← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 167

Sashe 13

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To nawa ne ma a account dinta before she think of doing so, ko dai kawai ta tafi Motor park ta hau mota zuwa kano, dollars din da Housemate dinta ya bata ne ya fado mata a rai don gaba daya ta ma mance, ta bude handbag dinta ta ciro kudin tana kallo, takardan da ya saka mata hade da kudin a jaka ya fadi kasa, ta duka ta dau takardan tana kallon numbers din jiki sai kuma ta mayar cikin jaka tare da Dollars din, masallacin dake cikin Murtala Muhammad International airport ta tafi don yin sallan asuba, tana ta zaune cikin masallacin bayan ta idar da sallah tana azkar dinta, can ta ciro wayarta a handbag ta duba agogo taga karfe bakwai da minti goma, dollars din jakar ta sake cirowa ta kirga taga dala dubu ce, kallon kudin ta dinga yi jiki a sanyaye don bata yi tunanin har haka ya bata ba, ta dau white paper din dake dauke da digit tana tunanin to ko digit dinsa ne wannan din, kati ta siya ta Ussd sannan tayi dialing number a wayarta, sai da ya kusa katsewa aka daga, daga daya side din aka yi sallama ta amsa, amma sai taji kamar ba muryarsa bane, ta dai ce "Ina kwana?" Yace "Hajiya ko kece kika taho daga America?" Tace "Eh" Yace "To barka da isowa Hajiya, ina ta sauraren kiran naki dama tun daxu, kina cikin airport din ne yanzu?" Tace "Eh" Yace "Ohk to gani nan tahowa ba da dadewa ba in sha Allah" Bayan ya katse wayar ta kalli screen dinta, to waye kuma wannan, maida kudin tayi jaka ta ciro nose mask dinta ta saka sannan ta mike ta fito daga Masallacin da trolley dinta with handbag, bayan wasu mintoci sai gashi ya sake kiranta, ta fito outside of the airport, yana hangota ya nufota ya gaisheta da ladabi har da bowing kansa yace "Ya hanya Hajiya?" Ta sauke idonta tace "Lafiya Alhamdulillah" With respect yace "Ga mota can Hajiya, zaki je hotel ki huta zuwa karfe daya na rana don Flight dinki zuwa kano na karfe Biyu ne in sha Allah..." Khaleesat was speechless ta dinga kallonsa babu ko kiftawa cike da mamaki, can kuma ta kalli lafiyayyen motar da ya nuna nata, tuni ya karasa ya amshi trolley dinta ya tafi ya bude booth ya saka, sannan ya bude mata bayan mota yace "Bismillah Hajiya" Sauke idonta tayi kasa taji kafafuwanta sun mata nauyi amma a haka tana tafiya a hankali ta tafi ta shiga back seat sannan ya kulle motar, ya zaga ya shiga driver seat, Hotel me tsada sosai that isn't far away from the airport ya kai ta, sai da ya tabbatar tayi check in har zuwa dakinta sannan ya bar hotel din, tana shiga babu jimawa wata ma'aikaciyar hotel din ta kawo mata lafiyayyen Breakfast, ita dai Khaleesat ba um bare um um, gaba daya kanta ya gama kullewa, tashi tayi ta bude trolley dinta ta dau Shower gel zata yi wanka.

Khaleesat na bacci wajen karfe daya da minti ashirin vibration din wayarta ya tasheta, ta jawo wayar a hankali tana duba me kiranta taga mutumin da ya kawota Hotel ne, ta mike zaune sannan tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yayi mata sallama sannan yace "Hajiya fatan kin shirya in taho in dauke ki, flight din naki nan da minti talatin ne in sha Allah" a hankali Khaleesat tace "Toh" Yace "Gani nan tahowa yanzu da izinin Allah" Yana katse wayar Khaleesat ta sauka daga saman gado taje tayi alwala a bandaki, tana idar da sallan Azahar sai ga kiransa, ta dau trolley dinta da handbag ta bar dakin hotel din ta sauko downstairs, yana hangota a Reception din hotel din ya tafi da sauri ya amshi trolley din hannunta, ya karbi makullin dakin ya kai ma Receptionist, sannan suka fita haraban hotel din ya bude mata back seat bayan ya saka trolley dinta a booth, cikin mintuna kadan suka isa MMI Airport, sai da ya tabbatar ta amshi boarding pass dinta sannan yayi mata sallama da murmushi fuskarsa yace "Toh Allah Ubangiji ya tsare Hajiya, idan kun sauka kanon za a karasa dake gida in sha Allah...

We will keep in touch" a hankali Khaleesat tace "Toh Nagode, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen Hajjaju, nagode kwarai, Allah Ubangiji ya kai ku lafiya" A haka suka rabu ta nufi Departure lounge walking slowly, bayan kusan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin kano.

Suna sauka kano Khaleesat ta fito daga cikin airport gabanta na faduwa, sai gyara nose mask din fuskarta take tana waige waige, yanzu ina ma ta nufa tukun, tasan ko da wasa bazata nufi gida ba dai, wayarta ya fara ring ta duba da sauri gabanta na ci gaba da faduwa, wata lamba ce ke kiranta tayi picking tayi shiru, taji an mata sallama ta amsa, mutumin ya gaisheta yace "Hajiya Hamisu ne ya aiko min lambarki, naga jirgin ku ya sauka yanzu, yace za a karasa dake gida, kina ta ina yanzu?" Tace "Na fito outside of the airport" Tahowa taga mutumin yayi zuwa inda take tsaye bayan ya hangota, nan ya kai ta har motar dake jiranta, motar shigen wanda ta shiga a Abuja ne, mutumin ya bude mata back seat ta shiga tace "Nagode" Yayi bowing kansa yayi mata sallama yace "Allah ya kai ku lafiya" Tace "Ameen Nagode" Drivern dake mazaunin driver ya gaisheta yana tambayarta ya hanya sannan ya tada motar suka fita daga airport din yace "Ina muka nufa Hajjaju?" Khaleesat ta
an yi shiru kamar me nazari, sai kuma tace "Hotoro zaka kai ni" Yace "To Allah ya kai mu lafiya" Suna isa dai dai kofar gidan da ta nuna masa ya tsaya, ya bude motar ya sauka don fiddo mata Trolley dinta a booth, bude motar tayi ita ma ta sauka tana gyara facemask dinta, ta amshi akwatinta a hannunsa sannan tayi masa godiya ta shiga cikin gidan da sauri, Baaba Gaje dake zaune tana tankade garin tuwo ta daga kai tana kallonta, Khaleesat ta
an sauke Facemask dinta tana murmushi tace "Baaba sannu da aiki" Baaba Gaje ta ajiye rariyar hannunta tace "Khaleesatu?

Daga ina kuma haka?" Khaleesat ta duka nan gabanta har sannan tana
an murmushi tace "Makaranta" Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to ai ko minti ashirin banyi da dawowa daga gidanku ba kuma ba ace min kina hanya ba" A hankali Khaleesat tace "Baaba ya jikin Ummanmu fa?" Baaba Gaje tace "Kaddai ba a san kin biyo hanya ba kika taho Khaleesatu?" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to ai jikin nata da sauki er nan, shi Awdul din ne ya biya maki kudin jirgi kika dawo?" Khaleesat ta girgiza kai gabanta na faduwa tace "Bai san na dawo ba Baaba" Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to bari in kira Parida, ko kuma ke ki kirata da kanki, Gwara da kika yi dubaran zuwa nan kada Salubabben uban nan naki ya sa ki a bakin duniya mu shiga uku, Ga tabarma taho ki zauna ki huta, irin wannan tafiya me nisa haka, naji ance Amurkan har yapi legas nisa ko?

Kira Paridan mu ji yanda za ayi" Khaleesat ta zauna gefenta ta bude handbag ta ciro wayarta, duk da yanda gabanta ke faduwa haka tayi dialing din lambar kanwar Ummanta Aunty Farida, Baaba Gaje tace "Auu to ai Parida ba waya a hannunta wai an sace a mota" Khaleesat ta daga kai tana kallonta, Baaba Gaje tace "Abinda zai faru kawai ga garin tuwon nan ki karasa tankade min ga can murhu na dora ruwan tuwo in yayi ki min talgi ki tuka tuwon in ya silala ki kwashe, ga kuma kayan miya can bai dai da yawa ki jajjaga ki kada min miyar kuka, ni kuma sai in koma can Mariri yanzu in sanar ma Ummanku kin zo" Khaleesat tace "Toh Baaba" Mikewa Baaba Gaje tayi ta figi yakunennen gyalenta a igiyar shanyan dake
an karamin tsakar gidan ta yafa tace "Bara inje, dama ina da canjina dari da hansin sai in roke masu
an sahu su kai ni ko Farawa ne sai in karasa Maririn da kafa ta" Khaleesat ta bude handbag dinta amma sai taga Dollars kawai, ta daga kai ta kalli Baaba Gaje tace "Wallahi bani da kudin Nigeria a nan Baaba, amma bari in ciro a POS yanzu sai in baki kudin adaidaita sahun" Baaba Gaje tace "Aa yi zamanki kiyi aikin da na sa ki, minti nawa ne nan da Mariri, kawai dai ga wanke wanke can bakin kwararo ki wanke min har su, ki share tsakar gidan nan, in yaran nan suka dawo islamiyya ki dauraye masu Uniform dinsu, dakin ma na nan sunyi kaca kaca da shi babu kyan gani" Daga haka ta fice daga cikin gidan bayan ta saka slippers dinta, Khaleesat ta cire mayafin abayan jikinta ta dora kan akwatinta sannan ta ci gaba da tankaden da Baaba Gaje ta bar mata, Baaba Gaje makociyarsu ce a can unguwansu Mariri kafin 'ya yanta su siya mata wani
an kararramin gida a nan Hotoro Tsamiyar boka ta dawo tana zaune da jikokinta biyar tana dubasu, zaman mutunci da amana Baaba Gaje suka yi da Mahaifiyar Khaleesat da ta dauki Gajen tamkar uwa.

Wajen karfe shidda saura Khaleesat ta gama duk aikin da Gaje ta loda mata sannan ta dora ruwan da zata yi wanka a sauran rushi, zaunawa tayi kan tabarma ta jingina da bango don ta gaji likis, Housemate dinta ne ya fado mata, ta dai yi shiru staring into space, after a while ta sauke idonta a hankali ta mike ta shiga da kwanukan da ta wanke cikin dakin Gaje, dai dai nan Gaje ta shigo cikin gidan da Aunty Farida, Khaleesat ta tafi da gudu ta rungume Aunty Farida cike da murnan ganinta, Aunty Farida na kallonta tace "Ke kuma da wa kika yi shawara kika biyo hanya Khaleesah?
Chapter 13 · 0% Book details