta figi gyalenta ta fita daga gidan, Khaleesat ta fiddo duk siyayyan da tayi jiya, daga Ummanta har Aunty Farida kallonta suka tsaya yi, Aunty Farida ta rike ha
a tace "Haka kudin suke da yawa da kika canza?
Kuma wa ya aike ki kashe kudi haka mu da muke da sabga a gabanmu Khaleesat?
Maimakon ki bada a ajiye maki ko kujeru da setin gado ne da kudaden?
Kin de san ko tsintsiya mahaifinki ba lallai ya siya maki da sunan a kai ki dakinki da shi ba ko?" Khaleesat tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Umma dai ta ma rasa abun cewa, Aunty Farida tace "Ni da kin yi shawara da ni duk baza ki yi wannan siyayyan ba, iyaka ki siyi abinda zaki koma can Amurka da shi, in suka tado da maganar aure me garemu da za a kai ki da shi Khaleesah?" Khaleesat na murmushi tace "Allah zai rufa asiri zuwa sannan Aunty" Aunty Farida tace "Yanzu duk kudin sun kare kenan?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Aa, saura dubu dari biyar" Daga Aunty Farida har Umma bude ido suka yi sosai suna kallonta with shock, Aunty Farida ta gyara zama tana zaro ido tace "Har nawa ya baki haka?
Ko dai baki da hankali ne" Khaleesat ta kauda zancen ta hanyar cewa "Har fa da kudadena duk na canxa" handbag dinta ta jawo ta bude ta ciro sauran kudaden da suka rage don har wanda Safiyyah ta bata ta canza, ta kirga dubu dari a ciki ta ware, sannan ta kirga dubu dari da hamsin shi ma ta ware, kallonta kawai Umma da Aunty Farida suke, ta ba Aunty Farida dubu dari tace "Aunty kiyi kudin mota da wannan idan zaki koma Lagos sannan ki kara jari" Ta ajiye ma Umma 150k tace "Umma ki rike wannan a biya kudin makarantar su islam da Noor a kuma canza masu Uniform" Umma tace "Ko dai baki da hankali ne Khaleesah? baki ji shawaran da Farida ta kawo bane halan?" Aunty Farida ta mayar mata da 100k din tace "Aa gaskiya ban ga alamar da kan nan ba Umma, ina ga hakoranmu za mu je mu jera mata a gida idan bikin ya tashi...." Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace "Akwai fa kudade a account dina wanda Abdul ke bani kuma suna da yawa za su isa ayi duk abinda za ayi sannan Aunty" It took Khaleesat almost an eternity to convince her Mother and aunt akan su rike kudin da ta basu, nan kuma bata da wani kudin a zo a gani a account dinta sai miliyan 10 na Abdul da ya ajiye a account din wanda nashi ne ba nata ba, iya kudin foodstuff kawai yake tura mata duk karshen wata sai kuma kudin Uber na zuwa makaranta, sai house rent dinta da yake biya at due time, iya abinda kawai yake mata kenan amma naira biyar dinsa baya bata a matsayin kyauta, instead sai dai ya siya mata kaya masu tsada, monthly kuma yake mata subscription a waya, apart from this bai bata kudi da sunan kudin kashewa, a haka dai ta samu tayi convincing Umma da Aunty Farida suka amshi kudin da ta basu, Aunty Farida na kallon Umma tace "To kinga sai kiyi kaffa kaffa da wayar nan kar su sace maki tunda sun saba maki haka, kin dai ga ba dan karamin kudi aka siyo wayar da shi ba" Umma na kallon Khaleesat tace "To shi Malam din me kika siya masa?" Aunty Farida ta wani kalli yayarta, Khaleesat ma dai kallon Ummanta tayi bata ce komai ba, Aunty Farida ta kyabe baki ta kauda kai, Umma ta kalli Aunty Farida tace "Wai saboda hakki, naga ta siya min waya shima da sai ta nemi abinda ta siya masa kwatankwacin wayar, kuma bashi da wayar shi ma wallahi" Aunty Farida na kallon yayarta da kyau tace "Umma in kinsan zuwa za kiyi ki kyautar da wayar nan da ta siya maki to gwara dai ki bar mata kayanta, ina ce kwanaki can matansa ya siya ma Atamfa yar gadagalle lkcn bikin Salisu ke ya siya maki?" Umma tace "Aa ba ruwanta da wannan Farida, ai ubanta ne, kuma don ta siyi abu ta basa ai ba faduwa tayi ba" Aunty Farida bata sake tanka Umma ba ta fara harhada ma Khaleesat kayayyakin abinci da ta siyo waje daya, Sai kusan la'asar su Umma suka bar gidan kuma har sannan Baaba Gaje bata dawo ba, a boye Khaleesat ta ba Siblings dinta 50k wanda ta saka a karamin jakar Islam tace masu in sun je gida su ba Umma kuma ta ja masu kunni sosai kan daukan sabon wayar da ta siya ma Umma kar su lalata mata.
Washegari da safe Khaleesat ta fito wanka wayarta ya fara ring tana dauka taga mutumin nan ne dai, bayan ta daga suka gaisa sannan yace "Hajiya nan da karfe tara da rabi wani driver zai kiraki sai kiyi masa kwatancen inda zai zo ya daukeki ya kai ki airport, don flight dinki zuwa Abuja na karfe sha daya ne, in kun iso Abuja kuma jirgin da zaki bi zuwa Amurka jirgin karfe biyu saura ne" Khaleesat tace "To ba damuwa Nagode" Aunty Farida kadai ce ta zo gidan Baaba Gaje yi ma Khaleesat sallama, Khaleesat bata ji dadin da Umma bata biyo ta ba, duk jikinta yayi sanyi sosai, a haka drivern da zai kai ta airport ya iso, Baaba Gaje ta dinga sa mata albarkan wayar da ta siya mata da abubuwan da ta siyo ma jikokinta, bayan an kai akwatin kayanta cikin mota su Aunty Farida da Baaba Gaje suka rakata har bakin motar, bayan Khaleesat ta shiga motar ta daga masu hannu a sanyaye tana murmushin karfin hali, har cikin ranta bata ji dadin da bata yi sallama da Ummanta ba, a haka suka kama hanyar airport da drivern da ya zo daukarta, suna sauka Abuja karfe daya da minti 40 jirgin su ya tashi.